Chapter 42
Chapter 42
bikinda Hajiya kaka ta taɓa kashe kuɗi irin bikina,ta kashe kuɗi ba na wasa ba,har tausayi ta bani. Ana cikin wannan kiɗanne na zagaye a hankali na fita na koma ɗakin Hajiya kaka na dinga cin kukana idanuwa na sukayi jawur kamar gauta. A hankali mama ta ƙaraso inda na ke,ta ɗago fuskata sosai ta sharemin hawaye na sannan ta ce"khairat aƙwai abubuwa da yawa da ya kamata in faɗa miki amatsayi na,na mahaifiyarki duk wata uwa tagari tana yi wa ƴarta da nasiha da tabi mijinta,ta yi masa biyayya,yi na yi bari na bari sannan aƙwai wasu abubuwan da ya kamata in faɗa miki na farko shine,kada ki sake mijinki yaji wari ko wani bashi ajikinki,ki kasance mai tsarkake jikinki ki zamo kullum cikin tsafta,yin hakan zai ƙara kusanta ki da mijinki sannan tsafta na ɗaya daga cikin ginshiƙin aure,matuƙar mace ƙazama ce to za kiga babu inda auren ya ke kaiwa,kullum cikin faɗace2 da kai ƙara,abu na biyu kuma shine ki kasance mai kula masa da dukiyarsa wala yana nan wala baya nan,ke dai ki zamo mai saka idanu akan kula da dukiyarsa,sannan ki rintse idaniyarki akan kuɗinsa,duk yawan kuɗin da zai ajje kada ki ɗaukar masa,khairat nasan halinki nasan baki taɓa yin hakan ba amman ki kiyaye hakan.ladabi da kuma biyayya indai ya baki umarni ko menene ki yi,indai har bai take addini ba to ina mai jan hankalinki ki yi sa,iya girki nasan ke gwana ce akan hakan amman yanzu tunda miji zaki yiwa to tabbas ya kamata ki ƙara ƙwazo sosai ta yadda zaki yi fice aduniyar girki. Khairat idan har na ce zan zaunar dake inyi ta yi miki magana akan aure to tabbas zamu ƙwana ban gama ba,sai dai ince Allah ubangiji ya baku xaman lafiya me ɗorewa. Tana faɗar hakan ta rungume ni tana kuka sosai,nima kukan na ke a haka Rashida ta shigo ta samemu,itama ta taya mu kukan,babu mai rarrashin wani. Mama ta ce"khairat wannan envelope da kika bani wanda wannan bawan Allahn ya baki,jiya na buɗesa naga kuɗi ne aciki har dubu ɗari,to shine na wuce kasuwa na siyo miki wasu abubuwan,banso na yi amfani dashi ba amman Aliyu ya tabbatar min da mutumin arziƙine,sannan yau daya zo ɗaurin aure ya baki ƙyautar mota guda,amman mahaifinki ce wa yayi ba za'a amsa ba,amayar masa amman motar tana gidan Aliyu,za'a siyar a siya miki wani abin mai amfani." Na yi mamakin Ahmad sosai kamar bai san daɗin kuɗi ba?irin wannan zubar da kuɗi haka?nan dai mama ta sakani agaba na shiga banɗaki ta zubamin wani abu mai ƙamshi acikin ruwan,na shiga na yi wanka ƙamshi duk ya baɗe ɗakin,ina fitowa ta bani wata zuma mai kauri tace insha,babu musu na ɗaga kaina nasha,sannan ta bani wasu abubuwan ta koyamin yadda zanyi amfani dasu koda bayan aure idan ina da buƙata. Yadda ake haɗa zumar mata. *Zuma* *citta* *kanunfari* *minanas* *Riɗi* *sassaƙen ɓaure* *sassaƙen gamji* *ƙwaƙwa* Ki samu zumarki mai ƙyau,sai ki samu sassaƙen ɓaure amman bayan kin dakashi ya yi luƙui kin tankaɗeshi,sai ki ɗora zumar akan wuta kiɗan ƙara ruwa kaɗan,sai ki zuba garin minanas da kuma garin ɓauren da kika daka,sai gamji shima kamar garin ɓaure,chokali biyu biyu zaji zuba,ya danganta da yawan zumarki don ba'a son ya cika kauri da yawa,sai ki zuba garin citta,da kuma garin kanumfari,sai kiɗan soya ƙwaƙwa daban daman kun riga da kin soyata ƙananu sai ki zuba aciki,riɗinki ma ki zuba bayan kin wankeshi kin busar dashi sosai.sai ki rage wuta kina juyawa kaɗan kaɗan,shi wannan haɗin ba'a son ki cika masa wuta. Za kiji yana ƙamshi to alamar ya yi kenan,sai ki sauke ki samu ƙwalbarki mai ƙyau ki zuba aciki,ki dinga shan chokali 2 da safe biyu da yamma. Hmm ni dai bazance komai ba,sai an gwada akan san na ƙwarai. ***** "Ai Bilal ba sai ka nunamin ce wa baka son yarinyar nan ba?ƙarfe nawa yanzu?ɗaga kanka ka duba agogo?".a hankali ya ɗaga kansa ya duba agogon ƙarfe 10 na dare,ya sauke kansa sannan ya ce"kai Hajiya kaka gaskiya kina takuramin wallahi,yanzu me ki ke son inyi miki?". sheƙeƙe ta kallesa sannan ta ce"ungo Ruƙayya zaka yi min"?.ta faɗi hakan tana harararshi,ga dai mata nan ka bari agidanku ka ƙi ka kawo motocin da za'a kaita gidanka,mero wacce zata zauna agidannan tun biyar akazo aka ɗauketa,amman kai shine zaka gaya min maganar banza ko"?. "Haba grany!ba fa ita kaɗai ce matata ba,ga Jidda nan,amman ita babu wanda ya damu,sai ita ƴar gwal,kuma ni zanje in ɗauko jidda da kaina,ita kuma xan aiko azo a ɗauketa,shikkenan?". Ya faɗi hakan yana ɗagawa Hajiya kaka gira,ta ce"ai wallahi kuwa baka isa ba Bilal,wato ma har ka ke cemin ita wannan figigiyar matar taka kai za kaje ka ɗakkota,ita kuma wannan za'ka aiko a ɗauketa ko?to ban yarda ba,sai dai ita ka tura a ɗakkota wallahi,kuma ni zan kaita har ɗakinta". Ta faɗi hakan tana shiga ɓangarenta,daman mama ta sakani na canja kayana,wata haɗaɗɗiyar lifaya mai ƙyau,fara ƙal da ratsin kore na yafa ta har kaina na rufe ruf,hajiya kaka ta janyo hannuna mama tana ta rarrashina,muka fito waje. Yana tsaye inda kaka ta barsa,ya hangota ya juya kai abinsa,azuciyarsa yana ce wa yarinyar da aka haifeta agabana na raineta sannan yanzu acw wai ita ce matata?wannan ma ai janyowa mutum raini ne.ya shiga cikin motar ya tayar da ita abaya muka zauna nida hajiya kaka,sai ƴar uwar mamana guda ɗaya. Karatun qur'anine ke tashi acikin motar,ga ƙamshin freshner ya cika motar mai sanyin daɗi,har mukaje kuka na ke,duk haushi ya cika sa a fili ya ce"wannan ai dole mutum yasha pain reliep".Hajiya kaka na jinsa ta hararesa ta baya. Abakin kyakkyawan ɓangare na aka saukeni,ɓangare uku ne agidan,ɗaya nawa,ɗaya na jidda ɗaya na me gidan,ɓangare na ya yi kyau sosai,ko sisin mahaifina babu aciki Baba Abdullahi shi ya yi rawa ya yi tsaki,kayan da aka sakamin ko su Rashida dasu ke matsayin ƴaƴansa bai yi musu shi ba.har kayan kitchen bawan Allahn nan shine ya yi,ya bawa ƙannansa su Aisha suka siyo masu matuƙar kyau. Koda zamu shiga sashen nawa hajiya kaka ta ce"ki yi bismillah kafin ki shiga Allah ya kareki daga sharrin duk wani mai sharri". Da ƙafar dama na shiga gabana yana dukan uku uku,shikkenan ta faru ta ƙare yau dai Allah ya kawoni gidan da za'a gasa ni kamar yadda na nema,jikina duk ya yi sanyi sosai. Sai asannan aka dinga kawo mutane aka cika gida ɓam,Jidda kuwa ta cika ta yi ɓam,don ta kirasa amman bai gani ba wayarsa na silent,sai sannan ya duba ya gani,tuni jidda tafi awa agidan,don Babanta ya ce akawo ta tunda masu ɗaukarta basu zo ba,a sabuwar motar Jidda ɗin aka kawota,sabuwa dal sai sheƙi take. Shigowar saƙo wayarsa ne yasa ya duba alokacin yana shirin zuwa ya ɗauko jidda,da sauri ya kalli sashen jidda ɗin sannan ya kalli wajen motocin gidan,sosai abin ya basa mamaki me yasa bata jira yazo da kansa ya ɗauketa ba,wani kishi ya tokare masa ƙirjinsa,yanzu haka wasu mazan duk sun kalle masa matarsa. Kai tsaye sai da ya fara shiga sashensa ya ajje wasu abubuwan sannan ya shiga wajen jiddarsa,yana shiga ɗakin na ta ya hangota kan gadonta babu ko lulluɓin idanuwanta sun kumbura saboda kuka,ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87