Skip to content

Chapter 65

Chapter 65

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,296 words 0 views Progress saved
Download Book

baza ka taɓa yarda ba,tunda ƴar gaban goshinka ce,amman kalli wannsn hoton da kyau ka faɗamin ƙarya na yi maka"?. Da sauri Bilal ya kalli hoton,ya yi saurin ture kansa gefe yana hawaye,Jidda ce da Alhaji Damass suna shaye-shaye.kuma daga ganin hoton ba wai an ɗauka bane don a haɗa,a'ah hoto ne na ainihi,Bilal ya fara ambaton sunan Allah da duk addu'ar da ta zo bakinsa. Captain ya dafa kafaɗar aminin nasa ya ce"ka yi haƙuri Bilal nasan abin da zafi amman ka nutsu kasan inda zaka kama,ina faɗa maka sharri aka yiwa khairat amman ka ƙi yarda,kuma ka ƙi yin bincike ka tafi a haka,yanzu kaga ta yi maka babu wan babu ƙanin kaga yanzu sai kasan matakin da zaka ɗauka akan wannan muguwar matar ta ka". Bai gama jin abinda captain zai faɗa masa ba fuu ya fita daga cikin motar captain ɗin,ya shiga tashi motar ya tayar da ita cikin fushi,Allah kaɗai yasan yadda ya ke jin zuciyarsa kamar zata fito waje,Jidda daya bawa ragamar sonta da ƙarfinsa amman yau itace zata yi masa haka?har yanzu shike kula da komai na iyayenta baya ga gidan daya danƙara musu,ashe ba haka kawai yaji ya tsani jidda yanzu ba,ashe ha'intarsa take da kuma cin amanarsa. Ko da ya koma gida kai tsaye ɓangaren jidda ya yi,ya hau saman bane maimakon ya taka step ɗin ɗai ɗai to uku uku ya ke hawa saboda ya yi saurin hawa da wuri,ƙofar ɗakin ta arufe take alamar bata nan ya dawo farlo ya yi tagumi yana xaman jiranta,ai kuwa kamar haɗin baki sai gata ta shigo ko kallonta bai yi ba kansa na ƙasa yana tunanin mugun hali da rashin imani irin na jidda. Ta shigo duk jikinta ya yi mugun yin sanyi ganinsa ya yi tagumi,kuma gashi ko amsa sallamarta ma baiyi ba,hankalinta ya tashi sosai ta ɗan samu waje ta zauna ta ce"Love dafatan na sameka lafiya?daman. . . ."da sauri Bilal ya ɗaga mata hannu,ya isa inda take tsaye ya buɗe wayarsa ya fara neman wani vedio,daman kuma kafin yabar wajen Ahmad ɗin ya tura wannan vedion don kada ta yi masa musu. Tun kafin ya buɗe vedion taji gabanta na tsananta faɗuwa sosai,ya buɗe vedion ya nuno mata fuskarsa babbar wayar tasa,da sauri ta dafe ƙirjinta tana fito da ido waje,dan danan sai ta fara haɗa gumi sosai kunsan mara gaskiya sai kuwa ta ce"wa. .wa. .wallahi ba ni bace sharri aka yimin".wani irin mugun mari ya wanka mata wanda sai daya tara mata taruwar jini a gefen idonta sannan ya nuna ta da yatsansa ya ce"ki ka yarda ki ka ƙara magana wallahi Jidda zan iya shaƙeki ki mutu kowa ya huta".ya nuna mata ɗan yatsansa alamar shittt. Jikinta ne ya hau rawa sannan ya ce"Jidda ni dai babu abinda zance miki sai dai ince Allah ya isa na,kin rabani da matata sanyin idaniyata,kinyi mata sharrin zina,ashe kece babbar mazinaciya me cin amanar mutum abayan idonsa,yanzu zan nuna miki kalar muguntata jidda,zaki san ke baki iya komai na rashin imani ba,ni da nayi soja ai kinga baki isa ki nunamin kalar mugunta ba".ya faɗi hakan yana ɗaukar wayarsa.ba'afi minti talatin ba sai ga sojoji sun kusan ishirin sun shigo gidan. ******** Hamza ɗaya daga cikin masu gadin gidanne,suna zaune da matarsa ya yi tagumi sosai,Hafsat matarsa ta tsaya da cin abincin da take ta ce"miji na lafiua kuwa naga duk hankalinka a tashe idanuwanka sunyi jawur kamar ma ka yi kuka"?.ɗan murmushi ya yi wanda ake ce masa yafi kuka ciwo ya ce"Hmm Hafsa ina cikin mummunar matsala wadda ban taɓa shiga makamanciyar irinta arayuwa ta ba.Hafsa ni ɗinnan da ki ke gani na yi wata mata sharrin an kamata da ƙwarto." da sauri Hafsa ta miƙe ta rufe bakinta da tafin hannunta tuni hawaye suka fara zubo mata ta ce"Anya kuwa mijina Hamza ne agaba na?miji na me gaskiya da sanin ya kamata?anya kuwa kai ne"?.da sauri ya tashi ya riƙe hannayen Hafsa yana kuka ya bawa Hafsa labarin duk abinda ya ke faruwa. Yana gama faɗa mata taja hannunsa tana tafiya cikin fushi yana tambayarta ina za suje amma ko kallo bai ishe taba ta shiga mota ta ce"ka taho mu tafi".babu yadda ya iya da Hafsa don yana matuƙar sonta sosai. ********* Waje ya haɗu ga jidda,ga Bilal,ga khairat,ga hajiya kaka,ga masu gadin gidan Bilal sojoji,duk mutanen gidansu Bilal suna wajen,bayan sojojin sunzo wajen Bilal suka tafi gidansu Khairat ɗin,Baba Ƙasim ya ce suzo babban hall ɗinsu na gidan za'ayi meeting,to shine aka taru. Khairat kanta na ƙasa,cikinta ya fito yanzu sosai kowa yana ganinsa,tuni Bilal ya ruɗe ganin cikin jikin khairat,yaji wani mugun sonta yana yawo acikin zuciyarsa,Allah sarki ashe harda guzurin ciki ajikin khairat ɗinsa,to tabbas aurensu bai ƙare ba,tunda ba'a sakin me ciki. Baba Ƙasim ya ce"Bilal ka taramu anan wajen kuma bamu san me ya faru ba?ga matarka tana kuka ga kuma sojoji?Allah dai yasa lafiya ko"?. babu abinda Bilal ya ɓoye musu na dangane da duk abinda ya faru har sharrin da aka yi wa Khairat. Sosai kowa ya yi mamakin hakan aja shiga kallon kallo,Hajiya kaka ta nisa ta ce"oh yau ina ganin ikon Allah to meye kuka tsattsare ni da ido?gaskiya ce ai ta bayyana,anyi wa yarinya sharrin ƙazafin zina har sau biyu,yanzu gashi Allah ya wanke ta aguda ɗaya saura ɗaya". Da sauri Maher ƙanina ya ce"a'ah kaka kin faɗi ba dai dai ba,guda ɗayan ma yanzu zai tonu don bazan yarda a gurɓatawa Yaya ta suna ba".yana faɗar hakan ya fito da wayarsa ya buɗe wani vedio,da sauri Hajiya Iklima ta miƙe tana rarraba idanuwa,Abbana ya kalleta da wani irin kallo. Hajiya Iklima aka nuno ajikin wannan vedio ɗin ita da Anty kishirya ƙuru-ƙuru,Hajiya Iklima ta ce"hmm yanzu kinga mun gama da khairat harda uwarta saura wannan munafukar tsohuwar". *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 Badi'at Ibrahim _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨 Instagram links👇 https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY= Facbook group https://facebook.com/groups/463653111781414/ Telegram links https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com MISS GREEN CE [23/09, 16:29] Miss Green🍀: 81&82 . . . .hajiya kaka na shigowa na fashe da kuka Sosai,,sai kuwa taja baya

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87