Chapter 41
Chapter 41
ƙasa,na wuce banɗakin na ɗauro alwala sannan nazo na tada Sallah na yi raka'a huɗu,sannan na ɗaga hannaye na sama ina roƙar ubangiji ya kawo min sauƙi acikin lamarin aure na,ya cusawa yaya Bilal sona wanda har yafi ƙarfin son da na ke masa. Na shafa addu'ar ina kuka,Rashida da ke kusa dani ta kalleni ita ma hawayen take muka shafa addu'ar tare. **** Washe gari da wuri su Rashida suka fara shirinsu,ni kuwa sai bacci na ke mai cike da son Yaya Bilal,wai gamu da wasu fararen yara aƙasan wata bishiya mai kyau muna lilo gwanin sha'awa. Rashida ta ce"ikon Allah sai kallo mu duk mun tashi mun shirya amman ke da ki ke matsayin amarya sai baccin asara ki ke?ta faɗi hakan tana tashi na,miƙa na yi sannan na tashi ina salati. Kai tsaye banɗaki na shiga na shiga na yi wanka tare da brush,don na yi sallah tun asuba tare da yin azkhar ɗina na safiya,wanda kuma wannan tarbiyyar gidanmu ce,duk wani yaro ko babba da asuba ya ke salla tare da karatin qur'ani da kuma azkhar. Ɗaya daga cikin kayan da Hajiya kaka ta bayar aɗinkamin na ɗakko shadda ce fara sol,wacce ta gaji da aiki ga shi tasha tsone work,ɗinkin doguwar riga,ni da mero ta bayar aka yimana,amman ita mero nata kalar ash ce shaddar. Munyi kyau sosaj sai ɗaukar ido muke,na fito daga ɓangarenmu sai sheƙi na ke,lalle na ya yi kyau sosai a hanya muka haɗu dasu Salimat da Iman,duk suna da cikinsu har ya fito ma,Salimat ce ta yi dauriyar ce wa"oh su khairat amarya?babu magana ne?". Banyi niyyar yi musu magana ba,na gaishesu iman tana wani cin magani ta wuce gaba tana ce wa"hmm Allah dai yasa cikin ya fita kada akaiwa wani gidansa".ta faɗi hakan tana hararata. Sosai naji zuciyata ta yi wani irin zafi,na wuce ina goge ƙwalla acikin idanuwa na,kai tsaye na wuce sashen Hajiya kaka. Ɓangarenta acike sosai na wuce cen cikin ƙuryar ɗakinta ina gaida mutanen da ke wajen,ɗakinta babu kowa aciki ashare a goge sai tashin ƙamshin turaren wuta ya ke,daman Hajiya kaka aƙwaita da tsaftace waje. Na baje akan gadonta tare da cire golden ɗin mayafina,na cire awarwarona da ɗan kumne na cire kayans nabar iya under ɗin dake jikina,na hango kayan lefena akan sif ɗin hajiya kaka saiti tara cif,wanda daƙer yaya Bilal ya yi lefan wai shi bashi da kuɗi,alhali ko ƙwanan nan an ƙara masa matsayi kawai dai bai so na ne shiyasa zai ce hakan,jidda kuwa abakin mutane naji ana cewa dozin biyu ya yi mata. Na rintse idaniya ta ina kiran sunan Allah,a haka wani bacci mai nauyi ya ɗaukeni,sai da naji Hajiya kaka na tashi na tana ce wa"ikon Allah wannan amarya da lalaci ki ke,ga mero cen ta shige cikin gida ana ta hotuna da ita,ita da ma yaushe tazo gidan?amman ke da kika rayu agidan kina nan kina wani baccin asara. Banɗaki na shiga na yi wanka na fito Hajiya kaka ta ce"buɗe cikin sif zakiga wata atamfa super ɗakko ta ki saka, jiya na amso miki ita,amman banda mero saboda ita na barta ta saka kayan lefanta saboda ita babu rashin mutunci aciki,amman Ruƙayya ji bi lefan da ta haɗo miki duk aƙwatin bai cika ba,ai wallahi baza ko saka ko ɗaya ba,ana gama bukin zan mayar mata tsiyarta,don itace matsiyaciya don ni dai ban gada ba,ɗinki kala goma na yi miki ki yi ta sakawa kina fita,kuɗi na ware sosai na bawa Rashida ta yi komai,sai da aka ɗinka sannan ta kawo min,yarinyar arziƙi wacce bata yo mugun hali irin na uwar taba. Ni dai ina jin hajiya kaka bance komai ba,na shirya cikin atamfata blue da kuma ratsin brown ɗinkin riga da zanine amman ɗinkin ya yi ƙyau sosai,musanman ma dana saka kayan na yi ƙwalliyata simple na ɗaura ɗan ƙwali na akan ƙwantaccen gashina wanda yasha saloon sai tashin ƙamshi ya ke. Rashida ta shigo tana dariyar tsokana ta ce"to Alƙawarin Allah ya cika an ɗaura auren Rahama da kuma Bilal". Wani irin faɗuwar gaba naji,yanzu shikkenan an ɗaura aure na da Yaya Bilal?yanzu shikkenan na zama matarsa?mun zama abu ɗaya?tuni hawaye suka fara ƙwaranyo min kamar an buɗe bakin fanfo. . .✍🏿 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 [23/09, 16:21] Miss Green🍀: 45. . . . 46 Rashida ce ta share min hawayen ta juyo da fuska ta tana kallona sosai ta ce"Khairat wannan kukan da ki ke ya yi yawa,don Allah ki daina kinji"?.Ta faɗi hakan tana kallon cikin idanuwa na,a hankali na ce"to na daina sis Don Allah ki yafemin kinji". Dariya ta yi sannan ta ce"a haba matar yaya ai bata laifi,yanzu dai tashi mu fita waje ana ta hotuna bakyanan,waccen rasai ɗin matar yayanki mero tana cen gindin camera ana ɗaukar hoto,abin dariya Yaya Salim yaƙi fitowa yana cen wajen abokansa,wai kunya ya keji kada araina sa don ya auri mero". ta faɗi hakan tana jan hannuna,murmushi kawai na yi mukazo muka wuce ta kusa dasu Hajiya Kaka ta ce"yauwa Rashida fita da ita,don ni na gaji da zaman ta aɗakin nan". "Cikin shagwaɓa na ce"au yanzu Hajiya kaka har kin gaji dani ko"?.murmushi ta yi sannsn ta ce"haba Me sunana yaya za'ayi in gaji dake?ai hakan ma bazai yiwu ba". Hotuna sosai aka yi mana,mamana da ƴan uwanta duk sunzo an ɗaukemu hotuna,da yaya Salim da Yaya Aliyu da autanmu maher duk an ɗaukemu hoto gwanin sha'awa. Duk abinda muke yi a idon su Hajiya Iklima,ta ciji laɓenta har sai da taga jini ya fito,Anty kishiyarta ta zaro idanuwa waje ta ce"ikon Allah Iklima jini fa na ke gani abakinki"?.ta faɗi hakan da mamaki. "Hmm Za kiga abinda ma yafi jini abakina,matuƙar ina ganin matar nan da ƴaƴanta sai inji kamar zan mutu saboda baƙin ciki,a duk duniya babu halittar dana tsana irin Zulaiha da kuma ƴaƴanta musamman waccen baƙar ƴartata,na tsanesu tsana mafi muni arayuwata". "Ai ba ke kaɗai ki ka tsanesu ba,nima na tsanesu wallahi,duk wani iyaye na Zulaiha yanzu ai ya zama tarihi,wai ita wadda miji keso ta dinga wani iyawa,yanzu ina iyawartata take?kinga kuwa ai ko yanzu ɗan koli yaci riba wallahi".Anty ta faɗi hakan tana hararar mama wacce ma bata san wainar da ake toyawa ba,da Rana aka kira masu kiɗan ƙwarya sosai suka ƙware wajen sana'arsu,aka sakamu a tsakiya nida mero,ai tuni amarya mero ta ware ta zage tana ta muskuta mazaunai kamar ba amarya ba,ina ta taɓa ta wai kada ta yi amman ina rawar take ta yi,ko ajikinta. Hajiya kaka sai liƙi take ta mana,musamnan ma ni,atarihi babu wani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87