Chapter 46
Chapter 46
don ba nida wata amsar da zan bata,don na fitar azuciyata ce wa na cire tsammanin wai wataran Yaya Bilal zai soni kamar yadda na ke sonshi. "Yauwa gobe ne fa hutunki zai ƙare amarsu don wallahi nida zee munyi matuƙar missing ɗinki sosai,mutuminki ma sir Deen sai tambayarki ya ke muka ce masa ai kin riga da kinyi aure,wallahi ina baki labarin har kuka sai da muka laɓe mukaga yana yi,kai ni da zee munga abin mamaki." "Hmm" kawai na ce don ni yanzu ban ma san yadda za'ayi da makarantar ba. ina gama cin abincin na tashi na fita duk jikina asanyaye,sun daɗe da dawowa don haka kai tsaye na wuce sashen Jidda,suna zaune afalo suna kallo Jidda ta jingina da kafaɗar Yaya Bilal na yi sallama na shiga. Gabana ya bada wani rassss,kaɗan ya rage zuciyata ta buga,dukkansu wani kallo suka bini dashi,cikin sarƙewar murya na fara gaishesa,wani banzan kallo ya yi min sannan ya cigaba da shafa kan jidda kamar me yi mata shafa. Da ƙer na buɗe bakina sannan na ce"daman Yaya Bilal ina son ka bani izini gobe zan koma skull ne". Ko kallon ƙura ta bai yi ba,sai da ƴar gaban goshin nasa ta ce"honey kace ta fitar min a ɓangare na wallahi wari take... .✍🏿 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 [23/09, 16:23] Miss Green🍀: 51. . . .52 . . . .tsananin mamakin wulaƙancin jidda yasa na kasa koda motsawa,sosi maganar jidda ta daki zuciyata,wato ma nice na ke wari?lallai jidda tazo da abinda bazan ɗauko ba. Kallon ƙasa na yi wa jidda kafin Bilal ya buɗe bakinsa ya yi wata magana,cikin fushi na ce"jidda haƙiƙa ke acikin mutane ta dabance shiyasa kike ganin kanki kamar wata sarauniya,to ki sani dama ɗaya ce arayuwar ɗan adam,idan kuma ka bari ta wuce ka to ta wuce ka har abada,don haka ki taka asannu2 duniya ce tafi bagaruwa jima daɗi". Ina faɗar hakan na fita da sauri daga ɓangaren,zuciyata tana ƙuna sosai wato yau nice na ke wari awajen jidda?yarinyar da da kuɗina nasha biya mata kuɗin watan makarantar islamiyya,wai yau ita ce ke kira da me wari.na faɗa sashe na ina wani irin kuka mai cin rai,tabbas idan waɗannan abubuwan suka cigaba da faruwa to tabbas barin gidan nan zanyi,don naga alama yaya Bilal so yake ya sakamin ciwon zuciya don gab take da ta buga ƙarshe kuma inyi wa iyayena asara,don ko kusa nasan yaya Bilal ba zaiji ciwon mutuwa ta ba tunda ba damuwa ya yi dani ba. Ina fita jidda ta kalli Bilal wanda kansa ke wajen system ɗinsa,yana shigar da wasu bayanai akan Damas,sai kuwa jidda ta saka idanuwanta sosai,ta ɗauki wayarta ƙirar iphone,ta ɗauki hoton abinda Bilal ya ke,ganin ya juyo yasa tayi saurin ajiye wayar don kada ya ganta. Ya ce"jidda bana son kina biyewa wannan yarinyar,don sam ni bana sakata acikin masu hankali shiyasa ma kika ga ban kula ta ba,don ko kallon inda take bana son kalla".sosai jidda taji daɗin hakan ta ƙwanta a faffaɗan ƙirjinsa tana shafa sa ahankali cikin kissa irin tamu ta mata ta ce"hmm shiyasa darling kaga ko kallonta banyi ba.don warin jikinta ma ya ishi mutum". Wayarsa ce ta fara ringing ya ɗaga yana ce wa"Ahmad lafiya dai ko?dan kasan idan ina tare da iyalina bana san kowa ya shiga sabga ta".? Dariya captain ya yi sannan ya ce"ikon Allah masu mata manya,to idan banda abin ka yaushe ne ma kayi auren?".ya faɗi hakan yana dariya ya ce"to ka fito waje nazo inason yin magana da kai?idan madam ɗin ta bari sai ka fito,Angon Hauwa da khairat".wannan magana ta ƙarshe da captain ya faɗa ita ce tafi tsayawa jidda ta kalli wayar ji take kamar taje ta shaƙe Ahmad ta cikin wayar don Allah ya gani ta tsanesa. Bilal bai ce komai ba ya fita tare da janyo jidda ya yi mata wani irin hot kiss sannan ya fita,ta tsaya kamar tabi sa taje ta shaƙe wannan captain ɗin,sam ta tsani taji an danganta wata mace da Bilal don son da take wa Bilal,tare da matsanancin kishinsa. "A'ah kaga angon mata biyu har ka fito?".Banxa Bilal ya yi masa sannan ya ce"kaga mlm faɗi abinda ya kawo ka?kawai ina cikin nishaɗi na da matata ka wani zomin?sai kace gauro,ƙarfe nawa yanzu?". Sosai captain ke dariya harda riƙe ciki,Bilal cikin jin haushinsa ya ce"au daman iskanci ne ya kawo ka?to maza zo ka tafi wallahi".gimtse dariyar ya yi don yasan mutuminsa aƙwai shi da saurin fushi. Haɗe rai shima captain ɗin ya yi sannan ya ce"to akoma bakin aiki yanzu,kana sane da abubuwanda suke faruwa kuwa?a game da Alhaji Damas?na yi bincike sosai na gane tabbas aƙwai wanda ya ke naɗar duk wani sirrinmu yana kai masa,don a yanzu duk wani plan da muka haɗa masa yasan komai". "A'ah mlm daga ni sai kai muke wannan binciken,sai dai idan kai ne kake kai masa to sai ka faɗamin"?. "ah haba mutumina ta yaya za'ayi in haɗa kai da wannan mutumin?kar ka manta fa Damass shine ya yi sanadin mutuwar ƙanwata,shine ya sace ta ya tafi da ita ƙarshe ya kashe ta,duk dalilin taƙi aurensa,saboda munanan aikinsa,kuma ta yaya kake tunanin hakan daga waje na,no matter how hakan ta kasance,ni dai abu ɗaya zan faɗa maka shine aƙwai na kusa damu wanda ya keson ya san komai,sannan ya ruguza mana plan wanda muka daɗe da gama kayanmu". "hmm zan duba maganarka captain,amman gaskiya ina mamakin wannan waye kuwa"?. "Hmm Bilal kenan aishi makashinka yana tare da kai,don haka gwara ma kawai musan abinyi yanzu,kada mu tsaya kallon kifi kwaɗo ya yi mana ƙafa." bayan sun gama wannan maganar ne captain ya ke faɗa masa matarsa zata zo gidansa gobe. Bilal ya ce"ok Allah ya kawo ta lafiya".amin captain ya ce sannan suka cigaba da hirarsu. Sosai na ke kallon yaya Bilal wanda ke ta dariya kamar ba shi ba,ina kallonsa ta sama window ɗin ɗaki na,Ina ji araina dama dani yake wannan hirar,yau da har sadaka sai na yi saboda murna,amman kash!ba dani ya ke ba. Na saki labulen ɗakin na zauna abakin gadona ina tunanin irin wannan zaman dana ke,sai kace wani auren ƙwangila?ah to idan ma auren ƙwangila ne ai da sauƙi tunda dai ana kula da matar?amman ni ina nan dai zaune kamar wata gunki,ko kallon arziƙi ban taɓa samu daga wajen me gidan ba. **** Ƙarar wayar jidda ne ya karaɗe wajen,tana sama kan bene tana wanka,Bilal na kusa da wayar ya shiga kiranta da honey!honey!!amman jidda bata ma san yana yi ba,ya ɗaga wayar don ya bada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87