Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,260 words 0 views Progress saved
Download Book

ce wow so delicious bari inci daman tun jiya banci komai ba duk abinda naci dawowa ya ke".duk zubar da take ance mata ƙala ba sai sannu dana ce mata don ni na tsani mace ƙazama duk sai najo ta fice min araina,to da ta ke ce wa ba tada lafiya ta kasa aiki ita me aikin me ye amfanin ta da baza ta iya yi ba sai wani goge farlo saboda wato shi mutane zaso gani. buɗe cikinta ta yi sosai taci abinci kamat wata sabuwar mahaukaciya tasha lemon sosai tana gamawa ta ce"kai Khairat kin samu ladana wallahi rabon da naci abinci haka har na manta wallahi".ni dai bance komai ba ko da ta tashi daga baccin ko brush bata yi ba ina kallonta amman wai tazo har ta iya cin abinci gaskiya Yaya Aliyu yana ƙoƙari. *** "Umma wallahi Alhaji Damas ya tsaya sosai akan wai sai mun sayar masa da gidannan,kin san wannan mutumin yana da hatsari sosai wallahi,shiyasa muke binsa a hankali". Hajiya kaka ta kalli Abdul malik sannan ta ce"kai ni fa aduniyar nan ina ganin ikon Allah ace mutum ya dinga tsoron mutum?a i'na aka taɓa haka?ashe duk zafin zuciyarka na banza ne?shi dan ubansa ya isa ya karɓi gidan ya siya to wallahi kuce masa inji uwarku ƴar ƙasar uman bai isa yazo ya ce zai wani amshi gida awaje na ba,da a uman ne da banu shakka sai an garƙame shege,ɗan arnan kan dutse kawai". *GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE* 1, *MU GANI A ƘASA..🔥* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨* _Miss Hajo_ Guda ɗaya N300 Guda biyu N500 Guda uku N600 Guda huɗu N700 Guda biyar 1k *ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇* Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 StanbicIBTC Bank. Shaidar biya tanan 👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 ...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎.... *ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇 +227 84 50 64 76 *MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO* [23/09, 16:17] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI🥚* MALLAKAR *ummu maher(miss green)*🍀🍏 masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi. *Sirrinmu* yawan bin ƙwaƙƙwafin miji ma'ana yi masa bincike a ma'ajiyarsa ko a wayarsa yana saka kullum a zauna zargi kuma kunsan aure da zargi haramunne don haka don Allah mata mu kiya ye. 21🟪22 .. . . . .a ƙofar ɗaki na tsaya na bashi jakar na wuce don shiryo masa abinci,ko da ya shiga ɗakin ya hangeta cen nesa da gado tana ta sharɓar baccinta abinta harda yawun bacci,san baiyi mamakin ganin gidan fes ba saboda yadan khairat tana nan,yana shigowa yaji gidan ko ina sai tashin ƙamshi ya ke,tunda sukayi aure da khadija zai iya ce wa bai taɓa ganinta dai-dai da rana ɗaya ta ɗauki tsintsiya ta yi shara ba,kulli yaumin bacci,babu abinda ta iya sai bacci kamar kasa musamman ma da ta samu ciki duk sai abin ya ƙara jagulewa,filon ya fara ɗan bugawa a hankali ta buɗe idanuwanta ta yi miƙa ta buɗe hammatarta gashin nan ya cunkushe sosai ya kauda kansa yana jin rashin daɗi har cikin zuciyarsa ya ce"ke wai me yasa ko da yaushe babu abinda ki ka iya sai baccine?kuma ga ƙazanta ko da khairat tazo ai ba yana nufin ki sakar mata aikin komai bane?musamman yanzu da ki ke da ciki,ai ba'a son yawan ƙwanciya ko ka jibge waje ɗaya kama ta ya yi ace ki dinga ɗan exercise saboda kema zaki fi jin daɗi amman sai ki jibge ki yi ta bacci kamar kasa". yana gama faɗar hakan ya fita ta kallesa ta baya ta ɗan hararesa ta ce"to ai ya dawo kuma yanxu babu zaman lafiya,wato don ƙanwarsa tana aiki kada ta yi?to wallahi ina ganinta bazanyi aikin komai ba,ƴaƴan ne tsafta duk ta lalatu da wani tsafta-tsafta a damu mutum kawai".tana faɗar hakan ta tashi ta fito waje da kayan jikinta tun na bacci mai makon ta shiga banɗaki ta tsala wanka ta saka kaya masu ƙyau ko babu komai ko don mijinta ya gani yaji daɗi. ina cikin jera abinci ta fito na kalleta ta gefe na gaisheta,ta amsa tana wani ya mutsa fuska azuciyata na ce"oh Allah ya haɗa yaya da gamonsa mace har mace amman babu tsatfa yadda kasan bola haka ta mayar da kanta,su asalin babarsu ma buzuwa ce,agidanmu ana saka ƴan ɗakinsu a jerin masu ƙyau fari da kyakkyawar halitta amman fa sai dai ƙazanta ce za ta yi maka sallama dasu suna dai ƴammata idan zasu fita idan suka ɗauki ado sai ka rantse ba ƙazai bane amman fa ƙazanta na nan cunkushe jikinsu. Abincinta ta Zuba ita kaɗai tana ya mutsa fuska ta fara ci,yaya Aliyu ya kalleta ya ce"yanzu don Allah khadija ke bakiji kunyat kanki da kanki ba?yanzu fa ki ka tashi daga bacci ko alwala bakiyi ba bare brush sannan har kizo ki fara cin abinci a ture ma ta bani haƙƙina don bakisan haƙƙina da ke kanki ba sam". ture abincin ta yi gefe tana tura baki ta ce"gaskiya honey kana takuramin wallahi?daga dawowarka ai ka bari ka huta ma?amman ka balbaleni da faɗa agaban ƙwanwarka salon ta rainani ko"?. "raini kuma na nawa khadija?ai wallahi sai dai idan mutum bai san halinki,amman babu komai ki cigaba da wulaƙanta ibada wataran kema sai ta wulaƙanta ki".yana faɗar hakan ya fara cin abincinsa hankalinsa ƙwance,a zuciyata na ce Allah sarki yaya aƙwai haƙuri muddin kaga ya yi magana to abu ya ƙure ne musamman akan ibada,ko sanda kafin ya yi aure ba ƙaramin takura mana ya ke akan ibada ba,sai gashi Allah ya jarabcesa da mace mara ibada wacce sam hakan bai dame ta ba. ko ajikinta sai ma ƙara lomar abincinta da ta yi tana ta lodawa cikinta abinci wanda ya fito sosai ina tunanin ma ta kusa haihuwa,ana haka ya ce "ƙanwata kun gama waec da Neco ko?". "Eh yaya mun gama sai jiran sakamako a tayamu da addu'ah".ɗan murmushi ya yi sannan ya ce"to Allah ya baku sa'a ai nasan sister ɗina aƙwai ƙoƙari da bada himma insha Allah sai kin fito da good result".ya faɗi hakan yana murmushi. Na lura haushin hirar da muke yi Anty khadija ke yi don haka ni ko inda take ma ban kalla ba,muna gama cin abincin na ƙwashe kayan na kai kitchen na dawo na gyara wajen tsaf,ya janyo wani ɗan kit ƙarami ya ce"ƙanwata ga wannan tsarabarki ce daman Baba ya yi muku alƙawarin idan kun gama makaranta xai yi muku suprise so shine ni na riga sa".da murna ta na amsa ina yimai godiya. Anty Khadija ta ya mutsa fuska,na buɗe ƙwalin zaro idanuwa na yi ina kallon kan screen ɗin hamshaƙiyar wayar na zaro ta daga cikin ƙwalin aiphone ce mai masifar ƙyau sai sheƙi take.da tsalle na na rungume yaya ina godiya.sai kuwa naji anty khadija na ce wa"ah ah me ye kuma haka xaki wani rungumesa sai ka ce wata yarinya".ta faɗi hakan tana wani muzurai,da

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87