Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,285 words 0 views Progress saved
Download Book

kalla ba hotunansu kawai suke cikin farin ciki,kana kallon fuskokinsu kasan cike suke da son junansu. Juyar da kaina gefe na yi ina ɗan kallon mutanen wajen,hall ɗin ya cika ɓam,kamar ba gobe kowa sai harkokinsa ya ke,sai dai fa ƴan gulma sun kasa sun tsare don suga abinda zai faru. Ƙawaye na da suka zo sai rungumeni suke muna hotuna,suna dariyarsu sai dai suma sun fuskanci ce wa nifa ko tani mijin ma ba ya yi,wata ƙawarmu Safiya ta ce"hmm ni dai idan baka mutu ba ka yi kallo?ki duba kiga namiji har namiji amman khairat ki ka damu sai kin auresa,yanzu ai gashinan ya samu kyakkyawa irinsa,sun barki sai ka ce wata bolarsu". wani malulu ne ya tsayamin aƙoƙon zuciyata ƙwalla ta sauka akan fuskata,wata me suna Hajara ɗaya daga cikin ƙawayen namu ta ce"Haba Safiya ai bai kamata kice haka ba,shifa ubangiji babu ruwansa da mai kyau da kuma mara ƙyau,idan Allah yasa ka auri miji mai kyau dole ne ya kula da kai,matuƙar yana so ya gama lafiya".. . . . .✍🏿 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 [23/09, 16:21] Miss Green🍀: 43. . . . .44 . . .taɓe baki Safiya ta yi sannan ta ce"hmm ni dai duk da haka wallahi ina jiye mata zama da miji irin wannan,yawancinsu kansu kawai suka sani,babu ruwansu da mutum za kiga har wani ɗagawa matar kai suke wai su gasu masu kyau,ko kuma kiga ana miki layi agida na neman mijinki". "To Safiya ko ma dai menene ta auresa,don haka daga baya kenan,Allah dai ya basu zaman lafiya".cewar Hajara. Ni dai sunkuyar da kaina kawai na yi,sai hotuna ake a hakan ni kuwa hankalina sam baya kansu,na tafi duniyar tunanin halin da zan sinci kaina aciki,don yaya Bilal sam bai son haɗa inuwa ɗaya dani. Tunda akazo wajen ko kallon ƙurata Yaya Bilak baiyi ba,hankalinsa duka yana ga jidda wacce take wani yimin kallon tara saura ƙwata,ni dai Allah2 nake atashi daga wajen don duk jikina amatuƙar sanyaye ya ke. Cen sai ga Hajiya kaka ta zo ansha gwaggwaro itama leshinta fari ne tas,ta yi sosai farinta na salin fulani da kuma kyaunta ya fito sosai,kai tsaye ɓangarena ta taho,ta kalleni sheƙeƙe sannan ta ce"yau naga ikon Allah ke saboda ba'a sonki sai suka matsa cen ke shine suka barmin ke anan?To yanzu zanji dalilin yin hakan?yadda waccen mara kunyar ta matsa sosai jikinsa kema haka zaki yi,yo in banda kalan dangi ai kece ma ƴar uwarsa amman shine zai wani matsa cen gefe,zanji abinda ya kawo wannan wariyar." tana faɗar hakan ta yi gaba abinta,ina janyo mayafinta don in hanata amman sai da taje,ta kusa dasu maryam ta wuce wacce ke zaune kusa da Yaya Aliyu sai zuba soyayya ake,ta wuce kusa dasu Yaya Salim da mero,su dai ba lallai ka gane basa son juna ba,don dukkansu sai hotuna ake gwanin sha'awa. "Inye au daman kai Bilal sakarai ne?tun daga yanzu mace ta fara juya ka?yadda uwarka ke juya ubanka?ah lallai su Ruƙayya za'a ɗauki darasi anan,kana wulaƙanta ƴar uwarka saboda wannan yaloluwar yarinyar wacce ko ƙugun arziƙi ba tada shi,aba kamar muciya an ɗaura mata zani,shine ka ke wani rawar ƙafa da rawar kai,kai ga me mata ko?to wallahi ka sake ka cuci jika ta Allah ya isa". Tana faɗar hakan ta dawo inda na ke ta janyo hannuwana fuuuuu,sai gani gaban Yaya Bilal,na tsaya da ƙer ƙafufuwa suna ta rawa saboda tsoro da fargaba. "Yauwa tsaya nan!". Hajiya kaka ke faɗar hakan ta ce"yauwa kema tsaya adinga yaƙe bakin dake tunda tallan makilin suke,ana wani hoto ana yaƙe haƙora kamar wasu masu tallan makilin".ta faɗi hakan tana harararsu. Abinda kaka bata sani ba,ashe duk ana jinta acikin lasifiƙa don kusa da lasifiƙar take,haushi sosai Bilal yaji akan wannan cin fuskar da kakarsa ta yi masa,don kakar tashi ta ƙara jin haushi sai ya riƙe hannuwan Jidda ƙam kamar wani zai ƙwace masa ita. Sai kuwa kaka ta ce"Hmm ai kin ɓur inji tusa,ai idan baka mayar da ita ciki ba,kai baɗan Ruƙayya da Abdullahi bane,shasha mara sanin ya kamata,ke kuma kina nan kamar wata ƴar tsana da wani jememmen jikinki". sosai aka saki dariya awajen,Hajiya Ruƙayya abinda surukar tayi ya tsaya mata sosai,kaɗan ya rage ta yi kuka tsabar takaici,wata ƴar uwar Hajiya Ruƙayya ta ce. "Wai ni Anty har yanzu wannan masifaffiyar tsohuwar bata daina rashin mutuncin nan ba?kawai ki saka yara agaba,don ba'ason jikarki,to uban waye yasa ta nace sai ta aureshi?ai yanzu gashinan agaban mutane ya wulaƙanta ta ai ni ya yi min dai dai daya wulaƙanta ƴar banza". Ita dai Hajiya Ruƙayya kasa magana ta yi saboda tsabar ɓacin rai,ji take kamar ta kama Hajiya kaka ta yi ta dukanta,saboda yau Hajiya kaka ta kai ta ƙarshe. Jidda taji zuciyarta kamar zata fito saboda haushin tsohuwar take ji,amman ta yi alƙawarin sai ta koya mata hankali sosai. Ko da akazo wajen yanka cake,sosai akayi drama don da Bilal ya bawa Jidda ta basa,sai ya kasa juyowa ya bawa Khairat sai dai abinda ya bawa kowa mamaki da sha'awa bai wuce yadda Khairat ta yanko cake ɗin ta saka a bakinta ba,sai da ta bawa kowa tausayi awajen,abinda kuma ya ƙara bawa kowa mamaki bai wuce yadda khairat ta juyo da Bilal ba,ta saka masa cake ɗin abakinsa. Ya samu kansa amai haɗiyesa,yana kallonta da mamaki da kuma ƙarfin hali irin na ta,Jidda kuwa ta cika ta yi ɓam,saboda haushi tana ta hararar Khairat. Ran Hajiya kaka ya yi fes da abinda ya faru,hajiya kaka ta kira mai hoto ta ce ya yi mata ita kaɗai da jikarta,haka kuwa akayi mai hoto yazo ya ɗandasa musu hotuna masu matuƙar ƙyau,ta janyo hannun Bilal ta saka ana khairat suka kalli junansu unexpected mai hoto kuwa ya ɗauka ƙes.ƙes. Sannan aka yi musu da hajiya kaka ma. Anci ansha amaren sai hidimarsu suke,gwanin sha'awa,nima yanzu na saki jikina gani ga su Rashida ga Maryam ma,ƙannen Anty khadija ko mutum ɗaya bai zo ba,saboda suna taya ƴar uwarsu kishi. Sai ƙarfe tara aka tashi goma sha ɗaya aka tashi daga dinner ɗin,muka koma gida duk a matuƙar gajiye,mun fito daga cikin wajen kawai idanuwa na suka kaimin kan Jidda da Yaya Bilal,tana rungume a ƙirjinsa har suka shiga cikin motar mai ƙyau. Na kafesu da idanuwa na,zuciyata sam babu daɗi sai yanzu na gane ce wa ka auri wanda ya ke sonka ma wani abune arayuwa,rai na duk babu daɗi muka tafi gida. Kowa ya yi bacci sai munshari suke,na wurwucesu duk sun baje akan kafet ɗin,suna ta bacci wasu akan gado wasu kuma a

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87