Chapter 43
Chapter 43
fara harararsa,ya matso inda take ya kalleta sannan ya ce"haba my jidda ki yi min uzuri don Allah". . . tun kafin ya ƙarasa ta ce"don Allah kada ka ƙarasa faɗar abinda ka yi niyya,idan banda rashin adalci shine ita kaje ka ɗaukota ni kuma ka barni ni kaɗai ko?wannan shine alƙawarin da ka ce za kayi min?". riƙe hannayenta ya yi wanda suka sha lalle ya ce"jidda kece matar da na keso,ta yaya ki ke tunanin rashin adalci daga wajena?ko kaɗan bazan taɓa haɗaki da wata mace ba,u are my one and only".ya faɗi hakan yana sumbatar goshinta,tuni ta washe bakinta don arayuwarta tana matuƙar son Bilal,amman idan ta tuno da wani abu sai taji duk ranta ya yi masifar ɓaci. Ina rungume ƙirjin Hajiya kaka sai rarrashina take,Rashida ta ce"hmm wallahi Hajiya kaka duk kinfi son khairat, ni fa har yanzu ko gida na ma bako sani ba".ta faɗi hakan cikin shagwaɓa. Sai kuwa Hajiya kaka ta ce"Allah sarki dukkanku ina sonku amman a gaskiya ita khairat ina tausayinta ne sosai,sam ita bata ƙwatar kanta kamar yadda ku keyi,haƙurinta ya yi yawa gaskiya,shiyasa na ke tausayinta balle yanzu kuma za ta zauna da wannan miskilin sai yadda hali ya yi.to wallahi daman ina faɗa miki duk abinda ya yi miki ki rama,kada ki zauna kina wani jin kunyarsa yasa miki hawan ruwa ya barki anan." Hajiya inna wadda zuwanta kenan ta ce"khairat ki ka biyewa Ramatu kaiki za tayi ta baro,don haka ki yiwa mijinki biyayya iya bakin iyawa,yi na yi bari na bari kinji". "To ai ni cewa na yi kada tayi masa biyayyar?Allah hajiya Inna ki dinga kyautata zato". "A'a to Ramatu tsakaninki da Allah banyi gaskiya ba?so ki ke ƙwana biyu a sako miki ita kome?,ah to adinga sara ana duban bakin gatari dai". Nan dai suka dinga yimin nasiha sannan suka tafi har su Rashida,har ta tafi sai kuma ta dawo ta rungumeni tana share hawaye ta faɗamin wani abu a kunne,dariya na yo itama ta yi sannan suka tafi suka barni da kewa ni kaɗai kamar mayya. Na ya ye mayafin fuskata ina kallon ɗakin,naji wani hawaye yana fita acikin idanuwa na..oh ko wata irin rayuwa zanyi a wannan gidan?mijin da baiso na?wani irin ƙalubale zan fuskanta?Allah kaɗai yasan abinda zan gani,na rintse idanuwa kuka yaci ƙarfina,ina tuno lokacin da na ke neman yafiyar mahaifina,ko kallona baiyi ba,ƙarshe ma ya tashi yabar wajen". . .✍🏿 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 [23/09, 16:21] Miss Green🍀: *_🪺ABIN CIKIN ƘWAI🪺_* 📃LITTAFI NA 2 UMMU MAHER(MISS GREEN🍀) Wattpad user name Rabiatu333 Arewabooks rabiattu0444 *addu'ar samun lfy ga ko wani irin ciwo* an rawaito daga Aisha (R.A),tace manzon Allah(S.A.W)ya kasance idan mara lfy yazo wurinsa da kokena rashin lfy ya kan ɗauka hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa sannan ya dangwali ƙasa sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo,sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka; "bismillahir turbati ardina biriqati ba'dina yashfa Taqimuna bi'izni rabbina". 47. . . .48 . . . .Nasha kuka na sosai kamar ma bazan daina ba,na tashi na shiga banɗaki Na ɗaura alwala sannan na shimfiƊa sallaya na tayar da sallah,na yi isha'i da kuma shafa'i da wuturi Na Ɗaga hannaye na sama ina kuka ina addu'ar Allah yasa yaya Bilal wataran yaso ni kamar yadda na kesonshi,Allah kuma yasa albarka acikin auranmu. na shafa addu'ar na tashi na Ƙwanta na Ɗaga idanuwa na sama ina tuno da wasu abubuwa,waƊanda suka wanzu arayuwata,gashi haryanxu ban samu sauƘinsu ba. Babu zancen zuwan ango,don tun ina yaudarar kaina wai ina tunanin zaizo har naji shiru babu shi babu labarinsa,na rintse idanuwa na hawaye yana fitowa. *** "Jidda ki faƊamin abinda ya faru da rayuwarki?Jidda ni fa ba yaro bane balle kice ko yau ne aka haifeni?nasan komai ayadda ya ke duk dani ba mazinaci bane amman ki sani shekaruna sun kai in san hakan,kada ki Ɓoye min komai,na yi miki alƘawarin indai ki ka faƊamin gaskiya,bazan taƁa zarginki ba". ya faƊi hakan yana kallon jidda wacce ta yo tsuru kamar munafuka,tana kallon yadda Bilal duk yana yinsa ya canja jijiyoyin kansa sunsha ta ruƊu-ruƊu. tana kakkarwar jiki dana baki ta ce"Bilal ka yi haƘuri haƘiƘa banyi maka adalci ba,dana Ɓoye maka komai na rayuwata,amman yau zan gaya maka gaskiyar lamari." Kasa cewa komai Bilal ya yi zuciyarsa na masa wani irin turiri,ta cigaba"Bilal wata rana baba na ya aikeni shago,naje na yo siyayyata na fito,wasu mutane waƊanda bansan su waye ba,suka Ɗauremin Idanuwa na suka sakani a mota sukayi gaba dani,tun daga ranar Bilal na rasa martaba ta na Ƴa mace,na rasa mutuntaka ta baki Ɗaya,Bilal bayan wannan lokacin nasha wuya sosai don har sai dana Ƙwanta agadon asibiti,an Ɗaukama ko ina da wata cuta ne,ashe babu komai wahalar da nasha awajensu ne."ta faƊi hakan tana shessheƘar kuka. sosai ta bawa Bilal tausayi,sai dai awani sashe na zuciyarsa sai ya kasa gasgata hakan,gani ya ke kamar ba haka bane?wani sashen na zuciyarsa kuma ya ke tunatae dashi ga barin zargi tsakaninsu don muddin zargi ya shiga to babu aure. samun kansa ya yi da rungume ta yana Ɗan bubbuga bayanta,har ta yi shiru,sannan ya Ɗaga Ƴar Ƙaramar haɓarta ya ce"jidda ke matata ce,ki daina saka komai aranki game da hakan,insha Allah na yi miki alƘawarin zama da ke da amana,kuma babu mai jin wannan sirrin namu".ya faƊi hakan yana Ɗaga mata gira ta yi masa wani mugun murmushi wanda ita kaƊai ce tasan manufar yin hakan. tun daga ranar komai ya koma dai-dai,sosai jidda ke jin daƊin Bilal,don yana nuna mata so da Ƙauna,tare da tarairayarta,abinda yafi yi mata daƊi bai wuce yadda Bilal ya watsar da matarsa ba,don haka sai ta Ƙara miƘe Ƙafafuwa,wai ita gata matar so. **** Rayuwa ta yi min zafi,komai ya tsayamin cak don iya wulaƘanci yaya Bilal ya yimin shi,yau ina Ƙwana huƊu agidansa,amman ko shinge na baizo Ba,ballan tana ma ya duba lafiyata,Ƴan gidanmu cak suka Ɗauke Ƙafarsu babu wanda ya leƘomin. waya ta dake ringing na Ɗauka Ƴar gidan mama ce Ƙanwar mahaifinmu me suna maryam,na Ɗauka naji muryarta kamar zata yi kuka ta ce"khairat yau dai gani nazo gidanku amman me gadi yaƘi ya barni in shigo,wai hajiya jidda bata bayar da oder in shigo ba,jiya ma baƘi da yawa sunxo amman wallahi ba'a basu damar shigowa ba,wai wannan wani irin abune haka ya ke faruwa".? jin na yi shiru yasa ta ce"a to nidai babu inda zani,don yanzu na kira hajiya kaka ta ce kada in sake in dawo sai na shiga,to nima Ɗin na yarda da maganar kaka don haka ki fito ayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87