Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,287 words 0 views Progress saved
Download Book

ɗinsa,hajiya Ruƙayya ta yi mamako sosai sai dai ɗan adam ba abin yarda bane musamman ma yaran yanzu,sai dai kawai addu'ah. Wasa-wasa sai ga hajiya kaka ta fara ciwo don ko iya magana ma bata yi,sosai abin ya taɓa ƴaƴanta sunyi kuka har sun gaji kuma kullum magani ake amman shiru. Yaya Aliyu da kansa yazo ya samu Babanmu ya faɗa masa ina wajensa,amman buɗar bakinsa sai ce wa ya yi"ni fa na cire ta daga cikin ƴaƴana idan taso ma ta shiga uwa duniya wannan bai shafeni ba,tunda haka ta zaɓa".sosai maganat ta daki zuciyar yaya Aliyu amman ya daure kawai,don mahaifi ya wuce gaban wasa. Yaya Aliyu san bai gaya min ciwon hajiya kaka ba,sai abakin Rashida naji wacce ks kawomin ziyara akai-akai,ita ma ta yi baƙin ciki,ta yi kuka abisa ƙazafin da aka yi min a kullum bani haƙuri take don haka yanzu damuwata ƙadance akan ta da,yaya salim ma yana yawan zuwa,maher ƙanina da ke skull shima ya dawo yaji duk abinda aka yi min,kai tsaye ya ce ƙarya ne sharri ne,kuma asannu sai ya tona musu asiri. Abinda ya ƙara saka rayuwata acikin garari bai wuce kai kuɗin yaya Bilal da saka ranarsa da jidda da aka yi ba,naci kuka har na godewa Allah,wato ni tawa ƙaddarar kenan?kamar wadda ba tada sa'a a rayuwarta?haka dai na dinga sambatuna ni kaɗai a ɗaki,daman idan na gama aiki na sai in shiga ɗaki in ɗakko wayata in ta karatu a arewabook don ina jin daɗin manhajar anan naci karo da wani littafi wanda miss green ta rubuta silar fyaɗe sosai littafin ya ɗaukemin hankali don kusan abinda ya faru dani shine ya faru da yarinyar cikin littafin,anyi mata fyaɗe amman bata san waye ba?anan naji hankalina ya daɗa ƙwanciya don yarinyar cikin book ɗin ta yi haƙuri sosai ƙarshe kuma komai ya zama labari. Ina cikin karanta book ɗin na jiyo nishin anty khadija sosai hankalina ya tashi na fito farlo,na ganta durƙushe jikin dining table ta riƙe bayanta da hannu ɗaya,da sauri na isa inda take ina ta rafko mata sannu,na yi saurin kiran yaya Aliyu awaya,shima cikin tashin hankali ya taho. *Miss green ce* [23/09, 16:20] Miss Green🍀: 33🟫34 . . . .muna zuwa kai tsaye labour room aka kaita duk ta galabaita sosai,sa ƙer take nishi duk hankalinmu atashe muka zauna a reception ɗin bayan sun shigar da i'ta ɗakin ƴan haihuwa. Na kalli yaya Aliyu wanda duk a ruɗe ya ke na ce"bro ka kira mutanen gida mana susan halin da ake ciki?".girgiza min kai kawai ya yi alamar baya buƙatar hakan. Munfi awa biyu a zaune sannan likitab ta fito ta ce"ta kasa haihuwa da kanta suna tunanin ma operation za'ayi mata,likitan ta tambayi mijinta?yaya Aliyu ya bisu zuwa wani office. Data na da ke kunne naji saƙonni na ta shigowa,sunan Rashida da na gani ne yasa ni duba saƙon na ta,anan na ke gaya mata abinda ke faruwa,na ce"Rashida ni naso ya faɗawa mutanen gida don baki gani ba wallahi ta sha wahala sosai". "Ai gwara kada ya gaya musu,kin san dai yanzu a halin da ake ciki,ni bana son su ganki ma tunda su basu yarda da ƙaddara ba,kuma abinsu babu bincike,yanzu hajiya kaka ma tana cen rai a hannun Allah kuma nasan duk sanadin wannan abin ne". wata irin muguwar faɗuwar gaba naji ina hawaye na ce"Rashida kina son ki ce min hajiya kaka ce tace babu lafiya?innalillahi yanzu a gida take ko a asibiti?kuma me ya janyo ciwon na ta?". Duk alokaci ɗaya na rattabo mata waɗannan tambayoyin?ganin hankalina ya tashi sosai yasa ta fara ƙwantarmin da hankali sannan ta ce"khairat kada kice zakije gidanmu ki ƙelesu aƙwai lokacin zuwan,Hajiya kaka addu'arki take buƙata ba wai kuka ba,idan ki ka yi mata addu'ah ko a i'na take Allah zai amsa,don Allah khairat kada ki ɗaga hankalinki kinji don Allah". Muna cikin wayar mijinta yaya Aliyu ya amshi wayar ya ce"khairat kada ki ɗaga hankalinki babu abinda zai faru da hajiya kaka kinji".goge hawayen fuska ta na yi ina jin kaina ya yi min wani iri kamar zai tsage gida biyu. A haka har yaya Aliyu ya dawo ya sameni ganina riƙe da kaina wanda ke barazanar rabewa gida biyu ya ce"khairat me ya ke damunki?kanki ne ke ciwo".?duk babu amsa don haka ya saka bayan hannunsa kan goshina yaji mugun zafi kamar wuta,yana cirw hannuna daga kan goshina sai yaji na tafi luuuuu. Sosai ya tsorata ya fara girgiza ni yana kiran sunana,amman ina sai na yi sharaf a hannunsa,wani irin salati ya saka da gudu ya ɗaukeni kamar ƴar tsana yana ihu yana kiran likitocin. Da sauri likitocin suka bayyana,suka sakani a gadon marasa lafiya suka yi wani ɗako dani,yaya Aliyu fa ya zama kamar wani mahaukaci sabon kamu,ga matarsa tana labour ga ƙanwarsa babu lafiya,ya rasa awani bigire zai kira wannan ƙaddarar ya ɗaga hannayensa biyu sama yana ce wa"ya Allah ina roƙonka don tsarkin sunayenka tsarkaka Allah ubangiji ya bawa waɗannan bayin na ka lafiya ƙanwata da kuma matata. Da ƙer likitoci suka dai-daita numfashi na amman ina wani stage wanda addu'ah kawai na ke buƙata,waya ta dana ajje i'ta ce ta fara ringing yaya Aliyu ya ɗauka yaga an saka mamana,shahada ya yi kawai ya ɗauka ya kara a kunnensa hawaye na fitowa daga cikin idanuwansa. "Haba khairat me yasa ki ke ajje wayarki ne ki tafi wani wajen ina ta kiranki baki ɗaga ba"?.hankalin yaya Aliyu ne ya ƙara tashi ya ce"a'aaa mama ni ne Aliyu ne". Gaban mama ne ya faɗi sosai ta ce"a'a to ina khairat ɗin"?. Kasa haɗa kalma ɗaya ya yi wacce mama baza ta gane komai ba,ya yi dauriya ya ce"eh daman na shigo ne yanzu ta ajjs wayar a farlo i'ta kuma tana maƙontanmu nan". Ajiyar zuciya mama ta yi sannan ta ce"to ka aika mata da wayar inason muyi magana da ita ne"?. Jikinsa ne ya yi sanyi sosai da jin abinda mahaifiyarsu ta faɗa bakinsa yana rawa ya ce"am daman mama ni yanzu zan koma da gaggawa ne na kai khadija asibiti labour take".ya faɗi hakan yana jin bai ƙyauta ba ƙaryar da ya yi wa mahaifiyar tasu. "Ayya to Allah ya sauketa lafiya,to nima ina kan hanya insha Allah daman suprise na yi muku,ni da mama muna kan hanya". Gabansa ne ya yi mummunar faɗuwa da ƙer ya aro dauriya suka yi sallama,ya leƙa khairat wadda aka saka mata oxigien saboda numfashinta da ya ke tafiya ba dai dai ba. Wasu hawaye ne suka zubo masa yasa bayan hannunsa ya goge,ya samu kan wani benci ya zauna yana kallon kyakkyawar fuskar ƙanwarsa wadda ke kan screen ɗin wayarta,ya shafa fuskarta a hankali yana kuka ya ce"sister Allah ya baki lafiya,Allah ya tona asirin waɗannan mugayen mutunen waɗanda sukayi silar rashin lafiyarki,da kuma silar mutuwar auren mahafiyarmu." fashewa da wani matsanancin kuka ya yi,yana jin zuciyarsa na yi masa zafi sosai,yana zaune yana kukan wata nurse ta fito cikin farin ciki ta ce"congrat munyi nasarar cirowa matarka babynta mace yanzu haka uwar na ɗakin hutu,babyn kuma tana nan." Bin nurse ɗin ya yi har ɗakin ya hango kyakkyawar babynsa sai wulga fararen hannayenta take fafare ƙal,kamanninta da khadija kamar ta yi ka ki komai iri

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87