Chapter 29
Chapter 29
433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com [23/09, 16:19] Miss Green🍀: [03/09, 20:31] Ummu Maher(Miss Green): [03/09, 20:19] Ummu Maher(Miss Green): *🥚ABIN CIKIN ƘWAI* NA💋 UMMU MAHER(MISS GREEN) 29🟨30 . . . ."Na tsane ki zulaiha tsana mafi muni arayuwata,kin cutar dani kin cutar da iyali na,akanki na yi faɗa har da mahaifiyata ashe sakayyar da zaki yi min kenan?kin san ƴarki na da ciki amman don mugun hali baki taɓa faɗa min ba?ki ka barni a ƙudundune?to cutar ta yi haka,ayau ba sai gobe ba na ke son ki bar min gida na." yana faɗar hakan ya fita cikin fushi har yana haɗa hanya,hajiya kaka ta ce"haƙiƙa wannan abin ya bani mamaki kuma ya ɗaure min kaina,bana fahimtar komai?wutar kaina baki ɗaya ta ƙone,wallahi ko mutuwar mahaifiyata bata kai wannan abinda na riska acikin jikokina ba,tunda ita dai nasan mutuwa ta yi ba abin kunya ta yi ba,khairat mun nuna miki so da kuma ƙauna amman abinda zaki saka mana dashi kenan?to babu komai kije duniya ce ta ishi bawa riga da wando,ke kuma zulaiha da ki ka ɓoye mana komai kije ke da Allah shine zai yi wa ɗana sakayya". I'tama tana faɗar hakan ta fita tana kuka,jirin da na ke jine naji ya ƙara hawa sosai bibbiyu na ke ganin mutane,tashin hankali da kuma ɗimuwa sun cika doɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwa ta wadda ta kasa ɗaukar komai ayau.ni kaina tambayar kaina na ke akan wannan ƙaddarae da ta afkamin balle in amsa tambayar wani?. motsi mai ƙyau mamana ta kasa yi kuka kawai take tana kiran sunan Allah,shekara 30 kenan tunda ta shigo dangin Malik take ganin abubuwa kala kala,na rashin ƙyautawa daga danginsa wai don ita tuba ce. "Hmm daman wannan ranar na ke jira zulaiha,ranar da zanga ƙarshen wayonki da kuma makircinki,wai ke mai sanin miji,mai kuma tattalin miji,wacce miji yafi so,hmm sau gashi tun kafin akai ko ina kin fara ganin sakamakonki,muɗin dai da ki ka gani a gidan dole a tafi a barmu,sha-sha kawai". Mama iklima ke faɗin haka mahaifiyarsu nadiya,ita kuwa anty maman iman ce wa ta yi"hmm ni fa wallahi wannan hukuncin ma baiyi min ba,so na yi ya lakaɗa musu ɗan banzan duka daga ita har ƴar banzar ƴar ta,shegiya me yawon karuwanci,yanzu kinga ai sai asan yadda za'ayi,kin ɓata mana sunan gida yanzu za a dinga kallonmu a wofi". Caraf mama iklima ta amshe"La-la-la ni fa ko ajikina wallahi tunda dai ba ƴata bace cen su ƙarata uwarta ta ɓatawa suna amman ba mu,haka kawai aka ƙalawa ƴaƴanmu sharri a banza yanzu gashinan ai ƴarki har abin kunya ta yi". Asanyaye mahaifiyata ta tashi da addu'ah a bakinta,mahaifiya ta macece mai yadda da ƙaddara ta kallesu kamar babu wani abinda ya dame ta ta ce"Iklima &mariya ku kasance masu faɗin alkhairi akan ƴaƴan wasu,sai kiga kuma naku ƴaƴan sunyi albarka amman ba zagin ƴaƴan wasu ba,matsalar khairat ni ta shafa ba wani ba,kuma mutuwar aure ba ku aka saki ba ni aka saka don haka wannan ba matsalarku ba ce,ku fita daga ɗakin nan". ta faɗi hakan cikin ɗaga murya". Dukkansu sun tsorata da canjin yana yin Zulaiha,donbata taɓa yi musu koda musu bane,amman yau ita ce har da ɗaga musu harshe". "hmm zulaiha kina borin kunya ne dai kawai saboda asirinku ya tonu ke da gantalalliyar ƴarki ƴar daɗi maza,to kodai baki ce mu fita ba yanzu zamu fita daga wannan ɗakin shaiɗaniyar ƴar ta ki don haka mu mun fita kada ma garin tsayawa wata masifar ta shafi namu ƴaƴan don ku ba alkhairi bane acikin al'umma. Da sauri suka fita don sunga yadda mode ɗin mama ya canja sosai kada silar tsayawarsu ta yi musu wani abin. Kulle ƙofar gam mama na ta yi sannan ta matso inda na ke,numfashi na yana fita da ƙer ta kalleni fuskarta sam babu annuri ta ce"khairat kin bani mamaki kuma kin bani kunya,haƙiƙa ban taɓa zaton haka daga gare ki ba,yaushe ki ka lalace?yaushe ki ka zubar da tarbiyyar dana baki?haƙiƙa khairat na ji matuƙar kunyar kaina da kuma mutanen da suka yarda da ke ɗari bisa ɗari". ta juya min baya ta ce"khairat ki faɗa min wanda ya yi miki ciki har ki ka yi ɓari?idan har ki ka ƙi faɗamin to Allah ya i'sa tsakanina da ke,kuma na cire ki daga cikin ƴaƴa na".sai ta juyo tana fuskanta na. Tausayin khairat ya cika zuciyar zulaiha,uwa da ɗa kenan amman a fuskarta rashin imani tsantsana ta nuna wa ƴar ta don ta faɗa mata gaskiyar abinda ya faru. Bakina yana rawa na ce"haƙiƙa mama wannan rana har tafi ranar mutuwa ta zafi,bantaɓa tunanin ko da a mafarki zan tsinci wannan rayuwar ba,ban sani ba ban san kuma me ya faru dani ba?ni dai na tashi na ji ni a baƙon yana yi,ban taɓa zama na minti goma dana miji awaje ɗaya ba,mama kin sani koda saurayin ma na yi to ya zamar min dole in faɗa miki,don ban saba ɓoye miki komai ba,tun yarinta na har zuwa yanzu,wallahi mama ban taɓs kusantar wani ɗa najimi ba?me zan gaya miki yanzu ki tabbatar da hakan?". da sauri mama ta juyo ta ce"khairat tashi in duba ki"?. duk da halin da na ke ciki sai da na shiga ɗimuwa sosai akan hakan,duk da mahaifiya ta ce amman da tsananin kunya,tunda dai yanzu ni ba ƙaramar yarinya ba ce". tsawa ta bugamin da ƙarfi,da sauri na tashi daman rigar bacci ce ajikina na ciresa baki ɗaya. Kallona sosai take da mamaki,babu wata hanya ko kaɗan daya nuna khairat ta taɓa kusantar ɗa namiji,grady a matsayin budurwa taje cikakkiya. Shiru mama Ta yi ta kasa ce wa komai,ta tafi tunanin wani abu daya shuɗe,tabbas jiya taga hajiya iklima na barbaɗa abu a ƙofar ɗakin khairat amman bata san kome ye ba,da sauri ta fita waje kai tsaye ɗakin hajiya iklima ta shiga,zuciyarta har wani bugawa take,lallai hajiya iklima ta taɓo ruwan dafa kanta,don yau za ta nuna mata ko da yaya kurna tafi magarya daɗi. Sosai ta tsorata da ganin zulaiha,tos wani ɗan ƙwalba da ta ɗakko ya fashe,tsoro sosai ya fito daga idanuwan hajiya iklima. Bakinta na rawa ta ce"zu. .zu. .zulaiha ms ki ka shigomin ɗaki"?.bata i'da gamawa ba zulaiha ta shaƙo wuyanta sosai har dai da ta kaita bango tana kakkarin aman wahala,cikin ɓacin rai da baƙin ciki zulaiha ta ce"kina tunanin Allah zai barki da abinda ki ka yiwa jinina?yarinya bata ji ba,bata gani ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87