Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,267 words 0 views Progress saved
Download Book

yanzu ciwon so ne ya kamasa daga kallo Ɗaya,da sauri jidda taja baya don Ƙur'anin da ta rungume yana son faƊuwa cikin fushi ta Ɗago tana kallon motar Bilal. A hankali Bilal ya fito daga cikin motarsa idanuwansa na kan jidda Ƙur wacce take sanye cikin green Ɗin hijabinta wanda ya yi matuƘar haska ta. ta buƊe baki cikin masifa xa ta yi magana,amman me ganin me fitowa daga cikin motar sai ta yi sauri ta mayar da maganar ta,sai dai sukayi kallon Ƙuda yafi na minti goma har sai da Ƙawarta Rabi'ah ta taƁa ta ta ce"ke jidda lafiyarki kuwa".? Da sauri ta dawo hayyacinta cikin jin kunyar Bilal ta sadda kanta Ƙasa,ya kalli zara-zaran yatsunta waƊanda suka sha jan lalle wanda ya yi mata mugun Ƙyau. A hankali jidda ta raƁa ta gefe ta wuce da sauri tana murmushi,Ɗan shafa Ƙwantaccen sajensa ya yi sannan ya bi jidda wacce har tasha Ƙwana,ya tsaya da motarsa a dai dai wajenta ya fito cikin muryarsa mai daƊi da zaƘi ya ce"jiddatul-khairi"!.da sauri ta juyo jin muryarsa wacce ta tafi da ita baki Ɗaya,gani take kamar babu wanda ya taƁa faƊin sunanta ya yi daƊi kamar haka". ganin jidda ta tsaya yasa Rabi'ah ta wuce gaba don har sun fara makara lokaci ya wuce,a zuciyar Rabi'a Tana ji da ma ita ce ta yi wannan gwagwaƁan dacen tunda take bata taƁa ganin namiji hamshaƘi irin wannan ba,kai ko a fina finan nan na indiyawa bata taƁa cin katari da mai aji kuma kyakkyawa irin wannan ba. kallon jidda ya yi sosai wacce take wasa da Ƴan yatsun hannuwanta take Ɗam wasa dasu ya rungume hannuwansa akan faffaƊan Ƙirjinsa yana murmushi ya ce"sorry jidda na tsare ki kan hanya wanda bai kamata hakan ba,amman ki yi haƘuri nima zuciyata ce ta kasa barina ij haƘura in Ƙyaleki har sai na zo na sameki". jin haka yasa jidda Ɗan Ɗago fararan idanuwanta farare sol wanda har wani ruwane ya kw taruwa acikinsu suna wani shining oily. Tuni ya Ƙara mace wa akanta yaji wani shork a jikinsa da kallonta da ya yi,ya ce"jidda ki Ɗago idanuwanki ki kalle ni"?.a Hankali ta fara kallonsa gabanta yana faƊuwa don wani irin mugun Ƙwarji ni ne da Bilal don ba abanza ya yi soja ba. "Jidda!tun kallon farko naji wani abu a dangane dake amman kuma na kasa tuna meye wannan abun dana ke ji acikin ziciyata,amman yanzu zuciyata ta bani amsa sonki da ƙaunarki sune suka kamani alokaci ɗaya,wanda dukkan wata rai an halacceta da son waninta,Jidda tunda na ke bantaɓa son wata mace ba dai dai da sakon ɗaya idan ba ke ba,jidda ke ce komai nawa ayanzu,ins fatan kema zaki ƙaunace ni kamar yadda na ke sonki". wata irin kunya ce ta mamaye ta tarasa a wani bigire za ta saka abin,wani nishaɗi da farin ciki take ji mara misaltuwa,ta rufe fuskarta da tafin hannayenta saboda kunyarsa,ko da bata faɗa masa ba wannan shine ya ke nuni da ta yi na'am da zancensa,don haka ya ƙara kallonta a karo na biyu ya ce"idan har ba zaki damu ba ina son muje inga gidanku"?.da sauri ta ɗago kanta ta ce"a'ah da zai yiwu dai ka biyoni kaga gidan,amman idan aka ga na shiga motar namiji bansan irin hukuncin da za ayi min ba".ta faɗi hakan cikin shawaɓa,sosai yaji ta ƙara burgesa arayuwarsa yana masifar son yaga mace tana shawaɓa ba yaga mace tana acting kamar namiji ba. Haka kuwa akayi kai tsaye ta koma gida tana tafiya cikin takunta kamar tana tausayin ƙasa har suka iso gidan na su,suna zuwa da sauri ta kallesa ta yi rau-rau da idanuwanta ta ce"to yanzu zan wuce makaranta kada ayimin bulala babanmu yana ciki". tana faɗar hakan da sauri ta yi hanyar islamiyyar tasu tana murmushi,ta daɗe tana jiran wannan ranar taga mijin daya ƙwanta mata.ko a mafarki bata taɓa tunanin Za ta samu miji irin Bilal ba,sai gashi ta samu mijin wuce sa'a,daman ko wani saurayi idan yazo wajenta ta koreshi sai ya ce wai ta fiya iyayi don tana ganinta mai ƙyau,shiyasa take ƙwaɗayi da buri. Har tasha ƙwana bao daina kallonta ba,yarinya ƙarama amman ta tafi da hankalinsa haka?shi kansa mamaki ya ke ko da awasa bai taɓa tunanin hakan za ta kasance dashi ba koda a nafarkine kuwa. Wani farin tsohone ya fito daga gidan,kana ganinsa kaga ba fulatani na asali,kamarsu ɗaya sak da ƴarsa ya faɗaɗa fara'arsa ya ƙaraso suka gaisa da Bilal sosai ya ke mamakin ganin wannan kyakkyawan saurayi,wanda kana ganinsa kasan kuɗi sun samu gindin zama ajikinsa. Ɓoye mamakinsa dai ya yi don wata ƙila ko wani abune ya kawosa. Cikin jin kunya da nauyin mahaifin jidda ya ce"Baba daman naga jidda ne ina sonta da aure so shine na ce bari in fara zuwa gidansu inyi iso sannan kuma idan an bani izini sai in fara zuwa zance".ya faɗi hakan cikin kunya da sunkuyar da kai. Sosai dattijon ya yi mamakin jin haka daga gareshi,ya daɗe bai ga yaro mai hankali irin wannan ba,da yawa yawan yaran masu kuɗi basu fiya tarbiyya ba,wani ma sai dai ya yaudari ƴarka ya tafi ba tare dama kasan abinda ya faru ba. "Yaro naji daɗin maganarka sosai don daman haka akeson neman aure,mutum ya zama jajirtacce kuma mai hankali wanda yasan ya kamata,to yaro ni dai ko daga ganin hankalinka nasan ka fito ne daga gidan mutunci,amman kai ɗan wani gari ne?kuma kai ɗan wani gida ne?". Cikin nutsuwa Bilal ya ce"to Baba ni dai ɗan asalin garin kano ne anan unguwar rijiyar zaki,wacce take nan ƙasanku,iyayena kuma ƴan asalin bauchi ne garin azare,ni ɗan gidan Alhaji Abdullahi mai ƙwabo ne". sosai mahaifin jidda ya faɗaɗa fara'arsa ya ce"ah to kace min kai ɗan gidan manya ne?masu kuma dattaku da sanin ya kamata,kai naji daɗi sosai sai dai inyi muku fatan Allah ya haɗa kanku da ƴa ta". *hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba* *GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE* 1, *MU GANI A ƘASA..🔥* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨* _Miss Hajo_ Guda ɗaya N300 Guda biyu N500 Guda uku N600 Guda huɗu N700 Guda biyar 1k *ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇* Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 StanbicIBTC Bank. Shaidar biya tanan 👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 ...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎.... *ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇 +227 84 50 64 76 *MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO* *miss green ce👉🏼* [23/09, 16:19] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚* 📃Littafi na 1 By🪶 *®️Ummu maher(Miss green)🍏🍀* _*TEAM GAWURTATTU BIYAR 5🔥*_ *Wattpad user name* Rabiatu333 *Arewabooks* rabiattu0444 Ya ku ƴan uwana mu yawaita addu'ar fita daga gida don neman kariya daga sharrin shaiɗanu. --------------- 25🟩26 . .. . ...Kai tsaye ya wuce gidansu captain,yana isa kai tsaye ya shiga gidan,da kansa yazo ya taresa,Halisa matarsa ta fito suka gaisa harda ɗansa ɗaya wanda sunan

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87