Skip to content

Chapter 58

Chapter 58

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,304 words 0 views Progress saved
Download Book

ƙara bi ta kaina ba ta yi zamanta afalo ta kunna radionta,ta ware ta sosai sai ƙara take,haushi duk ya isheni idan na gaji sai in toshe kunnuwa na duka.ina jinta tana ce wa"oho dai babu inda mutum zaije,ko inyamura ce tazo nan baki isa ki fita ba,zan saka akiramin likita har gida ya duba ki eh tunda abin rashin mutunci ne,ai tattaɓa kunnen basu isheni ba eh so na ke sai sun kai ɗari sannan Allah ya ɗauki raina". Tana cikin wannan maganar Rashida ta shigo,ta ce"a'ah ƴar tsohuwa ina khairat ɗin?naji banji ɗuriyarta ba?."chono baki Hajiya kaka ta yi ta nuna hanyar ɗaki na sannan ta ce"tana ciki ƴar nema kin san fa tana da ciki to wai shine take son ta zubar eh saboda rashin mutunci,to nidai ba a gidana xa'ayi wannan kisan kan ba,ciki gashi nan har ya turo kai amman wai a haka akeson a zubar,saboda shashanci to wallahi baki isa ba". Da sauri Rashida ta faɗo ɗakin dana ke ta rungumeni ta ce"Allah na gode maka daka nunamin wannan ranar da zanga ƴaƴan yaya Bilal,don Allah khairat kada ki zubar da cikin nan kome za'ayi kada ki zubar da cikin nan,wannan cikin shine zai kawo ƙarshen komai".ta faɗi hakan tana kallon ciki na wanda ya turo kai sosai. Na ce"ni fa Rashida sai na zubar da cikin nan,saboda me xan barshi ubansa bai so,ko so ki ke in haihu ɗin yazo yana ce ba shine ya yi cikin ba?a'ah wallahi sai na zubar wannan sharrin ma da ya yimin abarni dashi,don haka ki bar wannan ma maganar sai na zubar."na faɗi hakan ina tashi daga ɗakin don dukkansu haushinsu na keji. Farlo na fito na zauna Hajiya kaka na ƙwance ta yi matashi da filon kujera ta saka radionta akunne tana ji,ta kalleni ta watsar sannan ta ce"ai kin banza ai ko uwarki ce ta harareni sai na faɗi magana balle ke tabi'i tabi'ina."banza na yi mata ina jin yadda ɗan cikina ke juyawa kamar juyin waina,ya tattaro ya dawo ƙasan mara,ga wata muguwar yunwa dana keji. Ina zaune Rashida tazo ta wuce ba tare da ta cemin komai ba,ta wuce cikin fushi na kalleta na watsar amman azuciyata banji daɗin abinda na yi mata ba,amman nima ai sai ayimin uzuri su fuskanci abinda na ke hangowa gaba. Hajiya kaka ta ce"hmm Allah khairat kina bani mamaki,yanzu ke kina ganin Rashida duk yadda ki ke da ita baza taji haushinki ba,akan wulaƙancin da ki keyi har kike ce wa zaki zubar da cikin yayanta,kuma kice zakuyi shiri?ai kema kin san kin cuci kanki". bance mata ƙala ba naji ina muguwar jin yunwa na ce"babu abinda ki ka dafa ne inci".?banzan kallo ta wur gamin sannan ta ce"oh yanzu abincin ki ke nema ko?wa yagaya miki barni gabas take?ai dole ki nemi abinci baka da komai ma ajikinka ka ke neman abinci?balle kuma ga ciki cikin ma ba yaron ciki ba,to wai ni yaushe rabonki ma da al'ada".?da sauri na kalleta na tuno last dana yi da sauri na ce"6 month fa na shiga uku".da sauri kaka ta ce"ke ni ban wani san turancinki ba na dai gane 6 ɗin,wato shida ko?,amman wannan yarinyar ko shasha wallahi yanzu ciki ajikinki har na tsawon wata shida amman baki sani ba?kina zaune kamar wata bagidajiya?".ah to yau ɗinnan zamuje asibiti." Banza na yi mata na wuce kitche ɗinta na buɗe indomie na dafa da ruwa ruwa na ɗakko nama a fridge na ɗan tafasa shi da albasa da kayan ƙamshi na ɗan soyashi sannan na haɗa da indomie ɗin.na fito na samu waje na baje na cika ciki na sai a sannan na ƙara kula da cikina yadda ya fito sosai. Hajiya kaka ta harare ni sannan ta ce"ai kin banza da mana kada kici,badon tattaɓa kunne na dake cikinki ba da baki isa ki wulaƙantamin abinci kice kuma zaki barmin shi ba,ai ko kina so ko bakya so sai kin cinyesa".ni dai bance mata ƙala ba na cigaba da cin abinci na,ina cikin cin abincin su Babana suka shigo sai da gabana ya faɗi ko kallon inda na ke baiyi ba,balle ya amsa gaisuwar dana yi masa. Abin ya tsayamin sosai sai kuwa naji yana ce wa"Umma wannsn yarinyar me ya kawo ta gidan nan?".saboda tunda naxo ƴan gidan basu san da xuwa na ba.Babu abinda kaka ta ɓoye masa na abinda ya faru dani,sai kuwa ya ce"umma shine ke kika ɗauketa ta kika ajjeta a ɓangarenki?ni tun tuni na cire wannan yarinyar daga cikin ƴaƴa na don ba zan zauna da bara gurbi ba". . . tun kafin ya ƙarasa maganarsa Hajiya kaka ta ce"kai Malik faɗi abinda ya kawo ka amman ba wannan ba,tunda dai kai ka kasa gane ce wa sharri akewa ƴarka".ta faɗi hakan tana harararshi. Yasan sarai halin mahaifiyarsu ba ƙara sauraransa za tayi ba koda ma ya yi magana,sai ya ce"Hajiya daman magana ce akan Yaya Abdullahi,to muna taso mu gaya miki ammsn don Allah kada ki tada hankalinki akan wannan,yanxu haka ma ya fara samun sauƙi". Da sauri kaka ta fashe da kuka ta ce"Allah sarki ɗana bawan Allah mutum me haƙuri,me yasa kuka ƙi faɗamin abinda ya faru,kuke ta ɓoyemin kuka cemin wai ya yi tafiya ne ta gaggawa?ashe ɗana yana cen babu lafiya"?.sosai suka dinga tausar zuciyarta. Ina kitchen ina shan sanyayyan ruwan dana fito dashi acikin fridge bayan duk na gama jin abinda mahaifina ya ke faɗa,naji zuciyata tana min suya sosai na ɗaga gorar ruwan swan sai da na shanyesa tsaf sannan na ajje,sai ga Hajiya kaka tana kuka take faɗamin abinda ya faru,sosai jiki na ya yi sanyi donshi Baba Abdullahi babu ruwansu sam da rayuwa da rikicin da ke cikinta,na shafa cikina take naji son cikin ya shige ni,ko don babu komai sai saboda Baba Abdullahi sam bazaiji daɗin hakan daga gare niba,don yana iya bakin ƙoƙarinsa. A bayan mota muka zauna nida Hajiya kaka sai kuka take ina rarrashinta,a asibitin naga su Rashida har da jidda da Hajiya Ruƙayya,naje na gaisheta ko amsawa bata yiba,Jidda ta zubomin idanuwanta ƙuri tana kallona ganin cikina wanda ya fito sosai,itama hajiya Ruƙayyan sosai ta yi mamakin ganin hakan. ******** Captain Ahmad ya ce"a gaskiya Bilal bazan ɓoye maka ba,ka yi asarar mata irin khairat yarinya mai haƙuri da nutsuwa amman har ka yadda da wannan sharrin da aka yi mata?".wani banzan kallo Bilal ya yiwa captain sannan ya ce"ok kada ma in yadda kenan ko?in kamata da ƙwarto kace min wai ba haka bane?to meye ɗin?". Captain ya yi murmushin takaici sannan ya ce"a'ah ni gaskiya ban yarda ba,kai meye shaidarka na yadda da hakan"?.ya faɗi hakan yana kallon Bilal.murmushin takaici Bilal ya yi sannan ya ce"eh to ai har masu gadi na tambaya suka shaidamin tunda na yi tafiya take yawo,kaga kuwa dole in yarda".ya faɗi hakan cikin gadara. "Hmm lallai Admiral da sauranka,kai wato har yanzu baka san mutane ba?suyi maka micijin sari ka noƙe ba".? Micijin sari ka noƙe sunan novel ɗina sa zan fara bayan na huta. Ɗakko wayarsa ya yi cikin aljihunsa ya shiga wani vedio ya nunawa Bilal ya ce"wacece wannan?".da sauri Bilal ya ce"jidda ce".captain ya yi ɗan murmushin gefen baki sannan ya ce"wannsn vedio ɗin yafi guda

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87