Chapter 60
Chapter 60
gidan ubanki ne,duk wanda zai yi miki gori ya yi miki,nidai na baki goyon bayan duk wanda ya yi miki kada ki barshi kema ki rama kinji"?. Ɗaga kaina na yi sannan na ce"gaskiya ne Yaya Aliyu awannan karon na saka tsoro araina da tunanin abinda mutane zasu iya faɗa akai na amman yanzu kome za suyi sai dai suyi amman agidan ubana zan zauna,babu kuma wani tsoron da zanyi tunda dai nasan abinda ake zargina akanshi sam ban aika tashi ba" . Ahmad yana jinmu sai kuwa ya ce"khairat su mutane daman idan kace zakaji tsoron su to sunfi son hakan,gwara ka dage ka amshi ƴancinka wanda ka rasa awajensu.ki nuna musu cewa kefa yanzu an daina cutarki ki bari,za kiga kowa yana jin tsoron haɗa hanya da ke." Sosai naji daɗin shawarar daya bani,Rashida ma ta goge hawayen fuskarta sannan ta ce"haka ne khairat duk abinda suka gaya miki,amman gaskiya Yaya Bilal bai kyautawa kansa ba,amman ni nasan aƙwai ranar nadama".murmushi kawai na yi sai naji zuciyata duk ta wanke. Na ce"insha Allah zanyi ta bincike har sai na gano duk wanda ya shiryamin wannan ƙulalliyar".murmushi Ahmad ya yi sannan ya ce"khairat kenan ki barsu da Allag yafi ki rama da kanki don ramawar zai zamo kamar kin raina hukuncin Allah ne,abinda na keso da ke shine ki nutsu sosai ki dage da addu'ah babu dare babu rana,wallahi khairat na baki wasu ƴan ƙwanaki ƙalilan sai kin bani labarin abinda zai faru,don haka ki manta da wannan abin." Murmushi na yi najin daɗin shawarar Ahmad na ce"babu komai insha Allah yaya Ahmad zanbi shawararka kuma zanyi duk yadda kace inyi".murmushi ya yi sannan ya ce"good girl yanzu na hangi Khairat ɗina".da sauri na kallesa jin abinda ya faɗa shi kuma sai naga ya yi murmushi tare da tashi tsaye ya sanya hannuwansa biyu cikin aljihunsa sannan ya ce"to ni zan tafi yanzu saboda ayyukan dana bari a office,Khairat Allah ya baki lafiya,ni zan tafi". Murmushi na yi sannan na ce"na gode Yaya Ahmad Allah ubangiji yabar zumunci".ya amsa da amin suka yi sallama da Yaya Aliyu sannan ya tafi,har ya tafi kallonsa na ke sai naji Yaya Aliyu ya yi magana sannan na juyo. ****** da wata baƙuwar number aka kirasa ya ɗaga,kai tsaye yaji muryar Alhaji Damas yana ce wa"kai ƙaramin ɗan rainin hankali,ka sani koda ka ceci wannan yaran to baka isa ka ceci mahaifinka ba,wanda ayanzu yana kan hanyar dawowa gida,amman kuma ƙarshe bazai dawo gidan ba,sunyi sallana bye bye".ya faɗi maganar cikin salon dabanci. Da ƙarfin gaske Bilal ya kira sunansa sannan ya ce"kai mutumin banza la'anannen Allah,har kana da wani iko wanda ya wuce ikon Allah ka sani na bawa Allah ajiyar mahaifina shine zai karemin shi,don haka don Allah idan kaso ka kasheshi ko yanxu,komai yana tafiya ne da ikon Allah ba da ikon wani chan ba.don haka ka yi duk abinda ka yi niyya".yana faɗar hakan ya kashe wayar hankalinsa a mugun tashe. Jidda da ke kallonsa ta taso cikin salo nason mantar dashi komai ta matso kusa dashi sosai zata taɓa sa,da sauri ya ɗaga mata hannu alamar bai buƙatar hakan,ta mayar da wani malulun haushi daya turniƙe mata xuciyarta cikin fushi ta fara magana"ai daman tunda wannan tsinanniyar ta gama da kai dole ka dinga yimin duk wulaƙancin da kaga dama,babu komai insha Allah kaima za kaga ƙarshenka,don Allah baya barin azzalumi irinka".. Da sauri Bilal ya miƙe ya ce"ke!jidda kada ki ƙara kirana da azzalumi idan kuma har ki ka kuskura ki ka ƙara kirana da wata kalma da bata yimin ba,to tabbas zanyi miki duk abinda bakya tunani".da sauri ta ce"to se me idan ka yimin?rashin mutunci ai ka gajeshi ne wajen wannan munafukar kakar taka". . .wani mugun mari ya wanka mata wanda har sai da taga hasken wucewar wasu taurari ta ɗauke wuta lokaci ɗaya saboda marin ba ƙaramin shigarta ya yi ba,ya ce"ki shiga hankalinki jidda kinga duk zagin da zaki yimin ki yishi a iya ni kaɗai amman ki ka sake kika saka wannan kakar tawa to tabbas zan miki abinda sai kinyi nadamar faɗar duk wata mummunar maganarki,domin ita dai wannan kakar tawa da ki ke ganinta,ina matuƙar ji da ita aciki n rayuwata,yadda na kejo da iyaye na to ita fiye da hakan na ɗauke ta,don haka matuƙar ki ka ƙara zaginta to wallahi abakin aurenki". Sosai abin ya bawa jidda mamaki kamar wani wanda aka yiwa asiri ta kasa gane kansa ko kaɗan,tabbas ashe da sauran rina a kaba,ya zama dole shima ta yi maganinsa kamar yadda ta yi maganin matarsa,ta yadda sai yadda ta yi dashi ya zama mijin tace hatta ita kakar tashi ma sai ya manta da ita. Tuni ya fice ya figi motarsa da mugun gudu,masu gadin sai mamakin ogansu suke don sunga gudun ya yi yawa,tun a mota ya kira Captain ringing ɗaya ya ɗauka,ko gaisuwar Bilal bai bari sunyi ba,ya faɗa masa duk abinda Damas yace masa yanzu awaya.Captaim ya ce insha Allah yanzu zanyi shiri in taho,insha Allah ƙarshen Damas yazo. Kai tsaye gidan Damas ɗin ya wuce,hatta gate ɗin wanda ya ke buɗe alamar yana nuna yanzu aka shigo ba'a kai ga rufesa ba,tuni Bilal ya ɓurma gidan da matsanancin kudu,masu gadin suka taho da sauri zasu rufe gate ɗin amman tuni Bilal ya shige ciki,Damas yana zaune a babbar fadarsa ya ɗaga kai ganin Bilal ya shigo da motarsa har Kusa da babban falonsa. Ya yi wata muguwar dariya irinta basawa,ya kalli Mahaifin Bilal ya ce"oh Allah sarki Alhaji ka godewa Allah ɗanka yana sonka sosai,tunda gashi har yaxo don kaucewa muguntata."Alhaji Abdullahi ya yi dariya sannan ya ce"haba bawan Allah ai duk ɗan halak ba ɗan shege ba yana don iyayensa,don haka kada ka yi mamaki don ka gansa,abinda yafi haka ma zai iyayi indai har akai na ne". . .ko kafin ya gama maganar har Bilal ya diro Falon. Alhaji Damas ya saka wata mahaukaciyar dariya ya ce"hhhhh Bilal kenan ta yaro kyau take bata ƙarko,don haka yanzu zan nuna maka isa ta akan mahaifinka,tuni ya yi wani fito sai ga wani mutum ya fito daga bayan mahaifin Bilal ya caka masa wuƙa.da wani irin mugun gudu Bilal ya taho Wasu majiya ƙarfi suka rirriƙe Bilal. Bilal ya ce"don Allah kada ku kashemin mahaifina wallahi ba shifa laifi akan komai".dariya sosai Alhaji Damas ya yi,dai dai lokacin kuma Captain ya bayyana da wasu ma'aikatsn suji sunfi mutum hamsin.wata irin sufa Bilal ya yi,ya hanɓare wannan wuƙar ta hannun wannan mutumin,tuni Alhaji Abdullahi ya faɗo kan ɗan nasa Bilal ya tare mahaifinsa yana kuka,don a ƙa ida idan abu ya faru da mutum irin haka to kada a yadda ta faɗi ƙasa ataresa da sauri,yin hakan zai sauƙaƙa masa komai. Captain yana shigowa ya saki uwar wuta shida sojojin da suka shigo ko ta ina sun saki wuta,ana ta ɗauki babu daɗi tsakanin Su captain da kuma yaran Alhaji Damas,Yana ganin haka tuni ya danna layar ɓatansa ya ɓace batt awajen,Captain ya daki iskar wajen yana jin haushin rashin kama Damas. Kai tsaye Bilal asibiti ya yi da mahaifinsa yana kuka sosai,jini sai malala ya ke ajikin Alhaji Abdullahi,Bilal ya kasa gayawa kowa abinda ya faru gudun kada hankalinsu ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87