Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,281 words 0 views Progress saved
Download Book

ta yi,kowaccs mata agidan so take Bilal ya ce yana son ƴaƴansu amman shi ya yi kunnrn uwar shegu harkokinsa kawai ya ke. To wannan maganar sosai ta hargitsa ƙwanyar ƴan gidanmu,musamman ma waɗanda daman ba so na suke ba,daga ni har mahaifiyata su mama iklima dukkansu jikinsu ya yi sanyi,wato ita wannan yarinyar duk muguntar da suka yi mata,ƙarshe sai dai ta zamo mata alkhairi,inji masu iya magana suka ce hassada ga mai tabo taki ce. Daga ni har mahaifiyata babu wanda yasan wannan maganar,saboda tunda mama tazo ko hirar ƴan gidanmu ba ballan tana ma har muji komai. Yaya Aliyu kuwa yasan komai don Baba Abdullahi ya kirasa ya faɗa masa komai,sannan ya ce kada a sake a gayawa ita khairat ɗin gaya mata kamar zai janyo wata matsalar,sannan suma ƴan gidanmu duk iyayenmu sunja musu kunne sosai akan kada a faɗawa Bilal har sai an ɗaura aure. **** "yanzu kai mukhtar saboda wannan lalatacciyar yarinyar ka ke kuka?yarinyar da agidannan har ciki ta yi shine don na ce baza ka aure ta ba,shine yanzu zaka sakani agaba kana kuka kamar wani yaro?"To wallahi ka buƊe kunnuwanka da Ƙyau ba zaka auri wannan yarinyar ba irin tsiya irin inyamurai,ni banda ma ubanka da ubanta ciki Ɗaya suke me zaisa ma in haƊa iri dasu,Kaji dai na faƊa maka don ni na tsani haƊa aure irin na kakarku ta haƊa kara da kishiya waje Ɗaya azo ayi ta masifa to ni haƊin nan ba dani ba,don haka ka maida hankalinka,bara'atun ma da ta liƘe maka ta yi ta gama don babu Ƴar da zaka aura ehe kaji dai na faƊa maka".tana faƊar hakan ta yi gaba abinta. Sosai mukhtar yaji haushin wannan mummunan zagin da mahaifiyarsa ta kewa sahibarsa khairat,sam ko a mafarki ba zai yarda ce wa khairat za tayi cikin shege ba,sai gashi ana yi mata Ƙazafi da ta yi ciki,tabbas zaiyi amfani da aikinsa na lauya ya tsaya tsayin dafi akan wannan Ƙazafin da aka yi wa baiwar Allah. ****** "yanzu Alhaji Ɗan na wa ne zai auri wannan yarinyar wacce ta zubar da mutuncinta tun awaje har ta Ɗakko ciki,shine ni za'a laƘabawa Ɗana ita saboda anga bai damu da kowa ba". "Hajiya RuƘayya haƘiƘa zanyi miki abinda baki taƁa zata ba,idan ki ka Ƙara ce wa khairat ta yi ciki?me yasa ku mutane arayuwarku kanku kawai kuka sani?muƘaddara ma hakan ya faru?ita sai aƘi aurenta saboda wannan?mata nawa ne suka yi cikin shege agidan iyayensu har suka haihu kuma hakan bai sa an sakesu ba?sai ita za'a ce baza a aureta ba?no possible ace kuma Ɗan uwanta bazai rufa mata asiri ba?abinda zan gaya miki shine,duk ranar da ki ka Ƙara zagin khairat kisan da ce wa zaki yi nadamar da baki taƁa tunani ba kinji na gaya miki,ruwan ki kiso auren ruwanki kiƘi so?"yana faƊar hakan ya yi fitarsa cikin tsananin fushi. A tun rayuwar aurensu Abdullahi bai taƁa fushi da ita irin na yau ba,sam bai da faƊa ko hayaniya mutum ne shi mai tsananin haƘuri kafin kaga abinda zai saka shi fushi ana daƊewa,daƁar ta zauna akan kujera wacce take tree seater azuciyarta tana tunanin ta yadda za'ayi wannan auren alhalin ranta bai so. ****** Na fara zuwa makarantar jami'a Ado bayero university kano,ina karantar fannin law(lauya),ban taɓa tunanin zanyi ƙoƙari kamar yadda na ka yi yanzu ba,saboda halin dana tsinci kaina har yanzu babu wanda ya faɗamin zancen aure na da yaya Bilal ko awajensu Rashida ban tsinci zancen ba,ga mama da muke tare itama bata sani ba ko abakin su yaya Salim kuma babu wanda bai san zancen acikinsu ba. Muna zaune a aji muna ɗaukar lecture,wata ƙawata Salima ta ɗan buge ni kaɗan ta ce"hmm Rahma ga fa mutumin ke nan?wallahi yana matuƙar burgeni sosai,handsome dashi". Banza na yi mata don ni sam hankalina baya wajensa yana kan wani note dana ke dubawa,ƙamshin turarensa yasa na ɗago don ƙamshin turarensa sak dana yaya Bilal. Ina ɗagowa muka haɗa ido dashi kyakkyawa ne sosai ba laifi,sai dai ko kaɗan bai kai yaya Bilal ba,na rintse idanuwa na ina jin zuciyata tana ƙuna sosai don tuno da yaya Bilal,na yarda ayanzu a tunanin yaya Bilal akashi ɗari yanzu babu goma aciki saboda yadda mama take ƙoƙari sosai akan in rage tunanin ko da kaɗanne. Hankalina yana cen kan tunani wanda na ƙwana biyu banyi ba,sosai ya ƙurawa khairat ido kamar zai cinye ta,yarinyar tana matuƙar burgesa sosai yana son mutumin da bai damu da duniya ba,wanda babu ruwanshi da tashin hankali so silent,bai taɓa tunanin zai auri mace mara mutunci irin matarsa ba,ga shegen surutu kamar aku amman kuma bata taɓa ganinshi da gemon arziƙi ba,idan kaga tana wani lallaminshi to tana son yin wani abu da kuɗine to zai ga kalolin tarairaya kala kala. Yana cikin tunanin monitor ɗin ajin ya shigo yana ta yi mai magana amman baiji ba,hankalinsa yana kan kallon khairat sai da monitor ɗin yaɗan buga desk ɗin sannan ya dawo cikin hankalinsa,duk kunya ta ishesa khairat ɗin ma hankalinta na cen tunani bata ma san wainar da ake toyawa ba,Salima sai dariya take ƙasa-ƙasa taɗan bangaji khairat ɗin sannan itama ta dawo cikin nutsuwarta,duk ɗagowarta sai sun haɗa ido dashi ta takura sosai tana addu'ar ya fita ko ta huta da wannan kallon. Ina dawowa daga makaranta naga yaya Aliyu da yaya Salim harda maher muka gaisa dasu hankalina na kan mama don ban jiyo muryar ta ba,ina zuwa falon naji tsit babu sai ƙarar tv dake kunne,abin ya bani mamaki don nasan mama afalo take zama gabana ya yanke ya faɗi,to ina mama taje?babu mai bani amsa don haka kai tsaye na shige ɗakinta wanda take ƙwana da ita da kakarsu. Sosai ta yi mamaki gani babu kowa,sai taji kanta har ya fara sara mata tabbas uwa ta dabance tunda mamana tazo bata taɓa barina ni kaɗai na yi tunanina ba,hankalinta na kai na tana bani labarai kala-kala ni kuma inyi ta dariya. Ina cikin wannan halin suka shigo,sai naji duk haushinsu na ke ji kamar su suka suga mama ta tafi,ana cikin hakan Anty khadija ma ta fito,ta wani kalleni ta watsar Khairat na hannunta. Yaya Aliyu ya ce"khairat sai kiga mama ta tafi ko?ki yi haƙuri lil sis bata son ki sani ne shiyasa ta tafi amman ta ce zata dawo ƙwanan nan."waau hawaye ne suka fara zubomin ina kukan na ce"wayyo mamana!yanzu waye zai dinga rarrashina ?mamana tana da lokaci na,bata son in shiga wani hali".sai na fashe da kuka kamar ƴar yarinya. Yaya Salim ya ce"haba khairat kamar wata ƴar yarinya insha Allah mu zamu dinga rarrashinki kamar mama tananan".ya faɗi hakan yana ɗago haɓata wadda ta gama jiƙewa da ruwan hawaye. Cire hannunsa na yi daga kan haɓata na ce"a'ah yaya Salim ba zaku iya kula dani kamar mama ba,ku mazane dole ko ta wajen ƙwanciya bacci zamu rabu,amman mamana har baci muke tare da ita,ni dai wajen mamana kawai zan koma". Na faɗi hakan ina kukan shagwaɓa Maher ya ce"kai anty khairat jibe kifa ƙatuwa dake kina wani kuka harda shgwaɓa ni idan na kula ma harda majina".?ya faɗi hakan cikin sigar zolaya. Da gudu na tashi na fara dukansa yana karewa da fillon kujerar,ni kuma ina

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87