Chapter 49
Chapter 49
musu baki damu dasu ba,sannan ki yi duk yadda za ki yi ki karɓe mijinki chas a hannunki,sannan wannan sirrin na ki ina so ya tsaya daga ni sai ke,don bana son kowa yaji". Murmushi sosai na yi cikin dakiyar zuciya na ce"insha Allah anty zanyi yadda ki ke so".murmushi ta yi muka cigaba da girkin namu. Muka zuba a babban faranti muka fara cinsa cikin nutsuwa har muka gama,na koma kitchen na wanke kayan tas.na dawo muka hau hira,ta ce"khairat gobe zan aiko ƙanwata ta kawo miki wani turare,ki daure ki yi amfani dashi don Allah kada ki bani kunya." Ɗaga mata kai na yi ina jin daɗin haɗuwa da ita,don ba don ita ba da ban san yaya zanyi ba,don yadda na ke tsoron yaya Bilal ko Babana bana tsoronsa haka. Halisa tana komawa gida ta shiga haɗa abubuwan da zata aikowa da Khairat,har wasu shegun ƙananun kaya waɗanda ra siya ƙwanan nan wanda bata yi amfani dasu ba,har kayan bacci duk da tasan khairat ɗin na dasu,ta haɗa su duka ta aika gidansu akira mata ƙanwarta Xeenatu. Turaren kuma oder ɗinsa ta bayar aka kawo mata,don daga saudia ake kawo turaren,halartaccen turare ne wanda ake shafawa ajiki musamman don jan hankalin mijinki". Mai suna miskil Zawaaj,turare ne mai matuƙar sanyin ƙamshi da jan hankali. **** ai kuwa ina dawowa daga makaranta na tarar har Xeenatu tazo,bayan mungaisa ne take sanarmin ita ce wadda Halisa ta aiko,murmushi na yi mata muka ƙara gaisawa sosai,an ciko min wata ƙatuwar bakko wai duk kayan ne aciki,idan ban gane ba in kirata awaya. Naji daɗi sosai tun Xeenatu na nan na fara gabatar da wasu abubuwan,ni da kaina sai da abin ya yi min cif sai naji jikina duk asake kamar nasha wani abu da zai ƙara min wani armashi ajiki na. Na saka wasu ɗamammun riga da wando,wanda ni da kaina sai dana ji kunyar yin hakan,dirina ya fito ɗas ɗas kamar wata ƴar bebi,hmm tuni na ɗauko turaren da ta aikomin na bulbulasa yadda ya kamata,tuni jikina ya kama ƙamshi sosai,na saka after dress akai,saboda zan raka zeenatu na yi kyau sosai,na samu wani plat ɗin takalmi na wanda ya yi min kyau,na rako ta muna hira. Dai dai nan hancin motar Yaya Bilal ya danno na yi gefe ina wata irin tafiya ina rangaji tare da girgiza jikina kamar wata macijiya,ko kallon saahensa banyi ba na fara taunar cinguim ɗin bakina yana bada ƙara ƙararas ƙararas,ina hangosa naga yana yimin wani kallon cikin ƙasa,sai da ya cire glass ɗinsa yana wani yimin kallon ƙasa ƙasa. Tuni na yi gaba nazo dai dai inda ya faka motarsa na wuce ko kallonsa banyi ba,Har na raka Zeeenatu na dawo na wuce har ta kusa dashi ina girgiza mazaunai na wuce,zuciyata sai bugawa take sai dai wani ɓangaren na zuciyar tawa yana bani ƙwarin guiwa..... .✍🏿 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 [23/09, 16:23] Miss Green🍀: *57. . . . . .58* Da sauri ta ɗaga hannayenta za ta mare ni,na riƙe hannunta da ƙarfu har sai da ta yi kuka,sannan na yasar da ita awajen na cigaba da motsa jiki na,duk yana kallon abinda ya faru,ya taso ya kalleni ransa aɓace ya fara magana"ke baki da hankali ne zaki jefar da ita?". kallonsa na yi sosai sannan Na ce"ikon Allah yanzu kai baka ji kunya ba?kazo wai zaka shigarwa matarka faɗa?ita baka ga abinda ta yi ba?wato ni gani mara galihu sai ta mareni ta takani yadda take so ko?to wallahi ahir ɗinku daka kai har ita,don ba ƴar aiki aka kawo muku ko baiwa ba". Ganin yadda na yi mai ne yasa yaja hannun jidda suka yi sashenta,ta zube kan tiles tana ce wa"Allah ya isa na wannan muguwar yarinyar mai kama da basamudiya ta yi min targaɗe". Da sauri Bilal ya ce"ke kada ki ƙara ce mata basamudiya,don ƙanwata ce kinga kuwa zubina tayo".da sauri Jidda ta tashi cikin fushi ta ce"hmm ai wallahi tallahi wannan matakin daka ɗauka agidan nan ba zai maka kyau ba?ai naga ce wa kayi ko kallonta ba zaka yi ba,ashe duk ƙaryar bogi ce.har da yimin alƙawari gashinan tun ba'a kai ko'ina ba ko'ina ba kayi fatali da alƙawarin daka ɗaukarmin". Kallon banza ya yi mata sannan ya ce"Jidda kada fa ki faɗamin zancen banza,wannan yarinyar itama matata ce kamar yadda ki ke,kuma inaso ki saka aranki daga yau zan koma wajen matata,in neme yafiyarta akan duk abinda na yi mata,haba ai na shiga haƙƙinta ma,ni narasa me ya shiga kaina yasa na yi fatali da ita na manta da ita sam,to zaluncin nawa bai kai nan ba,ke bakya tunanin in mutu in tashi da shanyayyen gefe?ke murna zaki yi ko?". "Hhhh ai wallahi Bilal baka isa kace yau zaka koma wajen wannan ƴar iskar yarinyar ba?ai ba haka muka yi da kai ba?Bilal yau ka nuna min ce war namiji baɗan goyo bane".ta faɗi hakan tana jan kwalar rigarsa. Fincike fici ficin hannayenta ya yi tayi gaba tayi baya kamar za ra faɗi,tana hawaye ta ce"Allah ya isa tsakanina da kai Bilal wallahi sai Allah ya sakamin,ƙara fincoka ta ya yi kamar kayan wanki sannan ya ce"ki shiga hankalinki jidda sam ni ban zama lusari har haka ba,da xaki mayar dani sa'anki duk maganar da tazo bakinki ki faɗamin ita,ita khairat ɗin da ki ke zagi bata fiki ba?,ki duba sosai ki gani." Yana faɗar hakan ya haye sama,bai fi mintina kaɗan ba sai gashi da waau sabbin kaya a hannunsa ya wuce ta,da sauri ta taso zata wurgar da kayan hannunsa,ya riƙe hannunta har sai da ta saki ihu awajen sannan ya yi tafiyarsa,yana jin haushin rashin tarbiyyar da jidda ke gwada masa,ada ya ɗauka babu wata mace a idonsa sai jidda amman a yanzu khairat ya ke gani acikin idaniyarsa. Na dawo daga training kenan,na shiga wanka har na fito,sai naji ana danna bell don na saka sakata aɗakin,don tunda ya fara hakan zai iya cewa zai shigo,ya yimin rainin hankali akan matarsa.ni kuwa ba kyalesu zanyi ba. Da mamaki na buɗe ƙofar a tunani na ma ko baƙo na yi,a tsaye na gansa da babban aƙwati na kaya,na kasa matsawa ko nan da cen,na kallesa na ce Lafiya mlm ya dai?." Banza ya yimin sannan ya ce"matsamin in wuce,gidanki ko gidana"?.murmushin gefen baki na yi irin na muguntar nan sannan na ce"hmm ai wannan gida gidanka ne da kai da matarka,sai kuma ƴar aikinku khairat,na faɗi hakan ina matsa masa ya shigo. Bai kulani ba naga ya yi hanyar ɗakinsa,ikon Allah daman yasan da zaman ɗakinsa anan gidan?da ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87