Chapter 44
Chapter 44
ta ta Ƙare".ƙit ta kashe wayar ba tare da ta Ƙara magana ba. abin ya yimin zafi sosai,na ciji leƁena na Ƙasa azuciyata na ce eh lallai jidda tazo da sabon salo,ai kuwa bazai taƁa yiwu a hana Ƴan uwana shigowa gidan ba,tunda duk gidan mijinmu ne. na saka takalmina soso mai tudu wanda na ajje don sakawa afalo,na fita raina aƁace Na yi hanyar gate Ɗin,a garding Ɗin gidan na hango jidda tana waya,ta kalleni ta zubar sannan ta yi saurin kashe wayar,don daman ta yi hakanne don in hassala,kuma gashi na hassala Ɗin. ina zuwa na kalli me gadin wanda keda kayan kaki ajikinsa,na ce"meye dalilin Hana Ƴan uwana shigowa Gidan mijina"?. Cikin girma mawa ya ce"hajiya ki yi haƘuri jiya me gidan ya yi tafiya kuma bai bani apointment akan wani zai shigo ba,ya bani umarni akan duk wanda zai shigo in kira hajiya jidda idan ta yadda sai mutum ya shigo." kallon jidda na yi wadda ke nufo inda muke.tana sanye da wani shegen takalmi mai mugun tsayi,ga wani uban glass afuskarta no respect.taɗan janye glass ɗin kaɗan sannan ta ce"obinna duk wanda bazai bi dokar mai gidan ba.ka ƙyalesa kada ka kuma wata magana,ka koma bakin aikinka". Ta faɗi hakan tana mana wani kallon banza,Maryam ta ce"hmm idan kunsan wata baku san wata ba".sai ta danna wayarta ta kira hajiya kaka tana shaida mata abinda ya faru. Kai tsaye Hajiya kaka ta shiga ɓangarensu Bilal.ta yi sa'a kuwa Baba Abdullahi yana nan suna hira da matarsa.hajiya Ruƙayya na ganinta ta gimtse fuskarta don tasan ba alheri ya kawo hajiya kaka ba. Hajiya kaka ta nisa ta ce"Ruƙayya zo ki dake ni ba murtuke fuska ya kamata ki yi ba?uwar rashin ɗa'a.yanzu gashinan kin koyawa ɗanki Bilal ya wulaƙanta ƴan gidansu,saboda shima yanzu ya yi gida ko?to wallahi ko awata uwa duniya ya ke ki kirasa ki faɗa masa wallahi ya yi maza yabar maryam ta shiga gidan nan idan ba haka ba.masifar akanki zata ƙare,yo idan ma ba rainin hankali ba tayaya za'ace a hana ƴan uwan mutum shiga gidan ɗan uwansa?a ina aka taɓa yin hakan?ko ke ƴan uwanki sun taɓa zuwa nan aka hanasu shigowa?to wallahi ahir ɗinki daga ke har ɗan naki mara kunya". sunkuyar da kai hajiya Ruƙayya ta yi,Baba Abdullahi ransa yakai ƙololuwar tashi,ya nisa ya ce"Ruƙayya yaushe Bilal ɗin ya yi tafiya?ashe shi yanzu idan zaiyi tafiya haka kawai ya ke yinta?saboda ya zama babba ko?babu saka albarkar iyaye?." "wallahi nima bansan ya yi tafiya ba?amman ka yi haƙuri". Number Bilal ɗin ya kira,ya ɗaga yana tsaka da aiki bayan sun gaisa ne ya rufesa da faɗa sosai,ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba,Bilal ya yi shiru kawai yana jin faɗan mahaifinsa,ya basa haƙuri ya kashe wayar ya kira obinna ya bada umarnin maryam ta shiga. Maryam na shiga ta kalli jidda ta ce"to uwar mata yanzu ma ai sai ki hanani shiga?uwar iyayi mai son raba kan ƴan uwa". Ta faɗi hakan tana hararar jidda ɗin.jidda ta yi ƴar dariya ta harɗe hannayenta a ƙirji tana wa maryam ɗin kallon rainin hankali ta ce"hmm kin bani dariya wallahi,ai ta banzar tunda ita dai wacce take cikin gidan ba tada wannan matsayin da zata bada doka da order aji,don haka ni baku burgeni ba". Ta faɗi hakan tana nuna halin ko in kula,har maryam ta yi gaba sai kuma ta dawo ta ce"hmm jidda ma ki ke kowa?to idan ban mayar miki ba kice ni ba jikar hajiya kaka bace?kema da ki ke wani fiffigewa wai ke gaki star awajen miji ko?to wallahi kiji tsoron Allah don duk matar da ta saka ido ana wulaƙanta ƴa mace tana jin daɗi to wallahi wataran itama sai an wulaƙantata wataran itama,don haka ki guji ɓacin rana". Dariya sosai Jidda ta yi ta ce"oho dai tsabar rashin zuciya ya ce baya so amman sai da aka liƙa masa."ta faɗi hakan tana tin tsirewa dariyar muguntar ta faɗamin magana. Har na yi gaba sai kuma na dawo,na kalleta idanuwa na suka cika ɓam,da hawaye ban yarda sun zubomin ba na wuce sashe na.na barsu ita da maryam suna ɗauki ba daɗi. Sosai maganar da jidda ta faɗamin take bin dukkan gaɓɓan jikina,na ƙwanta akan ɗaya daga kujerun farlona na saki kuka mai ƙarfi,tabbas na cancanci Jidda ta yi min gori,yau ƙwanana huɗu amman ko albarkacin haƙƙina da ke kansa ai ya kamata ya saukemin,amman madadin rashin hakan gashinan matarsa na wulaƙanta ni. "Haba Khairat yanzu don wannan banzar ta faɗa miko magana shine ki ke kuka?ai kuwa matuƙar zaki dinga yi mata kuka to kuwa ta samu lagon ƙuntata miki agidan aurenki,ki zama jajirtacciya agidanki,nasan kina da dauriya amman ki ƙara daurewa kinji".ta faɗi hakan tana sharemin hawaye na. Nan dai muka shiga hira take cemin gobe za'a kawomin gara ba'a gama haɗawa bane,na ce mata babu komai. Ta ce"yanzu ma daga asibiti na ke naje dubo Rashida,kinsan tun bayan bikinku ba tada lafiya".ta faɗi hakan cikin damuwa. Nima cikin damuwar na ce"innalillahi ashe haryanzu jikinne?shiyasa dana buga mata waya naji shiru?tun shekaran jiya na ke kira amman switch up".na faɗi hakan cikin damuwa. Maryam ta ce"ke dai bari ɓari ta yi wallahi ciki wata huɗu".da sauri na saki salati tsabar tausayi kamar zanyi kuka,na ce"yanzu ya jikin na ta?".maryam ta ce"ai da sauƙi ma yanzu don wallahi ranar da tayi ɓarin da mukaje baki ga ba abin tausayi,ko magana bata iyawa sai dai idanu,don ta zubar da jini sosai ai yanzu da sauƙi". Tuni jikina ya hau tsuma na idanuwa na suka kawo ruwa,don komai idan aka saka Rashida aciki mai mahimmaci ne,tun muna ƙanana idan ɗayanmu ba shida lafiya to zaka samemu cikin wani hali. Maryam ce ta dinga rarrashina,amman duk da haka ban daina kukan ba,tunanin halin da Rashida take ciki shine yafi tsayamin,na ce"insha Allah zanje in duba ta fatanmu dai Allah ya bata lafiya me ɗorewa,na faɗi hakan muryata na rawa. *** Har washe gari jikina duk babu daɗi,na kira wayar yaya Aliyu mijin Rashida yafi sau 5 amman bai ɗaga kiran ba,ƙarshe dai na haƙura. Na fito daga wanka kenan na jiyo ƙarar tsayuwar mota,jikina yana rawa na leƙo na hango Yaya Bilal yana fitowa daga cikin motar,kayan da ya sanya sunyi matuƙar amsarsa,kyaunsa ya ƙara fitowa sosai,hawaye masu zafi suka fara ambaliya acikin idaniyata na saka hannuna na goge,ban gama ida abinda na ke ba na hango Jidda ta fito daga sashenta taci uban riga da wando english wears ya yi matuƙar kamata,ta rungume Yaya Bilal shima ya rungumeta sosai,kamar wani zai ƙwace ta,tuni wani abu ya tsayamin azuciyata kamar wani mashi ko kuma guduma,tsananin kishi na yakai ƙarshe da sauri na saki labulen,ya yinda shi kuma ya ɗauki jidda kamar ƴar tsana suka yi ɓangaren Bilal ɗin. Na ƙwanta akan gado na hau aukin kuka,wanda ayanzu ya zamarmin kamar wani abinci,ina da komai a store ɗina,don tun kafin a kawo min gara ya ajjewa kowaccenmu abinci,fridge ma cike ya ke da abubuwa na more rayuwa,ni dai mijine ya zamarmin wahala don tunda muka yi aure ban ƙara sakashi a ido na ba sai yau. Ina cikin wannan yanayin naji ana buga ƙofar ɓangare na,jiki na duk babu ƙwari nazo na buɗe,wanda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87