Chapter 68
Chapter 68
Baba Abdullahi. Agigice suka fito su dukkansu kowa hankalinshi atashe,Baba Abdullahi ya ce musu bari yaje ya fito da mota don mu tafi asibiti.Hajiya Ruƙayya ta shigo suka riƙeni ita da kaka Nusaiba sai kuka take,tuni ta fiddo wayarta ta kira yaya Bilal da number ɗinsa ta ƙasar waje. Sosai hankalinsa ya tashi jin abinda ƙanwar tashi take faɗa masa.da sauri ya rubuta excuse akan ce wa matarsa ce babu lafiya xaije.aka amince masa tuni ya hawo fly ya taho duk hankalinsa atashe. Da gaggawa suka amsheni aka yi ɗakin haihuwa dani duk na fice hayyacina sosai.gashin kaina duk ya barbaje saboda tsabar zaba.da za'a shiga dani na riƙe hannun kaka na ce"Kaka don Allah zan bar miki wasiyya koda na mutu,don Allah ki riƙemin abinda zan haifa don Allah". Kuka kaka take ta ce"babu abinda zai kare ki jikata,mafi soyuwa araina Allah zai saukeki lafiya kinji".basu bari na bata amsar ba suka shiga dani ɗakin haihuwa.sosai ake shan gumurzu amman har yanzu ban haihu ba,ilahirin mutanen gidan duk sun taru kowa hankalinsu a tashe,Yaya Salim ma ya taho amman mero ta saka masa kuka wai sai tazo,dole ya taho da ita saboda itama a lokacin tana da cikinta na wata biyar. Duk ana zazzaune anyi jugum-jugum kowa da tunanin da ya ke aransa,kawai sai aka ga Bilal ya shigo asibitin amiliyan kamar mahaukaci,rigar sanyinsa irin ta sojoji ya cire ta,tana hamnunsa sai ƴar t-shirt ɗin.kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankal kowa ya tashi yana mamakin to waye ya faɗawa Bilal ɗin?gashi kuma har yazo. Bai samu damar gaisawa da kowa ba kamar yasan ɗakin haihuwar,kawai ya tura ɗakin saboda yaga duk anan suke zaune ƙofar ɗakin,kawai likitocin sai ganinsa suka yi a ƙofar ɗakin haihuwa,Masu karɓar haihuwa suka ce"haba yallaɓai maza fa basa shigowa,ka yi haƙuri ka fita".. Da sauri ya kalli unguwar zoman sannan ya ce"bazan fita ɗin ba,matatace zata haihu sannan kice in fita bazan fita ba".yana faɗar hakan ya yi inda na ke ƙwance ina yarfe hannuwana duk gumi ya jiƙani,gashin kai na duk ya barbarje ga cikin ya dawo mara gab. Da gudu ya ƙaraso waje na yana kiran sunana,tare da faɗomin sunayen Allah yana tofamin,unguwar zoman kawai kallo suka koma yi,yadda ya ke ta tofamin addu'o'i yana kuka kamar ba soja ba,kuma gashi unguwar zoman sun gansa da uniform na sojoji masu manyan muƙami,suka shiga ɗan kallon junansu suna ƴar gulma irin ta mu ta mata. A hankali ya ce"Khairat daure ki yi nishi da ƙarfi,ga kan ɗa nan ya fara fitowa".ya faɗi hakan yana ɗan buɗe zanin da suka rufamin.a hankali na fara nishi kan ɗan yana fitowa yana riƙe da hannaye na ya tufamin ayoyin Allah,a hankali ya saka safar hannu ya saka hannayensa biyu ya fara jawo ɗan a hankali.har sai da ya fito baki ɗaya. Tuni na fara jin reliep,ya miƙawa likitocin yaron namiji kyakkyawan gaske irin babansa kama hik kamar ya yi kaki,ai tuni naji wata naƙudar ta ƙara sakani agaba,tsoro ya bayyana akan fuskar yaya Aliyu ya yiwa Allah hamdala,ya ciromin ƴa mace kyakkyawa amman wannan kamarmu ɗaya da ita,kuma ita bata kai namijin fari ba. Yana miƙa musu ya juyo yaga na riƙe hannayensa duka biyu ina kiran sunan Allah,alamar wata naƙudar ta taho,sororo ta ya yi yana kallo na saboda mamaki amman ba'a mamaki da ikon Allah.ƙarshe dai sai da na ƙara yo wasu ƴan biyun,duk maza Yaya Aliyu yana cirowa yana hamdala har suka gama fitowa baki ɗaya,ya kalli gabas ya yiwa Allah sujjada yana kuka. Ɗaya bayan ɗaya suka ɗoramin yarana a ƙirji naji ɗuminsu suka ji nawa,tuni na saki kuka wanda a ɗazu banyi ba,naji wani irin mugun son ƴaƴa na yana shiga ta,tare da godewa mahaifiyata akan haihuwa ta da ta yi,don yau ɗinnan naje lahira ina ga yafi sau goma saboda azaba,ashe haka uwaye mata suke shan wahala?lallai duk wanda baiji tausayin iyayensa ba ya yi asara. Yaya Bilal fa yana maƙale dani sai da umguwar zoman suka bashi haƙuri ta fita akan ce wa zasu gyarani da baby's ɗina,don dole ya fita shima sai gumi ya ke kamar tare muka yi haihuwar,yana fitowa dukka suka taso ya zauna kan kujera yana mayar da numfashi.tuni dukkansu jikinsu ya yi sanyi,harda Baba na ma awajen,Yaya Aliyu ya yi ƙarfin halin zuwa ya tsugunna gaban Yaya Bilal ya ce"yaya dai ta haihu?".ɗagowa yaya Bilal ya yi a hankali kamar wani abu ya faru sai kuma ya hau dariyar murna ya ce"ta haihu ƴan huɗu". Ai wajen wasu harda rawa wasu kuma sai kabbara suke suna mamaki sosai,ƴar yarinya ƙarama ta haifi yara har huɗu.Hajiya kaka ta ce"kai yanzu bikin rawa yazo,daman banyi rawa ba bikin uwarsu saboda bani da lafiya,amman yanxu sai na yi,tuni ta hau rawarsu irinta tsoffi sai dariya akewa Hajiya kaka. Tuni aka shiga bugawa ƴan uwa na ƙauye dana birni,su Rashida da Maryam tuni suka taho murna kamar za ta kashe su,aka cika asibiti mam allurar bacci aka yimin don in samu hutu,don su da kansu sunyi mamakin ƙoƙarin dana yi na haifar waɗannan narka narkan ƴaƴan kuma ba tare sa c.s ba. Dukkansu aka basu damar zuwa don ganin yaran,suna ƙwance kan gadonsu na yara macen ce a tsakiya me kama dani sak,Hajiya kaka ta ce"au ikon Allah harda ƴar baƙa aciki kuma?yara sunyi gado,mazan duk ubansu sak macen kuma uwarsu ƴar baka."duka wajen aka saka dariya kowa yan sha'awar yaran kamar ƴan catoon. Nusaiba ta saka hannu zata ɗauki ɗaya daga cikinsu da sauri yaya Bilal ya riƙe hannunta ya ce"a'ah ajjesa ya huta wallahi,baxa'a jagwalgwalamin yara na ba".dukka wajen aka saka dariya ganin Bilal ko kunya bai ji ba. ********* Har a radio sai da aka buga haihuwata mutane sai zuwa min barka suke,ɓangarenmu na koma ɗakin mahaifiyata da ya ke yana da girma sosai,babu kowa yanzu su mama Iklima tuni an fara ƙarɓar gashi daga xamam gida,don su Amira da Afra sunje sun gaya musu haihuwar,sunyi mamakin ganin iyayen nasu duk yadda suka koma,abin tausayi. Sosai Yaya Bilal ya ke rawar kai akaina ni da ƴaƴana,ina ganin ya shigo sai in tashi in bar masa ƴaƴansa awajen ya yi ta sumbatarsu,sai yafi awa ɗaya awajensu Hajiya kaka kuwa ta kance".kai don Allah ka fito masu zuwa barka na zuwa amman kai ka shige ɗaki".sai ta shigo ta sakashi a gaba har sai ya fita. Mamana ana gaya mata ƙwana uku da haihuwa sai gata,harda ƙanwarta ranar kuma su mama iklima suka zo yin barka,har ƙasa suka tsugunna suna bawa mama haƙuri har dani akam mu yafe musu. Muka yafe musu ɗin tunda yanzu sune acikin matsala duk sun lalace don kuwa yanzu duk acikin ƙannen su suke,suyi ta yi musu rashin kunya,ita Anty ma mahaifiyarta ta rasu matar ubace sai abinda ta ce ayi agidan shi ake. Mamana suna fita ta ce"Allah sarki rayuwa khairat,alokacin da naji labarin mutuwar aurenki sosai na yi baƙin cikin hakan,na yi kuka sosai na share hawaye na na cigaba da yi muku addu'ah ku dukanku akan Allah ya karemin ku baki ɗaya,gashi kuwa Allah ya karemin ku cikin amincewar ubangiji." Anan kuma mama ke bani labarin mutuwar aurenta,na yi mamaki sosai ta ƙara da ce wa"hmm khairat ashe mutumin nan mutumin banza ne,har safarar miyagun ƙwayoyi yana yi,babu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87