Chapter 63
Chapter 63
kina da cikin ma,wannan cikin shine zai ƙara tsone idon maƙiya musamman ma Ruƙayya surukarki,don ɗazu da kiga dawo Ammaru yazo ya bani labari tana cen tana zaginki wai karuwa me bin maza,kinga kuwa yanzu zata tabbatar da hakan sannan hankalinta zai daɗa tashi".ta faɗi hakan tana ɗaga hannunta sama Alamar tana godewa Allah. Haushin Hajiya kaka ya kamani na ce"ayya hajiya kaka bazaki gane abinda na keji acikin zuciyata ba,sosai na kejin tsanar Bilal araina,na rabu dashi har abadan,ashe harda ƙullin cikinsa ajiki na?wallahi kaka zubarwa zanyi".na faɗi haka ina share hawaye harda majina. Hajiya kaka ta yi salati ta sanar da ubangiji sannan ta ce"ikon Allah ikon gaske,idan baka mutu ba zaka yi kallo khairat kina cikin hayyacinki kuwa?ko kuwa dai kin samu taɓin hankaline?kin zama me taurin kai Khairat,ba khairat ɗin dana sani adacen baya bace khairat ɗin dana sani acen baya yarinya ce me jin maganar nagaba da ita,amman ba wannan wadda ta tsaya agaba na tana yimin musu ba." "Kaka nifa wallahi zubar da cikin nan zanyi,tunda ubansu ma bai san da cikin ba,kuma gashi yana zargina kinga ai zai iya ce wa shi ba cikinsa bane,to kinga idan har na bari na haifesa zai iya ce wa shi ba cikinsa bane,kinga me zan ce wa yaron?ce masa zanyi ubansa ya ce shiba shine ubansa ba?kinga kaka bani da amsar da zan bashi dole in zubar da cikin yanzu kinga kowa sai ya huta". "To dan ubanki Malik baza'a zubar ba,zanga yadda za'ayi ki zubar da cikin idan har ban baki damar hakan ba,daga yau babu ke babu fita daga gidan nan sai inga ta yadda zaki xubar,tunda ke ƴar taurin kai ce".tana faɗar hakan ta fita fuu cikin fushi,Hajiya kaka bata fiya saurin fushi ba idan kuwa kaga ta yi fushi to abin ya yi yawa ne. Ranar nasha kuka kamar me,da yamma Rashida tazo waje na lokacin ina cikin ɗakin naƙi ci naƙi sha Hajiya kaka ta kawo min abinci amman ko kallon abincin banyi ba,saboda fushi itama bata ƙara bi ta kaina ba ta yi zamanta afalo ta kunna radionta,ta ware ta sosai sai ƙara take,haushi duk ya isheni idan na gaji sai in toshe kunnuwa na duka.ina jinta tana ce wa"oho dai babu inda mutum zaije,ko inyamura ce tazo nan baki isa ki fita ba,zan saka akiramin likita har gida ya duba ki eh tunda abin rashin mutunci ne,ai tattaɓa kunnen basu isheni ba eh so na ke sai sun kai ɗari sannan Allah ya ɗauki raina". Tana cikin wannan maganar Rashida ta shigo,ta ce"a'ah ƴar tsohuwa ina khairat ɗin?naji banji ɗuriyarta ba?."chono baki Hajiya kaka ta yi ta nuna hanyar ɗaki na sannan ta ce"tana ciki ƴar nema kin san fa tana da ciki to wai shine take son ta zubar eh saboda rashin mutunci,to nidai ba a gidana xa'ayi wannan kisan kan ba,ciki gashi nan har ya turo kai amman wai a haka akeson a zubar,saboda shashanci to wallahi baki isa ba". Da sauri Rashida ta faɗo ɗakin dana ke ta rungumeni ta ce"Allah na gode maka daka nunamin wannan ranar da zanga ƴaƴan yaya Bilal,don Allah khairat kada ki zubar da cikin nan kome za'ayi kada ki zubar da cikin nan,wannan cikin shine zai kawo ƙarshen komai".ta faɗi hakan tana kallon ciki na wanda ya turo kai sosai. Na ce"ni fa Rashida sai na zubar da cikin nan,saboda me xan barshi ubansa bai so,ko so ki ke in haihu ɗin yazo yana ce ba shine ya yi cikin ba?a'ah wallahi sai na zubar wannan sharrin ma da ya yimin abarni dashi,don haka ki bar wannan ma maganar sai na zubar."na faɗi hakan ina tashi daga ɗakin don dukkansu haushinsu na keji. Farlo na fito na zauna Hajiya kaka na ƙwance ta yi matashi da filon kujera ta saka radionta akunne tana ji,ta kalleni ta watsar sannan ta ce"ai kin banza ai ko uwarki ce ta harareni sai na faɗi magana balle ke tabi'i tabi'ina."banza na yi mata ina jin yadda ɗan cikina ke juyawa kamar juyin waina,ya tattaro ya dawo ƙasan mara,ga wata muguwar yunwa dana keji. Ina zaune Rashida tazo ta wuce ba tare da ta cemin komai ba,ta wuce cikin fushi na kalleta na watsar amman azuciyata banji daɗin abinda na yi mata ba,amman nima ai sai ayimin uzuri su fuskanci abinda na ke hangowa gaba. Hajiya kaka ta ce"hmm Allah khairat kina bani mamaki,yanzu ke kina ganin Rashida duk yadda ki ke da ita baza taji haushinki ba,akan wulaƙancin da ki keyi har kike ce wa zaki zubar da cikin yayanta,kuma kice zakuyi shiri?ai kema kin san kin cuci kanki". bance mata ƙala ba naji ina muguwar jin yunwa na ce"babu abinda ki ka dafa ne inci".?banzan kallo ta wur gamin sannan ta ce"oh yanzu abincin ki ke nema ko?wa yagaya miki barni gabas take?ai dole ki nemi abinci baka da komai ma ajikinka ka ke neman abinci?balle kuma ga ciki cikin ma ba yaron ciki ba,to wai ni yaushe rabonki ma da al'ada".?da sauri na kalleta na tuno last dana yi da sauri na ce"6 month fa na shiga uku".da sauri kaka ta ce"ke ni ban wani san turancinki ba na dai gane 6 ɗin,wato shida ko?,amman wannan yarinyar ko shasha wallahi yanzu ciki ajikinki har na tsawon wata shida amman baki sani ba?kina zaune kamar wata bagidajiya?".ah to yau ɗinnan zamuje asibiti." Banza na yi mata na wuce kitche ɗinta na buɗe indomie na dafa da ruwa ruwa na ɗakko nama a fridge na ɗan tafasa shi da albasa da kayan ƙamshi na ɗan soyashi sannan na haɗa da indomie ɗin.na fito na samu waje na baje na cika ciki na sai a sannan na ƙara kula da cikina yadda ya fito sosai. Hajiya kaka ta harare ni sannan ta ce"ai kin banza da mana kada kici,badon tattaɓa kunne na dake cikinki ba da baki isa ki wulaƙantamin abinci kice kuma zaki barmin shi ba,ai ko kina so ko bakya so sai kin cinyesa".ni dai bance mata ƙala ba na cigaba da cin abinci na,ina cikin cin abincin su Babana suka shigo sai da gabana ya faɗi ko kallon inda na ke baiyi ba,balle ya amsa gaisuwar dana yi masa. Abin ya tsayamin sosai sai kuwa naji yana ce wa"Umma wannsn yarinyar me ya kawo ta gidan nan?".saboda tunda naxo ƴan gidan basu san da xuwa na ba.Babu abinda kaka ta ɓoye masa na abinda ya faru dani,sai kuwa ya ce"umma shine ke kika ɗauketa ta kika ajjeta a ɓangarenki?ni tun tuni na cire wannan yarinyar daga cikin ƴaƴa na don ba zan zauna da bara gurbi ba". . . tun kafin ya ƙarasa maganarsa Hajiya kaka ta ce"kai Malik faɗi abinda ya kawo ka amman ba wannan ba,tunda dai kai ka kasa gane ce wa sharri akewa ƴarka".ta faɗi hakan tana harararshi. Yasan sarai halin mahaifiyarsu ba ƙara sauraransa za tayi ba koda ma ya yi magana,sai ya ce"Hajiya daman magana ce akan Yaya Abdullahi,to muna taso mu gaya miki ammsn don Allah kada ki tada hankalinki akan wannan,yanxu haka ma ya fara samun sauƙi". Da sauri kaka ta fashe da kuka ta ce"Allah sarki ɗana bawan Allah mutum me haƙuri,me yasa kuka ƙi faɗamin abinda ya faru,kuke ta ɓoyemin kuka cemin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87