Chapter 35
Chapter 35
kuka ina dukansa,su Yaya Aliyu sai dariya suke Anty khadija ta kallemu ta watsar sannan ta tashi tsaye ta ce"hmm irin wannan taɓara har ina haka,anbi duk an sangarta yarinya kamar wata ƴar baby".? Sosai yayannin na wa suke ta mana dariya,babu wanda baiji abinda anty khadija ta faɗa ba dukkansu dai sunji haushin maganar amman a fili kamae basuji ba suka barta kamar wata mahaukaciya,ba taso yin shirunsa ba don abin ya bata haushi yadda ko albarkacin gaisuwa bata ciba amatsayin matar yayansu kuma Ƴar uwarsu. **** Sosai hankalin Bilal ya tashi jijiyoyin kansa duk sun tashi ruɗu-ruɗu haka za lika idanuwansa sunyi jawur kamar gauta ya ce"yanzu mama ni za'a haɗa da wannan mahaukaciyar yarinyar wacce na tsana arayuwata?yanzu abinda Baba zaiyi min kenan?is no possible hakan ya faru bazan taɓa iya auren wannan yarinyar ba,wallahi dana aureta gwara in auri mahaukaciya wacce ke yawo bola-bola insan abinda na aura,yarinyar da ta gama gantalinta atiti,to wallahi ba umarnin kaka ba ko umarnin meye ne ni bazan aure taba". "don Allah Bilal idan har ka isa kana ganin kai wuyanka ya isa yanka kanka ɗaya damu da kuma mahaifiyarmu?to don Allah kada ka aureta?sakarai kawai wanda bai san inda ya ks mishi ciwo ba".ya faɗi hakan yana matsowa inda Bilal ɗin ya ke. Alhaji Abdullahi ya kalli Hajiya Ruƙayya sannan ya ce"ke kuma na gode da abinda ki ka yimin?amman ki sani daga ks har ɗanki babu wanda ya isa ya juyani akan wannan maganar,ƙanina ma Malik daya ƙalubalanci abin yanzu sama-sama na ke dashi kai bama shi ba koda mahaifiyarta ce ta nuna ba taso to bata isa,a ƙarshe ina ƙara jan hankalinku da ku kula sosai da abinda zaije ya dawo matuƙar kuka nuna min isa". Yana faɗar hakan ya wuce fuuu abinsa,Hajiya Ruƙayya ta kalli ɗan na ta sannan ta ce"my son mahaifinka mutunne mai kafiya akan abu,muddin yasa abu a gabansa to sai ya ci masa,don haka ka yi haƙuri kawai amman fa idan ka aureta ni na sakaka ka gana mata azabar da zai sa da ƙafarta tabar gidan,kuma sannan ban yarda ka kusance ta ko d sau Ɗaya ba. *Miss green ce* Hmm ku kasance da wanman littafi mai suna Abin cikin ƙwai aƙwai babbar tafiya nan gaba,mai cike da ƙalubale,ban tausayi,ban dariya,da sauransu ku dai ku kasance da ummu maher miss green,sannan aƙwai alƙawarin dana yi muku na koyar da girke-girke insha Allah ban manta ba sai anan gaba. *A C Ƙ* MISS GREEN *37⬜38* . . .da sauri Bilal ya ce"Allah ya tsareni da ko shiga ɗakinta don ban san abinda zan tarar ba,na tsani wannan yarinyar tsana mafi muni arayuwata,zan cigaba da addu'ah da kuma lallaɓa Baba Allah yasa kada in auri wannan annobar".yana faɗar hakan ya yi waje abinsa cikin zafin zuciya da kuma ƙuna. bai san adadin rashin son ta da ya ke acikin zuciyarsa ba,ko son kallonta bai yi balle kuma har ya zauna inuwa Ɗaya da'ita bai fatan hakan ta faru don matuƘar hakan ya faru to tabbas aƘwai babbar matsala agaba. ***** Ina yawan jin faɗuwar gaba,na rasa me ke janyo min hakan,na kasance acikin ruɗu sosai,ban san wanda zai rarrashe ni ba,shiri na ke sosai don yau so na ke zanje gidan Rashida don mun ƙwana biyu bamu haɗu ba,wata atamfa ta na ɗakko ɗinkin riga da siket atamfar holland ce ja yellow da ratsin ja,sosai na yi kyau acikin atamfar kamar ka ɗaukeni,haka kawai naji inason yin ƙwalliya na shafa hoda da janbaki ja amman maroon sai ƙwalli da maskara,wow gaskiya na yi ƙyau sosai daman gani da shape irin na coco cola sai na yi wani ƙyau kamar kasace ni,na yi park ɗin gashina a baya daman gani da tsayin gashi amman kuma kamar roba haka ya ke,na yi ɗaurina ture kaga tsiya.na yafa mayafi na ja amman da followers yellow kaɗan,na ɗauko dogon takalmina high hill,sosai na yi kyau kamar zarah acikin wata,na ɗauki wayata da ƴar fos ɗina suma suk red ne.ina fitowa muka haɗe da Anty khadija afalo,ta kalleni sama da ƙasa ta ce"ke kuma sai ina?".Tambayar ce taban mamaki don bata saba ganina ina gantali ba. Na ce"daman zanje gidan Rashida ne mun daɗe bamu haɗu ba",taɓe baki ta yi sannan ta ce"oky amman kin san dai baki gama aikinki ba ko?".Ta jeho min wannan tambayar ta rainin hankali,sosai tambayar ta bani mamaki don nasan dai tun safe na gama komai harda wankin kayan khairat,to kuma wani aiki ne zanyi?. "Ki ka tsaya kina kallona ko kin gama aikinne?".kasa magana na yi saboda ban san me zance mata ba,ni ba mutumce mai musu ba ko jayayya ma ban iya ba sai dai ka gaji ka yi shiru. Na ce"to idan na dawo ma zan ƙarasa aikin".na faɗi hakan inawa little khairat kiss akumatu na yi tafiya ta ko hangenta banyi ba.taɓe baki ta yi sannan ta kalli ƴar ta khairat ta ce"oh ke dai Allah yasa kada ki yo wannan mai mummunan halin,kawai an tashi an laƙabawa yarinya sunan wannan mara mutuncin,ga sunan ubana dana uwata ba'a saka ba sai na wannan banɗararriyar."ta faɗi hakan tana bawa Khairat mama. *** Tun akan hanya wani ya ke ta bina amman ko kallon ƙurarsa banyi ba,ya yi parking ɗin rantsatsiyar motarsa a gabana.na juyar da kaina gefe na tsaya ina kallon ikon Allah,wani mutumine ya fito daga cikin motar sanye da glass ya ce"Hajiya oga ne ya ke son yin magana sa ke".kallon tsaf na yi masa sannan na ce"ok kawai ya ganni a hanya sai ya ce wani zai yi magana dani to ka ce masa bazan tsaya ɗin ba".na yi wuce wa ta. Daga gidan Yaya Aliyu naira ɗari ne zai kaika gidan Rashida na shiga keke napep na yi gaba abuna,sai dai tunda na shiga motar na hango wannan motar abaya tana bina har zuwa ƙofar gidan Rashida. Na rasa me zance saboda haushi,na fito da kuɗin na bashi cikin fushi na shiga gidan,ko waiwayensa ban ƙara yi ba,a farlo na same ta tana cin abinci da gudu ta taho ta tarbeni tana ce wa"kai sis na ji daɗin zuwanki".har muka zauna Rashida bata sake ni ba kamar wani zai ƙwaceni. Na ce"ni don Allah sakeni bayan ma ko zuwa inda na ke biki yi ba?Yau watanku uku da aure amman kin manta da zamana".dariya i'tama ta yi sannan ta ce"hmm ai gidanku bazan iya zuwansa ba,saboda anty khadija sam bana shiri da ita don ni bana son rainin hankali da kuma wayo".na ce"hmm".kawai ba tare dana ƙara ce wa komai ba. Na ce"wai ni Rashida ya naga kin ƙara wani fari ne da cika idanuwa?".Dariya ta yi sannan ta ce"hmm ai nan da 7 month zaku zo suna". Rungume ta na yi ina dariya na ce"ah ki ce mun kusa zama manya?". Ta ce"ni kuwa ya naga ko ɗan gyaran amare baki fara ba?ai wallahi Khairat baki da mutunci ace zaki auri yaya na amman sai a duniya na ke ji"?. Kallonta na yi ƙuri na kasa ce wa komai,mamako da kuma ruɗu suka cika ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwata,na ce"hmm wai Rashida me yasa ki ka fiye wasa ne?Ta yaya za'a ce za'ayi biki na amman baki sani ba?"a'i kema kin san ba zai taɓa yiwu ba".na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87