Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,279 words 0 views Progress saved
Download Book

to ni wallahi ba zan yarda ba don ni ba sallamammiya ba ce". haƙuri Hajiya kaka ta fara ba ta ta ce"ki yi haƙuri waɗannan yaran addu'a zamuyi ta yi musu Allah ya shiryesu,kuma daman inason in gaya miki kada ki yadda ƴaƴanki su mayar da yarannan makaranta don ƙara lalacewa zasuyi,kuma sannan su fito da miji ayi musu aure ko hankalin kowa ya huta". da sauri kaka ta ce"kai Inna gaskiya ƙwaƙwakwarki tana ja wallahi,ke daman tun muna yara kina da ja,su Hansai basuyi asarar kuɗin tara ba".dariya Hajiya Inna ta yi sannan ta ce"to ai kinga gwara ayi musu auren kowa ya huta,ko kuma ma idan sukace muku basu da mazajen auren ga ƴan uwansu maza nan sun cika gida taf sai a harhaɗasu kawai kowa ya huta." Sosai kaka ta yi murna da shawarar ƙawatarta Hajiya Inna,suka cigaba da tsara abubuwansu ni kuma na fito waje don tafiya sashenmu ƙafata ta yi tsami sosai jan ƙafar kawai na ke,ƙamshin turaren yaya Bilal naji naji wani irin mugun shauƙi har cikin raina ban ankara ba na ji an bangajeni an wuce na buɗe idanuwa da ƙer,Yaya Bilal ya wuce ko kallon inda na ke baiyi ba ballanta na ma in saka ran zaiyi min magana,wasu zafafan hawaye ne suka fara ƙwaranyo min,son maso wani ƙoshin wahala tun ina ƙarama ta na ke dakon son yaya Bilal har girma na amman shi ko ajikinsa idan ya ganni ma yadda kasan yaga kashi haka ya ke nunawa. Allah ya yiwa yaya Bilal halitta mai ƙyau da tsari kaf ƴan gidanmu babu wanda ya kai koda ƙwatansa a komai,ga ilimi,addini,ƙyau,kuɗi,nasaba.duk ta haɗa waɗannan abubuwan duk jikokun gidanmu farare ne yawancinsu amman ni ba fara ba ce,amman kuma baza'a kirani da baƙa cen ba,ina da ƙira mai ƙyau kuma ina da ƙyau dai dai gwargwado,ina da ilimi,tarbiyya,nasaba,da sauransu. Ina cikin wannan tunanin na shiga sashenmu kai tsaye na wuce sashen baccinmu daman kowa da ɗakin baccinsa amman yau ina shiga naga Nadiya a ɗakin baccina ta fito daga ita sai tawul ta fito daga banɗaki tana jan ƙafarta da ƙer wata uwar harara ta bugamin sannan ta fita daga ɗakin ban kula taba na shige ɗakina na ƙwanta a hankali duk jikina yana yimin wani irin mugun ciwo wasu zafafan hawaye suka zubomin tuno da abinda ya faru dani. Ina cikin wannan halin mama ta shigo ɗakin ta ce"a'ah khairat daman kina nan?ina ta tunanin shiga ɗakin kaka ashe kin shigo?tashi muje yayanki Bilal ya kirawo dr xai duba lafiyarki."har zuciyata na ji wani irin sanyi mai daɗi wai yaya Bilal ya kirawo likita?to ko dai shima ya fara sonane ban sani ba?ina cikin tunanin mama ta ƙarayimin magana na tashi na fita Yaya Bilak na hango ya wani kame a kujera ya yi ƙyau a cikin jallabiyarsa ƴar asalin larabawa,wata irin kunya ce ta baibaye ko ina na jikina a hankali na isa wajen na gaishesu amman Yaya Bilal ko kallo na baiyi ba.naji babu ɗadi a raina amman ban nuna hakan ko a fuska ba. Allura ya ce zaiyi min ta kashe zafin ciwo,rau rau na yi da idanuwa kamar zanyi kuka naƙi in tsaya ayimin wata uwar tsawa yaya Bilal ya yi min jikina yana kakkarwa na tsaya akayimin ina kuka.tsaki naji yaja sannan ya yi ficewarsa tare da ce wa"dr maher ka sameni a waje".da to ya amsa likitan ya kalleni sosai ya ce"sannu crazy girl".ban amsa masa ba na cigaba da matsar ƙwalla ta,ya ajjemin magungunan da kuma allurar da ba'a gama min ba.mama ta yi masa godiya ya tafi. Mama ta ruƙo hannuwa a hankali muka fara tafiya sai ga Hajiya kishiyar mama ta fito daga kitchen ta ce"hmm ayi dai duk a gama wai ke uwarki ta koya miki munafunci ko?to duk kuyi a sannu in dai munafurci ne na iya shi har na dameku ba dai ƴaƴanmu kika ɓatawa suna ba?hmm kijira na ki ɓatancin don kare ma bazai shinshina ba,shegiya ƴar inyamurai kawa".tana faɗar hakan ta yi shigewarta ta barmu anan tsaye tunani ya cika zuciyoyinmu,muka haɗa idanu da mama na bata ce komai ba ta kaini har ɗakina sannan ta bani magani ta tafi. "Ƴar halak yanzu na je tunaninki?".dariya Rashida ta yi sannan ta ce"Allah sarki Khairat ya jikin na ki?".ɗan murmushi na yi wanda yafi kuka ciwo na ce"da sauƙi Rashida". "Hmm gaskiya Khairat idan da zaki yarda da kin koma ɓangarenmu sai mu dinga ƙwana tare don ban yarda da zamanki a ɗaki ke kaɗai ba,ni fa waɗannan munafukan har yanzu ban yadda dasu ba,don wallahi zasu iya aikin tumasancinsu a gidannan don haka ni zanje in samu mama in faɗa mata komai". Ruƙo hannunta na yi na ce"kada kije Rashida kin san halin mama da gudun zuciya ba za ta taɓa yadda ba,don haka ki barta kawai Allah zai kareni daga sharrinsu".taɓe baki Rashida ta yi ta ce"to ni yanzu me zance Allah dai ya tsareki daga sharrinsu".nan muka cigaba da hirarmu. **** Washe gari da safe har ɗaki mama ta kawomin abin kari bakina ya kumbura sosai ta ce"Khairat kafin kici abincin nan sai na gasa miki bakinnan don ya kumbura sosai".mama da kanta ta gasa min bakin muna cikin wannan halin naji muryar hajiya kaka tana ta tujara a babban farlonmu,na kalli mama itama ta kalleni sannan ta ce"kaka ce ki fita ku gaisa".ina shirin tashi sai ga tabta shigo ta ce"wayyo Allah na me zan gani Khairat?kai amman waɗannan yara sun cika marasa mutunci,shiyasa yanzu ina shigowa waccen munafukar ta taho wai za ta gaisheni ko kallon iskarta ma banyi ba na yi tahowa ta,shegiya sadakar yalla". tana ta sababinta bance mata ƙala ba mama ma bata komai ba sai kuwa kaka ta ce"hmm ai ke Khairat sallamammiyar uwa kika samu tunda duk abinda za'ayi miki sai dai ta yi shiru ta yi zugudum kamar buhun lalle".ta harai mama da sauri mama ta fita don zamanta awajen ba alkhairi zai janyo ba don haka ta fita don tsahon shekarun da ta yi da kaka tasan halinta tsaf. "Ke ba fa zaki zauna a wannan sallamamman sashen na ku ba,ɓangarena zaki koma don na ga aƙwai masu halin awakai a gidanku,don haka ki tashi yanzu yanzu ba sai anjima ba mu tafi don bazan lamunci halin masu laluben mata ƴan uwansu ba,kada Allah ya turo mala'ikunsa su rushe mana gidan duka tunda saɓon Allah ake a gidan". kallon kaka na yi rau rau da idanu na ce"a'ah ni dai kaka babu inda zanje wannan sashen na ki mutum yaje ki yi ta yimai masifa abu kaɗan ki zageni".galala Hajiya kaka ta yi tana kallon Khairat ta ce"eh lalla ai barewa ba tayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba eh halin Malik ki ka yi tsaf na taurin kai to wallahi ko zaki yi kashin jini yasin sai kin bini sallamammiya kawai".tana faɗar hakan ta fito. A farlo suka haɗu da Nadiya da iman suna kallo a tv da sauri kaka ta murza idanuwanta ta ce"yo ikon Allah khairatu zo ki ganemin waɗannan masu halin mutanen annabi luɗi sunyi rashe rashe suna kallo,ko uban waye ya basu damar zama suna kallo?su da sukayi wannan mummunan laifi". Da sauri su Nadiya suka kalli kaka sukayi wuƙi wuƙi da

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87