Chapter 18
Chapter 18
ƙwayar idanuwa na ya ce"khairat zuciyata ta kasance tana tare da ke ko da ke ɗin ba kya wajen?zuciyata tana mararin son ganinki ako da yaushe,zuciyata tana ƙaunarki da sonki,ki taimakamin ki yadda mu ƙulla soyayya mai ƙyau da kuma tsafta har ta kaimu ga aure."ya faɗi hakan yana kallona da idanuwansa da sukayi jawur yanzu yanzu". kasa ce wa komai na yi don maganarsa ta girmi ƙwaƙwalwata ya ce"kinyi shiru khairat yin shirunki dai dai ya ke da rashin amincewarki,wallahi indai baki sona kada ki ƙwari kanki ki faɗa min don arayuwata ina son wadda take sona don mu rayu cikin so da kuma amince wa." "Yaya Mk ka taɓa ganin wanda ya ke ƙin ɗan uwansa na jini?to bazan taɓa ƙinka ba nima ina sonka kamar yadda ka ke sona. . ."tun kafin in ƙarasa ya kama hannuna ya yi min kiss sannan ya ce"tnx so much khairaty ina ƙaunarki da yawa".idanuwa na ne suka firfito sosai tashin hankali ƙarara akan fuskata ban sake ce wa komai ba har ya buɗemin motar na fito. A tare muka shiga cikin gidan dashi mai aikinta tana farlo tana goge tile muka shiga,ta gaishemu muka zauna nan ɗinma hirar soyayya ya cigaba da yimin,ni kuwa mamakinsa kawaai na ke daman haka ya ke?don a gida ba zaka taɓa tunanin haka ya ke ba don ko dariya bai cika yi ba,don ko da su Amina ƙannensa bai fiya wani hira ba.azuciyata na ce namiji kenan a harkar soyayya babu babba babu yaro kowa yi ya ke. Ganin zaman na mu ya yi yawa ga shi har na gaji da hirar yaya mk na ce masa"bari inje ɗakinta ina tunanin bacci take".ya bini da kallo har na shiga ai kuwa baccin take ta ƙudunduna da bargo sai bacci take,ɗakinta duk kaya ko ina ga kayan yaya Aliyu nan daya cire haryanzu suna wajen mamaki sosai abin ya bani daman haka Anty Khadija take da ƙazanta ko kuwa ba abin mamaki bane don mahaifiyarta ma haka take,a hankali na fita daga ɗakin na samesa a farlo na faɗa masa bacci take ya ce"oky babu komai ni zan tafi don office na nan yana jirana".main compound na rakosa sannan na koma. har na juya sai ya ce"khairat!".cikin wani irin salo kamar shi kaɗai ne ya taɓa kiran sunan na wa da haka a hankali na ƙaraso kusa dashi na ce"ga ni yaya"?.murmushi yayi sannan ya ce"daga yau adaina ce min yaya na fi son azaɓomin suna mai natuƙar daɗi".ɗan murnushi na yi kawai na yi wanda bai kai zuciya ta ba,na sunkuyar da kaina ban ƙara ko da ɗago kaina na kallesa ba don idan na kallesa sai inji kamar Yaya B,na ke ganin a gabana ba wai don kama ba a'ah tsabar son da na ke masa ne sai na ke ganin kamar duk wani namiji tamkar shine. Ganin bazan ce komai ba sai ya ce"look! khairat ni fa wannan kunyar ta ki cutata kawai take wallahi,ni gaskiya mutum ne mara kunya gaskiya,kinga kuwa dole ne kema ki zama mara kunya don ina son a dinga bani kulawa yadda ya kamata".ɗan murmushi na yi don abin nasa dariya ya fara bani.daga nan mukayi sallama na miƙe na shige gidan har na shiga yana kallona yana bakin motarsa ya shafa sajensa wanda ya ƙwanta luf,wannan kuma gadone na ƴan gidanmu duk wani ɗan gidanmu zaka samesa da saje matuƙar kuwa ya fara girma to har da gemu. Ina shiga na kalli mai aikinta na ce"bata ce ki ɗora mata komai ba"?.ta ce"eh gaskiya bata ce ba don idan tana bacci har sai ta tashi sannan a ke yi".ɗan taɓe baki a yi sannan na tashi na shiga ɗakin da ke kusa da na ta.wa'iya zubillah ɗakin duk ƙura haka na ajje kayana a waje na cire wanda nazo dasu na yi ɗaurin ƙirji na hau aiki tas-tas na gyara ɗakin sannan na kunna burner ta ƙamshi na shiga bayin ma na wanke shi tsaf na kunna na'urar busar da banɗaki wacce ke cire duk wani bacteria idan da aƙwai. Ina fitowa na ce"mama iya farlo kawai ta ce ki dinga gyarawa ne"?ta ce"eh wallahi bata bani umarnin gyara ɗakinta ba kawai iya farlo ne,shima ada sai bayan ƙwana biyu sannan na ke sharewa wai bata don ƙura".mamaki sosai abin ya bani na wuce kawai ɗaki na faɗa wanka ina tunanin halin da yaya Aliyu ya ke,sam bai son ƙazanta don bai taso ya samu mamanmu na yi ba,tsaf za ta gyara ko ina har ɗakin Babanmu in dai ranar ƙwananta ne zakaji ko ina ƙamshi kuma ko ina tsaf,ga ladabo da biyayya ga haƙuri,shiyasa baka taɓa jin kansu matuƙar har idan ba Hajiya kaka ba ce ta haɗosu,mahaifinmu da kanshi ya ce yafi jin daɗin zama da mahaifiyarmu saboda babu ruwanta ita haka rayuwarta take,kuma duk ita mukayo da rashin son magana Salim ne kawai shegiyar zuciya kamar ta kuturu wannan kuma zuciyar babanmu yayo. ina gama wankan na fito na shafa maina me shegen ƙamshi da kama jiki sannan na wuce zuwa kitchen shima dai ƙazantar ce fal acikinsa ga abinci nan wanda ba a cinye jiya ba duk kyankyasa sun hau kai,kamar zanyi amai a haka na toshe bakina na gyarasa tsaf na saka air freshner ya hau ƙamshi sannan na shiga tsore na ɗebo dankalin turawa da kayan miya nazo na gyara na yi blnending ɗin kayan miyan sannan na ɗakko nama a fridge na wanke shi tsaf na tafasa shi sannan na ɗakko wata tukunyar daban na zuba mai na soya naman da kayanmiyan sannan na ɗan tsar da ruwa kaɗan na zuba curry da mai ɗanɗano yana tafasa na zuba dankaline wanda na feraye sa na wanke na yankasa a slice amman da kauri sosai saboda kada ya narke na zuba tafarnuwa da ƴar citta.haba sai ga girki ya hau ƙamshi sosai,na buɗe fridge na ciro mango ƙato na zo na wankesa tsaf na cire ɓawon sannan na cire tsokar na saka a blender ta markaɗa fruit yana markaɗuwa na zuba ruwa mai sanyi na faro harda ƙanƙara na ƙara blending sannan na juye na ta ce sa sosai,na juye a jug sannan na zuba suger enouph sosai ya fara ƙamshin mangwaro mai warin gawasa.girkina yana yi na sauke na zuba a babbar kula shima lemon mangwaron na saka sa a fridge sannan na wanke ƙwanukan tsaf na goge kitchen ɗin sannan na fito har lokacin bata tashi ba na yi mamakin mugun baccinta ace tun sanda nazo kusan awa uku mutum yana bacci,na zuba abincina na ci cikin ƙwanciyar hankali nasha lemon mangwaro na ina lumshe ido.sai ga ta ta fito daga ita sai rigar bacci iya guiwa duk gashin kanta a warwatse,na kalleta a fakaice na gaisheta ta amsa da ɗan wani guntun murmushi ta ce"au ashe ma kinzo?daman tunda zai tafi ya ce min kema yau zaki xo saboda bani da lafiya ne".sannu na ce mata kawai na cigaba da shan lemona ina kallo.ta ɗan kalleni duk sai taji kunya ta ce"kai rabonda naji ƙamshi mai daɗi har haka har na manta wallahi,gidan ya yi tsaf wallahi ban iya aikinne saboda wannan ciwon da ya sako ni agaba".ta faɗi hakan tana buɗe wamers na abinci ta ce"ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87