Skip to content

Chapter 83

Chapter 83

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,290 words 0 views Progress saved
Download Book

buƘatar ki samu kulawa sosai don haka kada ki Ɗaga hankalinki don Allah ciwon fa yanzu da sauƘi". da sauri na miƘe na ce"haba anty halisa ni fa ba yarinya bace kamar da,kowa fa ya shigo fuskarsa babu daƊi,ni nasan aƘwai abinda ake Ɓoyemin."Na faƊi hakan cikin kuka na tashi tsaye ina jin wani irin jiri yana Ɗiba ta,ga uwar yunwa da na keji wacce ta gama cika min ciki na ce"anty halisa don Allah zo muje ki nunamin Ɗakin da aka Ƙwantar dashi"?. da sauri ta ce"a'ah fa khairat bazan iya rakaki ba gaskiya,kinga ba kida lafiya kuma bayan haka mijinki ma fa yana cen yanzu na baro sa acen,kinga ai babu daƊi ki dai bari ki samu lafiya sai kije".da sauri na Ƙarasa kusa da ita ina kuka na ce"don Allah anty halisa ki rakani in duba sa,zuciyata ji na ke tamkar zata fito don Allah". sosai take kallona cikin mamaki,wato khairat micijin sari ka noƘe ce,wato duk tsanar da take ce wa ta yiwa yaya Bilal ashe duk Ƙarya ne?to idan ba Ƙarya ba me yasa ta damu don ba shida lafiya?. ganin khairat Ɗin ta dage ne yasa ta ce"to khairat muje".ta Ɗakko min jaririyar muka fito,ina dafe bango ina tafiya jirin yana Ɗiba na amman a haka har muka isa Ɗakin,duk naji jikina ya Ƙara yin sanyi sosai. da mutane sosai a Ɗakin duk suka zubomin ido mamaki Ƙwance kan fuskarsu har da shahid a Ɗakin,da ammi mahaifiyarsa da kuma mama har dasu yaya Aliyu,ga hajiya kaka a gefe su Rashida,sai maryam wacce bata fi wata biyu da haihuwa ba,ta haifi Ɗanta na miji,me sunan yaya Bilal. saurin dafe jikin bango na yi ina waro ido waje,ganin yaya Bilal Ƙwance kamar matacce an saka mishi abin shan numfashi ya yi wani irin fari fauu ga kuma ramar da ya yi,an saka masa kaya ruwan skye blue irin na marasa lafiya. wani irin kuka na fashe dashi tuni na tsugunna Ƙasa da rarrafe na Ƙarasa bakin gadon,saboda Ƙafufuwa baza su iya kaini wajensa ba,na ce"Yaya Bilal anya kuwa kai ne?me ya faru da kai?wani irin ciwo ne wannan?".duk ni kaƊai ke sambatu na kamar mahaukaciya sabon kamu,babu wanda ya cemin Ƙala,sai ma harara da wasu ke bina dashi. ban ma san na riƘe hannunsa ba sai yanzu na Ƙara ƘamƘame hannunsa na ce"don Allah yaya Bilal ka tashi,idan ka mutu nima tabbas zan iya mutuwa,da kai na saba yaya Bilal tun ina Ƙarama ta ka nuna min so,ka nunamin Ƙauna,haƘiƘa banyi maka adalci ba". Da sauri shahid ya tashi ya fita waje,duk zuciyarsa babu daƊi wani irin kishi yaji ya turniƘe masa Ƙirjinsa,ya zauna kan wani benci ya saki kuka kamar Ƙaramin yaro,mutane sai wuce wa suke suna kallonsa yana son khairat da duka zuciyarsa yana jin ciwon rabuwa da ita,amman ya zama dole ya yi hakan don ayanzu ya gano ce wa ba Ƙaramin so khairat ke yi wa tsohon mijinta ba. Yana zama ammi ta biyo bayansa don ganin halin da Ɗanta ke ciki,itama duk zuciyarta babu daƊi ko kaƊan,ta ce"shahid ka yi haƘuri ka ka baiwa Allah lamarinsa,sam banji daƊin hukuncin daka Ɗauka akan aurenka da khairat ba,ka sani shi Allah yana tsara lamarinsa yadda yaso,khairat suruka ce ta gari a azamana da ita dana yi,bata taƁa yimin wani abu da raina zai Ɓaci ba,kullum ƘoƘarinta shine ya za'ayi ta kyautatamin,don haka ni sam banji daƊin wannan abinda ka aikata ba." Murmushi shahid ya yi wanda masu iya magana suka ce yafi kuka ciwo ya ce"Ammi ki daina magana ki yi shiru,saboda ni kaƊai nasan halin da nake ciki xuciyata tana yimin zafi sosai akan wannan sakin da na yi wa khairat,wanda ita kanta bata san na yi mata ba,ammi jiya fa dana shiga wannan bawan Allahn kiran sunan khairat kawai ya ke,sannan ciwon zuciya ya kamasa saboda Ƙaunar khairat da ya ke yi,Ammi ina da imani ina kuma da tausayi bazanso nima ayimin hakan ba,ni nasan nima zan iya shiga wannan halin akan Ƙaunar khairat,amman babu komai zan karƁi Ƙaddarata insha'Allah". ya rungume mahaifiyarsa yana kuka me tsuma zuciyar me sauraro,shahid kiran sunan Allah kawai ya ke yi,halisa ta fito daga cikin Ɗakin da jaririyar a hannunta ta tsaya a tsaye tana kallon shahid wanda ke Ƙwance kan cinyar mahaifiyarsa yana kuka kamar Ƙaramin yaro. sosai ya bata tausayi ta matso a hankali inda suke ta fara magana cikin harshen turanci ta ce"shahid ka yi haƘuri ka fauwalawa Allah komai,amman banji daƊin sakin da ka yiwa matarka khairat ba,don ba'a wasa da aure". a hankali shahid ya tashi daga kan cinyar ammi ya ƙarasa wajen halisa ya amshi ƴarsa.wacce ke ta baccinta hankali ƙwance.me kama dashi sosai ya zauna yana kallon ƴarsa cike da so da ƙaunarta.sai yanzu ma ya tuno bai yi mata huɗu ba ba.wasu hawaye suka zubo masa ya share su tuno da halin da yarinyar zata kasance na rashin mahaifiya akusa da ita.shi da yarasa mahaifinsa ma ya damu sosai balle kuma mahaifiya.gashi nigeria ba wajen zaman bane dole zai koma masar.ko england tunda dai shi ɗan asalin ƙasar england ɗin ne. yana gama raɗa mata sunan Ammi ta amshe ta.tana manna mata kiss a goshinta na jin daɗin ganin jikarta ƴar shahid gudan jininta.lallai wannan yarinya zata sha gata.ya ce"Ammi na raɗa mata suna da Rahma(khairat)taci sunan mahaifiyarta. 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 1003. . . . . . .1004 ---------Ammi ta ce"Allah ubangiji ya raya mana ita.amman ni dai zuciyata bata yimin daɗi wallahi,shahid ba kai kaɗai ka yi rashin khairat ba har ni,ni kaɗai nasan irin kyautatawar da take yimin.Allah ya tashi kafaɗar baban yaran na ta".dukkansu suka amsa da amin. Hajiya kaka ta ce"khairat don Allah ki fita a ɗakin nan ina ce wa kece kika tayar masa da ciwon nasa ko?tsabar rashin tausayi da kuma imani haka ki ka rufe idonki ki ka ce kin tsanesa.amman shine yanzu zaki wani dawo nan?maza ki tashi ki fita cen bama nemanki". Sosai na fashe da kuka har da majina na ce"haƙiƙa hajiya kaka ban yi wa kaina adalci ba.na cuci kaina da nunawa yaya Bilal tsana har haka.ko da me ya yimin bai cancanci inyi masa haka ba.don Allah ina neman yafiyarku ku yafe min".na faɗi hakan ina kuka sosai. Likita yana shigowa ya bada umarnin kowa ya fita zai duba Yaya Bilal,haka aka yi kuwa kowa ya fita sai ni kaɗai.har hajiya kaka ta fita sai kuma ta dawo ta ce"to ke uwar ƴan marasa jin magana komawa kika yi kika zauna kamar mijinki"?.jin hajiya kaka ta faɗi hakan tuni na tashi gabana yana

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87