Chapter 47
Chapter 47
uzurin mai wayar shiru yaji anyi don haka ya ajje wayar ya cigaba da aikinsa cikin system ɗinsa. Tana sakkowa Bilal ke faɗa mata an kira ta,ai da gudu ta ƙaraso wajen tana ce wa"wa. .wa. .waye?". Kafaɗa Bilal ya ɗaga alamar shima bai san waye ba?.ta duba number gabanta ya bada wani irin rass rass,ta daure ta tashi tana wayan cewa ta ce"au bari in hau sama na manta nan wajen sam babu network,shiyasa idan zanyi waya ta nake hawa sama".ta faɗi hakan tana yin gaba zuciyarta fal tsoro amman ta godewa Allah da Bilal ɗin bai gai ne waye ba. Tana hawa saman ta shiga ɗakinta ta kulle harda saka key,sannan ta samu bakin gadonta ta zauna,ta kira number hannunta na rawa. "Barkanki da dare mrs Bilal Admiral B". Gaban jidda ne ya faɗi sannan ta ce"ranka ya daɗe Oga dafatan kana lafiya?wallahi ɗazu wayar na bari a ƙasa na shiga wanka ashe Bilal ya ɗauki wayar?".ta faɗi hakan tana jin bugawar zuciyarta na ƙara ƙaruwa. Sosai Alhaji Damas ke dariya sannan ya ce"Banyi magana ba mrs Bilal,idan da na yi magana yau nasan gidanku Boom wuta zata tashi kinga mutum ya yi asarar dukkanin wannan aikin dana sakaki,to kinga yaya kuma zan ɓata aiki na,i zuwa yanzu kin samu wani rahoto ne?". ya jeho mata wannan tambayar?jikinta na rawa ta ce"eh ranka shi daɗe yanzu haka na samu ka jiraye zuwa na gobe insha Allah,zan masa ƙaryar zuwa gida daga nan dai inzo". Dariya sosai ya yi irin dariyar basawa,sosai jidda take jin tsoron dariyar Alhaji Damas,tana cikin wannan halin ne taji yana ce wa"yauwa kinji ina dariya ko?ba komai na kewa dariya ba sai yadda kika mayar da ƙwaƙwalwar kamar wata babyn roba,duk da basirarsa da kuma fikirarsa,shiyasa akace mace tafi shaiɗan iya annamimanci." shiru jidda ta yi don ita lamarin Alhaji Damas yabar bata mamaki,don mutumin yasan kan rashin tausayi da kuma rashin sanin darajar ɗan adam. Suna gama wayar ta kashe wayar baki ɗaya,don haryanzu bata dawo nutsuwarta ba,anya kuwa ta yiwa Bilal adalci arayuwa?mutumin da ya taimaketa ya tsamota daga ƙangin rayuwar da take ciki?amman shine duk ta manta wannan kyakkyawan halarcin,yana sonta so na haƙiƙa,ta haɗa masa ƙarya amman kuma bai nuna mata komai ba,koda afuska ne kuwa. saboda Tsananin sonta da ya ke. Wata zuciyar ta ce mata,haba jidda Yanzu akan ɗan wannan abinda ya yi miki ne har ki ke wani tunanin har wani halacci ya yi,Alhaji Damas daga haɗuwarku ta farko ya baki gida mau shegen kyau da kuma tsada.ya bata shi halak malak,sannan duk zuwan da zata yi da kuɗaɗe take zuwa dami guda,tuni account ɗinta ya zama popular saboda muguwar cikar da ya yi da kuɗaɗe,ko shi Bilal ɗin da yake wani ƙafafar ya taimaka mata tasan sarai Account ɗinsa babu rabin kuɗinta,koda aƙwai ma waɗannan ƴan gidan nasu ba bar masa shi zasuyi ba,saboda yadda ya ke taimakonsu sosai. **** "mero!mero!!mero!!! Salim ne ya taƙar ƙare yana ta ƙwala mata kira,da sauri ta fito daga cikin ɗakinta da radionta akunne wacce Hajiya kaka ta saka ta siyo mata,wai ita baza ta iya zama ita kaɗai ba,ita kuma Hajiya kaka da taya ɓera ɓarna ta siyo ɗin,don ita da mero yadda kasan remote da tv haka suke.ita Hajiya kaka tv ita kuma Mero remote,don sai yadda mero ta yi da kaka ha suke zamansu,don ita hajiya kaka aƙwaita da ɗaurewa jikokinta gaba. Tana zuwa ta tsaya tana kallonsa shima yana kallonta,ta wani ture baki gaba tare da turo ɗaurin ɗan ƙwalinta ma gaba na rashin kunya. Sai kuwa ta ce"haba Yaya Salim nifa shiri na keji kazo ka tsaida ni,yanzu gashi nan har sun wuce ni".ta faɗi hakan kamar xa tayi kuka. Kallon banza ya yi mata sannan ya ce"ah lallai mero rashin kunyarki ta ƙara bunƙasa sosai,yau satinki uku agidan nan amman kullum idan na dawo sai dai inje in siyo abinci?a matsayi na na mijinki? Me ki ke nufi da hakan?,ko kina nufin kullum sai na dawo da uwar gajiya ta sannan inje inyo miki take away ki buɗe wannan ƙaton tunbinki,ki cinye ke gaki uwarcin tsiya,take away ɗaya baya isarki saboda haɗamarki,amman idan wajen girkine sai ki maƙale hannu ki ƙwanta ke gaki uwar san jiki ko?to ki buɗe kunnuwanki sosai kiji,wallahi daga yau na daina siyo abinci,ga kayan abinci nan a store komai aƙwai ki duba abinda ki ke da buƙatar dafawa ki dafa amman wallahi ni na daina siyo wani abinci kinji ko?". Yana faɗar hakan har ya yi nisa sai yaji mero na ce wa"oho dai ai naga ni ban iya girkin ba?idan kace inje wani hito in ɗakko kayan girki ni ta ina na sansu ma?ni koko kawai na iya damawa,don shi kaɗai hansai ta koyamin,kuma ni wannan ƙaton abin girkin na madafa wallahi ni dai ban iya kunnasa ba,kawai wataran inje ya babbake ni". abin dariya abin takaici,wai bata iya girki ba?to a gaba zai sakata yana kallo idan bata iya girkin ba?wata shawara ce ta faɗo masa aransa don haka kawai ya fita daga gidan ba tare daya ƙara magana ba. *** "Lafiyarki khairat bakya zuwa skull,ɗazu wannan malamin naku ya kirani wai bakya zuwa,me yake faruwa ne agidan naku?" Kasa ce wa yaya Aliyu komai na yi,don bana son tona asirin halin da na ke ciki.... .✍🏿 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 [23/09, 16:23] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_* 📃LITTAFI NA 2 UMMU MAHER(MISS GREEN🍀) Wattpad user name Rabiatu333 Arewabooks rabiattu0444 Matso kiji👂🏻 Kada ki kasance mai yawan yiwa mijinki musu wallahi yin hakan yana dakushe ki a wajen mijinki don haka a kiyaye,ba da faƊa ko fushi miji ya ke saka ya soki ba,A'ah da rarrashi da kissa ake mallake miji. ------------------------- 53. . .54 . . ."haba khairat da ke fa nake magana kinyi shiru?".Yaya Aliyu ya faɗi hakan cikin fushi don shima baya son rainin hankali. "Yaya Aliyu ka yiwa Yaya Bilal ɗin magana,wallahi ni nayi masa magana amman bai ce komai ba,idan ka yi masa magaba kai zai yadda".na faɗi hakan cikin shaƙewar murya,ya fuskanci tsoron Yaya Bilal ɗin na ke don haka ya ce"ok ba komai insha Allah zan yi masa magana,kada ki damu".yana faɗar hakan ya kashe wayar ya kira yaya Bilal awaya ya faɗa masa.taɓe baki ya yi ya ce"go a head kawai ni ban hana ta zuwa skull ɗinta ba,amman ka shaida mata kada ta kuskura idan taje ta kai dare ko kuma yamma,idan kuma ta taka doka ta to tabbas zan soke makarantar".ya faɗi hakan cikin gadara. Yaya Aliyu yasan halin Bilal sosai ɗan zafin kai ne,bai da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87