Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,278 words 0 views Progress saved
Download Book

amman sai dai me?tun kafin ta sauke hannunta itama meron ta rama jika ke tas tas maruka har biyu. Da sauri na riƘe hannun mero ina janta gefe sai kuwa mero ta ce"anty wallahi ki daina ja na don wallahi yau sai na fasawa wannan farar kamar Ƙwai baki". da Ƙer naja ta gefe tana Ta faman kumfar baki. ranar sosai aka yi rigima agidan momi iklima ta dage wai sai ta ramawa nadiya mari hajiya kaka ta ce taje idan ta isa ta dake ta,ai kuwa ta shige Ɗaki ba tare da ta Ƙara magana ba,don tasan halin hajiya kaka kaƊan daga aikinta ta ciwa mutum mutumci,musamman idan ta rufe waƊannan fici-ficin idanuwanta,sai ta wanke mutum tsaf. Sosai muke shirin yin sauka ni da rashida muke abinmu su nadiya ma nasu suke,don yanzu tsakanin rashida da nadiya abin ya Ɓaci,don ita nadiya kallon kishiya takewa rashida,ita kuwa rashidar ko kallon inuwar Nadiyar bata yi,don ta ce rashida bata isa ta yi kishi da ita ba,don bata kai wannan matsayin ba. sosai hajiya kaka ke ihu duk hankalinmu ya tashi,sai dai me!?muna zuwa muka tarar da ita ta saka kuƊinta agaba wanda suka kekkece kamar an Ɗakkosu a bakin kura. mamaki sosai kowa ya ke ga kuƊi da yawa amman kaƊanne ba'a keta su ba. Nice na yi Ƙarfin halin zuwa wajenta na ce"hajiya kaka me ya faru da kuƊinki haka?". Kukan ta cigaba da yi sannan ta ce"khairat ranar da kiga ina Ƙirga kuƊinnan?" sai kuwa na Ɗaga kai alamar na gane,ta ce"to tsautsayi ina Ɗakkosu A ƙarƙashin gado shine naga duk Ɓeraye sun cinye min". kowa guntse dariyarsa ya yi,sai kuwa mero ta ce"ah kiji min tsohuwa da wayo?yanzu ai gashinan kinyi biyu babu".? madoki hajiya kaka ta Ɗakko tana ce wa wallahi sai in dake ki in daki kuƊina wallahi". Da gudu ta yi gefe ta cigaba da dariyarta. yaya mukhatar wanda shigowarsa kenan ya ce"to yanzi kinga sai aje asaka kuƊin abola ko?". da sauri ta juyo ta ce"to ai ba haƊejawa ne suka bani kuƊin ba?Da dangin uwarkane suka bani yau da nasan sai sun garƘameni". Jan bakinsa ya yi kawai ya yi shiru,Ƙarshe dai yaya mk da yaya Aliyu sunyi mata alƘawarin biyanta kuƊinta wanda ta ce dubu sittin ne,don muddin basu biya taba aƘwai matsala. anan aka Ƙirga dubu shabiyar waɗanda su babu abinda ya shafesu,hajiya kaka sai tsinewa Ɓeraye take tana kuka. Su nadiya sai dariya suke don daman haushinta suke ji. ina fitowa daga sashen hajiya kaka yaya mk ya biyoni,yana kiran sunana haushi da kuma nadamar haƊuwa dashi suka saka baki Ɗaya na kasa koda kallonsa,shi kuma gani ya ke kamar kunyarsa na ke,amman fa azuciyata tsanarsa ce fal araina. da sauri na tsaya awani lungu wanda ya raba sashenmu dana baba Ƙasim,saboda san bana son kowa ya ganmu. hira sosai ya ke min ni kuwa Allah2 na ke ya Ƙeleni in tafi don ni Ƙwana biyu da ya yi tafiya har wani daƊi ne ya keji wai don ma bai san ina da waya ba,da na shiga uku da waya. kuƊi sosai ya bani wai inyi shagalin sauka ta dashi naƘi amsa amman duk da haka sai da ya takuramin na amsa,har na shiga Ɓangarenmu bai daina kallona ba,yadda kasan zai biyo ni,har tausayi ya fara Ɗan bani don mai sonka ka soshi ko yaya ne. mama na nunawa kuƊin,ta kalleni sannan ta ce"khairat wai ni mukhatar aƘwai wani abu da ke tsakaninku dashi ne?". kai na a sunkuye na ce"mama wai ce wa ya yi yana sona".da sauri mama wai mama sona ya ke mama". "khairat kinfi kowa sanin ce wa bara'atu fa ya ke so,tun kafin a gane kuna tare dashi ki rabu dashi don gaskiya ni bana son tashin hankali". GyaƊa kai kawai na yi don nima daƊin hakan na keso,don ni zuciyar nan tawa A.D,Ne kawai acikinta ma'ana yaya Bilal. **** sosai filin saukar ya cika ana sauraran Ƙira'ah mai masifar daƊi daga bakin jikar hajiya kaka ABIN CIKIN ƘWAI,wato khairat da yawan mutane hankalinsu na kan khairat yawancin mazan wajen kuma ce wa suke dama khairat ta zama matarsu don yarinyar Allah ya yi mata baiwa sosai,khairat dai ba wata mai Ƙyau ba ce,tana dai da baiwa sosai diri tana da shape wanda ake ce wa coca cola shape ga wani dimfil wanda ya Ƙawata doguwar fuskarta,kuma ita dai ba fara bace kamar sauran Ƴan gidansu,amman tana da baiwa ta ilimi na arabi da boko. abin mamaki da aka kira jidda wata Ƴar ajinmu da Ƙer ta kai karatun saukar na ta,amman wai sai mukaji ana sanarwar wai wani wanda ake kira da ADMIRAL BILAL ABDULLAHI,wanda aka fi sani da A.D ya bata Ƙyautar mota. Sosai kowa ya yi mamakin jin hakan duba da irin yadda karatuna ya Ɗauki hankalin mutane da dama,kuma nima na samu Ƙyautuka sosai ciki har da Ƙyautar wata hamshaƘiyar computer wanda Ɗan majalisa ya bani,sannan na samu Ƙyauta ta dubu Ɗari biyu daga hannun wani mai kuƊi. har muka dawo gida zuciyata tana wajen Ƙyautar da yaya Bilal ya bawa jidda Ƴar ajinmu. To me ye tsakanin jidda da yaya Bilal?babu mai bani amsar hakan,don haka na zubawa sarautar Allah ido ammab zuciyata sai kai kawo take,saboda tunanin abunda ya shige min duhu. satin bikinsu Rashida ya kama,sosai ƘwaƘwalwata ta yi busy duk hankalina kacokan yana kan bukin,ni da maryam ne manyan Ƙawayen amarya don haka tare muke komai. Wata rana ranar da bazan taƁa mantawa da ita ba,ita ce rabar dinner Ɗinsu rashida,yaya Bilal naga ni da jidda ya sama mata kujera ta zauna tasha anko irin namu sak,onion color ne material Ɗin sai mukayi pitet gown amman ita jidda riga da siket ta saka wanda sukayi masifar yi mata Ƙyau. Sosai jikina ya ke rawa hankalina idan ya yi dubu to ya Ɓaci,wasu zafafan hawaye masu zafi suka zubomin,na fito daga wajen baki Ɗaya,na samu wani wajen flower's kuraye shar,na tsugunna na fara wani irin kuka mai tsanani,ina jan doguwar rigar dana saka kamar ita ce ta yi min laifin. Dafa kafaƊa ta naji anyi,maryam ta bayyana agaba na,ta Ɗago haƁa ta cikin tausayi sannan ta ce"ki yi haƘuri khairat naga duk abinda ki ka gani,amman ina son ki daurewa zuciyarki ki yi haƘuri don Allah a Ƙarasa bikin dinner Ɗinnan kada kowa ya gane abinda ke faruwa,shi so haka ya ke yana da zafi musamman idan wanda ka keso baya sonka,to tabbas zaka shiga wani hali,nasan abinda ki keji tunda nima na taƁa shiga irin wannan halin." ta damƘe hannuwa na sannan ta ce"khairat ina tare da ke ako ina insha Allah sai kin auri yaya Bilal,ni Ɗinnan zan tsaya miki insha Allah",Ta kalleni tana saukemin idanu itama duk hankalinta atashe amman kuma tana dauriyar dannewa saboda ni. Nan dai ta cigaba da rarrashi na ta bani hoda na Ɗan shafa saboda kada a gane kukan dana yi. yaya salim yana zuma akan kujera,mero wacce take ta faman zuba ita da wata Ƴar Ƙyauye irinta,ga kuma wani lemo a hannunta tana ta faman zuƘa kamar za ta shanye har da bottle Ɗin. Tsi ta zubawa yaya salim a jikinsa duk ta Ɓata mishi kayansa,da sauri ya tashi alokacin yana waya da budurwarsa mai suna salimat yana

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87