Chapter 3
Chapter 3
ne mata ƴaƴan kaka goma maza,nan fa kaka ta shiga gaya musu wai tana ji lokacinda aka ce a ƙara volume tunda masifaffiya ta iso. *Miss green ce* [23/09, 16:15] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_ 📃Littafi na 1 By🪶 *Ummu maher(Miss green)🍏* *GAWURTATTU 5* ----------------------- *wattpad user name* https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333 --------------- *Arewa book user* https://arewabooks.com/u/rabiattu0444 -------------------- *Sirrinmu* manzon Allah (s.A.W) ya hanemu da gujewa mazajenmu a shimfiɗa yin hakan babban laifi ne kuma tsinuwar mala'iku za ta tabbata akanki. -------------------------------- 3🟪4 .. .Dukansu suka haɗa baki wajen ce wa "umma lafiya me ya faru?".kukan ta ƙara fasawa tana ce wa"yanzu har lokacin wulaƙanta ni agidannan ya yi?gaskiya zan bar muku gidannan ku zauna ku da matanku tunda haka kuka zaɓa". dukansu shiru suka yi sai malik ne ya ce"Umma ki faɗa mana abinda ya faru,don mun shiga cikin duhu wallahi". "To matarka ce inya mura ita ce ta ɓata min rai,wai ga masifaffiya nan ta iso,don ubanta gidan inyamurai ne nan da za ta tara mana ƴan bariki suna muskuta ɗuwaiwaka kamar gidan maguxawa?to wallahi ni nagaji xan barmuku gidanku".sai ta fashe da kuka sosai har da majina,Hajiya Iklima ta ce"kaka don Allah ki yi haƙuri ki daina kuka"sai kuwa kaka ta Juyo a fusace ta ce"indai na kuka ko?tunda ba uwarki ce taka kukan ba ai dole ki ce haka?ni tashi ma shi ki barni in yi magana da ƴaƴana bana son bare awajen. wani malulun baƙin ciki ne ya cika zuciyar Hajiya iklima ta Kalli fuskar hajiya kaka ta harareta,ita ta rasa wacce irin mata ce ba ta ɗaukar zuga ko kaɗan,amman ta yi alƙawarin muddin tana raye sai ta haɗa Hajiya kaka da dukkanin surukanta ta zama ita ce ta gaban goshi. Tashi ta yi ta fita tana mai ƙara jin haushin cin fuskar da Hajiya kaka ta yi mata,sai kuwa kaka ta ce"to as dai a fita don bana son ina shawara da ƴaƴa na a zo asakamin idanu irin na fulanin daji". wannan magana da kaka ta faɗa ba ƙaramin mugun haushi ya bawa Hajiya iklima ba,don tasan sarai da ita take don asalinta fulanin daji ce,don itama kafin ta bari a aurota ba ƙaramin gwagwarmaya aka sha ba. "Umma insha Allsh daga yau Zulaihat ba xa ta ƙara yi miki wani abu da zai ɓata miki rai ba,yanzu ma ba sai anjima ba za ta baki haƙuri",yana faɗar hakan ya yi saurin fita. Usman autan Hajiya kaka ya ce"gaskiya umma ki daina yi wa wannan baiwar Allahm haka,gaskiya ba a ƙyauta mata wallahi saboda ita ba yaranmu ba ce sai kuma ace za abi a tsaneta". "ah lallai ƙanin Zulai ka ce kaima an jiƙa an baka,kamar yadda sukayi wa ɗan uwanka a da cen baya,yanzu kuwa Allah ya dawo min da hankalin ɗana jikinsa,yanzu muna nan da kai za kaga caccakar da zai yi musu shegu masu cin arziƙi,tunda suka zo ina kula dasu babu abinda suke sai dafa nama daga an sauke wancen a ɗora wannan,ɗana yana ta kawowa suna cinyewa". dukkansu shiru sukayi har Alhaji Aliyu wato babban ɗan ta don shima ba'a bar matarsa ba,don haka haƙuri kawai ya iya bawa Hajiya kaka yaja bakinsa ya yi shiru. A ɗakinsa ta samesa yana kaiwa yana kawowa hannayensa ya rungumesu a baya,sallama ta yi ta samu waje ta zauna kanta a ƙasa sai ta ji ya ce cikin zafi"Yanzu Xulaihat abinda ki ka yi wa mahaifiyata ya yi miki daɗi kenan? ki tara ƴan uwanki suna zagar min mahaifiya ta to wallahi ba zan lamunta ba,kowa ya haɗa kayansa ya barmin gidana don ba zan lamunci cin fuskar kowaccenku akan mahaifiyata ba. Muryarta na rawa zata yi magana da sauri ya ɗaga mata hannu ran tsohon soja ya tashi ya fita yabar mata ɗakin,ya koma wajen mahaifiyarsa ya cigaba da lallaɓa ta,don yana fatan ya gama da ita lafiya. Kuka sosai ta yi awajen kafin ta tashi ta fita,tana tunanin ta yadda za ta gayawa ƴan uwanta wannan maganar garinsu da sai a yini a kusan ƙwana ana tafiya sannan sai da yamma ta yi sannan za a ce su koma da yamman nan ko kai amarya ba ayi ba sunga gida. Ɗaki ta koma tasha kukanta sosai,a hankali na buɗe ƙofar ɗakin mahaifiyata halin dana ganta a ciku shine ya ƙara jagula min tuna nina,na ƙarasa kusa da ita hankalina atashe ganin fuskarta ta jiƙe sosai da hawaye cikin daburce wa na ce"Mama lafiya me ya faru da ke?" Bata iya ce wa komai ba ta tashi ta fita,binta na yi da kallo ina hasashen abinda ya faru tabbas hajiya kaka ce ba wani ba,don tun ina ƙarama na sha kama mama tana kuka kuma ba kowa ne musababin kukanba sai hajiya kaka,sam bata san mama na ban san abinda ta yi mata ta tsaneta haka ba.nima bani da zaɓi daya wuce in fito daga ɗakin don haka na yo waje don ƙawayenmu duk sunci ƙwalliya don kai amarya,ina fitowa Rashida ta ce"lafiya naga fuskar mama duk ta canza?ko ke ce kika yi mata wani abin". "hmm Rashida ni kuwa me zanyi wa mama da za ta yi fushi dani haka?kawai dai kin san tsakaninta da hajiya kaka ina ganin wannan ne amman ba ni ba ce." "kin san Allah Khairat matar nab gaba ki ɗaya ta ishemu a gidannan,ni na rasa dalilin daya sa duk iyayenmu suke cikin gidannan kamar dole,ita kuma ba bari take a zauna lafiya ba,kullum sai faɗa ni wallahi matar nan ma na matsu ta margaya mu huta da jarabarta. Saurin rufe mata baki na yi na ce"wallahi Rashida ki kiyayi wannan bakin na ki kinsan dai matar nan kakarmu ce,babu yadda zamuyi da ita suma iyayenmu haƙuri suke da ita,muma ya kamata muyi haƙurin ko?" Iman da Salimat da suke juyo hirar da su Khairat suke sai kuwa suka ce"Hmm Rashida wallahi ki cigaba da maganarki kada ki biyewa wannan wacce bata san inda ya ke mata feeling ba,don haka ko muma wallahi mun tsaneta wallahi tunda bata san iyayenmu mu ma dole ne mu tsaneta". ni dai fitowa na yi babban hall ɗin da ake hidimar bikin abin mamaki duk babu ƴan uwan mama na awajen abin ya ɗaure min kai sosai,yanzu fa na gansu awajen amman har na nemesu ban gansu ba. Aranar dangin mama na duka suka koma ba tare da sun tsaya sai washe garin ba,hankalina ya tashi sosai na fito na yi sashen hajiya kaka,tana zaune ita da wata ƙawarta Hajiya Inna,na gaisheta tana tsokana ta tana ce wa saura na mu muma,kunya ce ta rufeni sai kuwa na ji Hajiya kaka na ce wa"Hmm Hajiya Inna kema dai kya faɗa wallahi wataran idan na ga yaran nan suna shiga suna fice agidannan su kusan ashirin duk ƴan mata,sai in shiga ɗaki inyi ta kuka sai ta buɗe injirnta ta ce"kinga duk inda na yi ƙashin wuya saboda yarannan duk dun tsotseni wallahi". duk da ina cikin tashin hankali sai da na yi dariya sannan na ce"Hajiya kaka kina da masaniyar dangin mamana duk sun bar gidannan acikin wannan daren ko kai amaryar basu yi ba sunga gidan brother". "brozo na ce ungo ƴar nema. to sai me don sun bar gidan ai ni sauƙina ne don wallahi idan na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87