Chapter 70
Chapter 70
zai yi,ya duba yaga su mama basa nan faɗowa ɗakin kawau ya yi yaga Haidar sai uban kuka ya keci,yana ta saka hannunsa a baki,alamar tunwa ya keji,su kuwa sauean baccinsu suke amman ganin haidar na kuka suma sai suka fara,haka suke min duk abinda ɗaya ya yi to ɗaya ma sai ya yi,haka suke da daddare su hanani bacci sai tsotso,da rana ne na ke samun lokacin bacci don ko da yaushe suna hannun mama ta riƙesu insha bacci na. jin zuciyarsa ya yi tana mugun zafi,to ina suka yi suka bar masa yaransa?ya ɗaukesa yana rarrashi tunda su nasu bai kai nashi ba,ya kira Nusaiba da Amira ya ce su ɗakko masa su duka.ai kuwa haka aka yi suka ɗaukesu suka fita dasu. Shima ya fita daga ɗakin ya buɗe mota ya shiga da haidar a hannunsa Amira,da Nusaiba sai ƴar baba ƙasim Suwaiba,ya ce su shiga bayan motar,suka kuwa zzazauna sai asibiti,yana zuwa ya kira likitan da ya yi masa magana kan ingantacciyar madarar da za'a dinga bawa yaransa,saboda ya lura suna shan yunwa,don wai yaga har sai an rarrashi Khairat sannsn take basu mama susha,abin nan yana bashi haushi don dai babu yadda zai yine,don ko ƙurarsa Khairat bata kalla. Ina fitowa daga wanka lokacin su mama suka shigo har da hajiya kaka,da sauri na kalli inda na ajje yarana naga babu su,tuni na fara kuka ina ce wa"na shiga uku na ni khairat waye ya shigo ya ɗaukesu?".na faɗi hakan ina muxurai ina jin zuciyats kamar zata fito saboda azaba. Hajiya kaka ta ce"a'ah to waye kuwa zai ɗaukesu sai dai ubansu,wataƙil kin barsu suna kuka ne shiyasa,jiya ma wallahi ya kawomin ƙararki,bakya kula masa da yaransa,kinga kuwa bazaku shirya ba".da sauri na ce"o ho shine ya samu damar zuwa ya ɗaukemin su?ya sakani cikin tashin hankali saboda shi damuwarsu suna kuka ko?to duk ranar dana bar masa waje na ce yazo ya kula dasu iyawa zai yi?amman duk a haka bai gani ba shinr yazo ya ɗaukesu ko?to babu laifin haka.xan bar masa yaransa ina shikkenan ko?sai ya samar musu uwarda zata kula dasu,tunda ni ya raina nawa". Na faɗi hakan ina fashewa da kuka Hajiya kaka ta ce"haba khairat ya zaki ce zaki bar masa yara?ya yi yaya dasu?karma ki faɗi wannan maganar wani yaji bayan mu."da sauri na ce"ok idan kun san haka me yasa zaku barsa ya tafimin da yara na?shi ya yi min naƙudarsu?ko ya fini sonsu ne?da zai ɗaikesu?to gasu nan na bar masa,ya ƙwaɗanta ya cinye duka". Na faɗi hakan ina ƙara fashewa da kuka,ita mama ma ta rasa me xata cemin,don wannan faɗan bai kamatz ta shga ba,itama fa har yanzu haushin Bilal take ji,na sakin rashin mutuncin da ya yiwa ƴarta.ƙanwar mama na ce tazo inda na ke zauna ta dafa kafaɗu na ta ce"yi haƙuri khairat kinji?son yaranne suka yi masa yawa,su maza fa haka suke kai zaka yi naƙudar yaranka amman kuma sai su fika sonsu,harma awani lokacin su nuna maka sunfi ka sonsu.don haka wannan ba wani abin mamaki bane tunda daman haka halinsu ya ke." Ko da ya dawo wucewa dasu ya yi ɓangaren mahaifiyarsa,ya zauna ransa a ɓace ya ce"wallahi hajiya bansan me ke damun khairat ba?don tana ƙina kuma sai ya shafi yara na?meye laifinsu anan?shin sune suka yi mata laifi ko ni?,to wallahi na amshe yara na,taje ta yi rayuwarta tunda haka ta zaɓa". Tunda ya fara magana Hajiya Ruƙayya bata ce komai ba,sai cen ta ce"Bilal ka taɓa ganin uwar da ta haifi yaranta taƙi su?kai ma kasan tana sonsu kuma har yanzu khairat yarinya ce. Da sauran yarinta akanta,kai da ka ke lallaɓawa kuma ina kai ina zuciya?don Allah ka rage wannan fushin,idan kuma ba haka ba ya sakaka nadama.saurin fushi yana haifar da dana sani,babu laifi idan ka zaunar da ita ka yi mata nasiha akan yadda zata kula maka da yaranka,ta lallashi da luma na amman ba ta faɗa ba,kaga ashe gyaran da ka keson yi sai ya ƙara rugujewa." Shiru ya yi kawai yana kallon idon iman wacce ke hannunsa tana ta wawure wawure tana neman abincinta,ya ce"Hajiya wallahi son da na kewa mahaifiyarsu ya yi yawa,shiyasa suma ya shafesu duk wanda zai wulaƙanta min su to tabbas ni ya wulaƙanta ba suba,don haka dole ne inyi mata faɗa ko babu komai ai ni yayanta ne."ya faɗi hakan cikin fushi. Sosai Hajiya Ruƙayya ta lallashesa har ya sakko,arayuwar duniya babu wanda yafi sanin kan yaro irin uwa,tun yana jariri take gane abinta,tun Bilal yana ƙarami ta sanshi ƙwarai da mita,ko mama ta hanashi da wuri to sai ya yi ta mita kafin ya amsa,shiyasa tun daga nan ta gane Bilal mutum ne me mita,amman bashi da riƙo ko kaɗan. Ina zaune ina xaune na yi shiru har yanzu tawul ne ajikina wanda na fito da shi daga wanka,na zabga uban ta gumi sai gasu sun shigo da yaran su Nusaiba ne suka fara shigowa,da sauri na tashi na karɓi Ahmad wanda har ya fara kuka na rungumesa a ƙirjina,bai shigo ba sai ya aiko da yaran,Hajiya Ruƙayya ta zauna abakin gadon duk sai kunyarta ta isheni,bayan mungaisa ne ta ce"Khairat da farko dai zan baki haƙuri ne akan abinda Bilal ya yi na ɗebi miki yara,amman ki yi haƙuri badon saboda ɗanane shiba zan faɗa miki kema baki da gaskiya,ki daina barinsu suna kuka don Allah idan zaki shiga wanka ki samu wani ya zauna dasu kinji?saboda irin haka fa har shaiɗanu suna shigar yara,sai kiga an rasa gane kan matsala,kuma alhali mu iyaye mu ke da alhakin kula da yaranmu,don Allah ki kiyaye kinji"?. Na ɗaga mata kai kawai tsabar kunyarta na kasa basu mama har sai da ta fita.hannuna na rawa na ɗakko Haidar da Iman na fara shayar dasu,ai kuwa zuƙar da sukemin ta yimin yawa har ƙwaƙwalwata sai da naji zafin tsotsar da suke min,na cije leɓe ina yarfe hannu. Yana tsaye jikin ƙofa yana ta kallo na,sai kuma yaji tausayina duk ya kamashi,ganin yadda na ruɗe har na rame daga ɗaukesu tabbas kenan har yanzu khairat na sonshi tunda tana son ƴaƴansa.sai da na bari suka ƙoshi dukansu sannan na sakasu a kafaɗa ta suka yi gyatsa sannan na ƙwantar dasu ina tofa musu addu'ah tuni bacci ya ɗebesu,na yi murmushi na manna musu kiss a goshinsu ina shafa sajensu wanda ya ƙwanta luf irin na mahaifinsu,tuni na tuno dashi amman kuma madadin so sai naji tsanarsa ta ƙara samun wajen zama. Na tashi ina cire kaya na kawai sai ya shigo ɗakin,ina juyowa na ganshi tsaye akaina tuni na runtuma da gudu na ɓuya abayan sif,sai kuwa ya ce"dama kinyi fitowarki don na riga dana ga komai tun ma ba yanzu ba".ya faɗi hakan yana hawa kan gadon shima yana binsu da addu'ah yana wasa da ɗan hannayensu gwanin sha'awa. Sosai na keji da tsiwa ta na ce"don Allah mlm ka fita tun kafin wallahi in tara maka mutane".ina faɗar haksn har hawaye na ke,sosai abin ya bashi dariya sannan ya ce"ok to yi ihun mana?ki tara mutanen kiga idan zan tsorata".?ganin bazai tashi bane yasa na yi saurin tashi na fara saka kayana. Ya yi murmushi ya matso inda na ke ya ce,da sauri na matsa gefe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87