Chapter 48
Chapter 48
tsoron faɗar magana idan ta fito masa,suna gamawa shima yaya Aliyu ya kirani ya faɗamin yadda sukayi tsaf,a zuciyata na ce kaji ɗan rainin hankali wato ma kada inje indaɗe kamar ma ya damu dani. Tun dare na kira su zuhra da kuma zainab na shaida musu gobe monday,ina skull insha Allah,sosai suka yi murna suka ce a to ai gwara ki dawo ana ta karatu babu ke,harma anyi wasu c/A ɗin baki nan wata ma mune mukeyi miki ita,naji daɗi sosai don sun cika ƙawaye na ƙwarai. Washe gari da wuri na shirya na fice makaranta,sanye na ke cikin wata doguwar rigar material mai kyau,ta rufe min ruf jikina na samu nayafina babba na yafa da takalmina mai ɗan tsayi,kasan cewa ba doguwa cen ba.banyi wata ƙwalliya cen ba daman ni ba ma'abociyar yin hakan ba na dai gyara ƙwantacciyar gira ta wacce take acike ɓam da ita gata kuma baƙa ƙirin,na kalli madubi,ni dirarriyar macece sosai,baƙina bai hana aga kyau na ba.na ɗakko jakar skull ɗina na saka na fito na ɗan kurɓi ruwan tea kaɗan,na zuba dankalin dana soya acikin ɗan launch box ɗina mai kyau,na kulle sashe na fito,naji duk babu daɗi saboda na saba saka turare yau kuma har zan shafa sai kuma na ajje tunowa ta a matsayin matar aure. Ganin rashin dacewar tafiyata ba tare dana sanar dashi ba .har na yi hanyar ɓangaren jidda sai kuma na tuno da irin wulaƙancin da ta yimin rannan,kawai sai na yi hanyar waje duk raina babu daɗi. Nafi kusan minti talatin a bakin titi ban samu abin hawa,na fara tafiya a ƙafa zuwa cen babban titi kafin in samu abin hawa,saboda unguwar mu G.R.A ce babu adaidaita sahu. Sosai naji ana ta yimin hon amman ban wani juyo ba,saboda nasan idan na juyo wata ƙila irin ƴan iskan nanne,cen dai dana gaji na juyo ina juyowa sau naga Captain,ya washe min baki ya ce"a'ah kaga mata agidan Admiral B.ya akayi kuma kike tafiya aƙafa?". Fara gaishesa na yi yace"ikon Allah yanzu duk motocin A/D sai arasa wacce zata kai ki unguwa?".sunkuyar da kaina na yi ina wasa da ƴan yatsuna.fuskantar kamar aƙwai matsala ne yasa ya ce"ok shigo in rage miki hanya". Na shiga amman baya na zauna,wannan ɗin ma don nasan aminin yaya Bilal ne shiyasa na shiga,ya waiwayo da kansa ya ce"khairat ina zakije ne?". "Makaranta zanje Bayero university".murmushi ya yi sannan ya ce"ayya ashe kin koma skull Allah ya bada sa'ah,anjima Halisa zata zo to na kira Bilal sai ya ce wai ita jidda zata je gidansu,to shine na ce ai gaki agidan tazo wajenki.ashe ma kema makaranta zaki". "ayya ba komai idan naje bazan daɗe ba,daman yanzu test muke yi idan naje zan dawo da wuri,ka faɗa mata tazo".murmushi ya yi azuciyarsa yana ce wa oh wannan yarinyar baiwar Allah,gashi yaga alamar wannan ita ce ya kamata ta zamowa Bilal garkuwa agidansa.don ya fara zargin jidda,don duk abinda sukayi da Bilal tamkar a gabanta ne,don matuƙar yaje inda ya ke laɓewa don ɗaukar wasu abubuwa a gidan Damas sai yaga khairat,abin ya tsaya masa sosai kuma ya rasa yadda zaiyi ya faɗawa Bilal hakan,tabbas jidda ta cika butula me mantawa da alkhairi. ***** Na yi sa'a ina zuwa makaranta na haɗu da mutanen nawa musamman ma Zuhra,tana ganina ta rungumeni tana ihu,ga amarya ga amarya ai kuwa ƴan ajinmu suka zagaye ni suna tsokana ta,nan dai aka shiga hira da bani labarin abubuwanda suka faru da bana nan,kun san ƴan makaranta da gulma. Sai dariya na ke kamar ba niba,Zainab na zuwa ta dinga kallona up and down,na kalleta na ce"ke dalla banza me kuma ki ke wani ƙare min kallo?".na faɗi hakan ina dariya dimpils ɗina sai lotsawa suke gwanin sha'awa. Ta magantu sannan ta ce"haba khairat ba dole in kalleki ba,kinyi aure madadin muga kinyi ƙiba .sai wannan uwar ramar da ki kayi,jibe kifa da ma har kinfi ƙibar?". Shiru kawai na yi na sunkuyar da kaina don bansan ma me zance musu ba,lamarin aure wuyar sha'ani gare sa,balle kuma na karanta na sani Allah ya tsinewa mai tonawa mijinsa asiri,na wayance na ce"hmm rashin lafiya na yi ne maleria ke damu na,amman yanzu naji sauƙi sosai." Haɗa baki sukayi wajen yimin sannu,nan dai aka cigaba da hira na ke tambayarsu abinda za'ayi yau.Zainab ta ce"hmm mutuminki ne kuma kinsan ya yi tafiya". "Na ce to ni ina ruwa na da tafiyarsa Allah ya dawo dashi lafiya,daman baƙuwa zanyi ne shiyasa na damu,amman yanzu zan tafi". Har bakin titi suka rakoni na hau adaidaita sannan suma suka tafi gida,ina zuwa gida na ajje jakata nasha ruwa na jiƙa maƙoshi na,na shiga aikin girki,ina cikin aikin naji ana ɗan buga bell ta ƙofar falona,na goge hannuna na fito,Halisa ce tsaye bakin ƙofar ta sakarmin murmushi ta shigo. Na gaishe ta tare da kawo mata five alive da kuma ruwa,sai kayan gara ta dubulan da alkaki da kuma cincin,na ce mata zanje kitchen in ƙarasa girki.ta ce"a'ah muje tare in taya ki,ai nima na ɗan wasa jini".muka saka dariya muka shiga kitchen ɗin tare muna girkin muna hirarmu gwanin sha'awa. Na fuskanci Halisa macece mai hankali da kuma kamun kai,na yarda da hankalinta har naji ina tunanin sanar da ita halin dana ke ciki,ko zata taimakamin. Muna aikin na kalleta na ce"maman Junior don Allah so nake in faɗa miki wani abu,ina son ki bani shawara akan hakan?".murmushi kawai ta yi sannan ta ce"ayya ba komai ina jinki?ai ke tamkar ƙanwata haka na ɗaukeki". Babu abinda na ɓoye mata akan zamana da yaya Bilal,har na gama magana ta,kallona kawai take sannan ta ce"kash!gaskiya khairat kinyi sakaci babba tun acen baya,shi fa namiji da ki ke ganinsa ba'a nuna masa so me yawa,matuƙar ki ka nuna masa duk duniya babu kamarsa insha Allah to ke ce baiwarsa,don ko yana sonki to za kiga ya rage sonki,shi namiji haka ya ke yafi son mace me aji sosai,ba wacce zai sameta kai tsaye ba,abu na farko da zan nuna miki shine,kibi duk hanyar da zaki bi mijinki ya dawo hannunki,ba tare da kin nuna masa fuskar kina son ku daidai ta bane,kissa da kisisina ita ce ke jan hankali miji awajenki,ko da bai ra'ayinki don dole yaji babu kamarki,don haka yanzu ki buɗe kunnuwanki kiji ni?dole kayan sakawarki ki ajje duk wata atamfa da leshi agefe,ya zamo kayan sakawarki ƙananun kaya ne,Sannan ya xamana kin iya tafiya ta jan hankali tare da salo salo kala2 ta yadda zaki dinga jan hankalinsa". Sauke numfashi na yi ina ganin kamar baxan iya wannan abubuwan duk da ta faɗomin ba,na kalle ta na ce"ni wallahi mmn junior kunya na keji,idan na gansa sai inji kamar ƙasa ta tsage na shige ciki,wallahi ina jin nauyinsa". Kallo na sosai ta yi cikin nutsuwa ta ce"hmm ai kuwa khairat ba zaki taɓa fita daga cikin wannan matsalar ba,ki cire duk wani nauyi da jin kunyarsa.ki nuna masa kema macece,sannan idan ya shigo hannunki ki nuna masa jan aji sosai irin namu na mata,kada ki sakar masa kanki kamar wata jaka,don Allah khairat ki nutsu ki karɓi mijinki a hannu,wannan zaman da kike me aikin gidan nan ma ta fiki matsayi,don haka ki daure daga shi har jidda ɗin ki nuna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87