Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,254 words 0 views Progress saved
Download Book

Allah bashi da laifi tunda ba shine ya ce yana sonki ba,dole aka yi masa kinsan dai Hajiya kaka tana ji yanzu ko yana so ko baya sonki saiya aureki don yadda take matuƙar sonki aduk cikin jikokinta,don Allah Khairat ki cire Bilal a zuciyarki don ba alkhairi ba ne kinji?na fi son ki auri wanda zai kula da ke sosai ba wanda zai zakunce ki ba". kuka sosai na ke yi sannan na ɗago idanuwana da suka jiƙe jagab da hawaye na ce"ummu arman don Allah ki bani goyon auren Yaya na Bilal wallahi duk yadda ki ke tunanin irin son da na ke masa to duk ya wuce hakan,ina jinsa ne har cikin ƙoƙon xuciyata duk sanda zanyi numfashi to tabbas sai na tuna da Yaya Bilal,don Allah ki bani goyon baya duk gidannan babu wanda zan tunkara da wannan maganar idan ba ke ba,don Allah ki fuskanci yadda na ke ji don Allah".tana faɗar hakan ta ruƙo hannun Ummu Arman ta ɗora sai tin zuciyarta ta ce"Ummu Arman aduk sanda ki ka ji zuciyata tana irin wannan bugawar to tabbas Yaya Bilal na ke tunawa,na so in cire wannan mayen son da na ke masa amman abu ya ci tura,saboda da sonsa aka haifeni kuma har na girma dashi cire wannan son a zuciyata tamkar cire numfashi na ne".sai na rungume Ummu Arman na fashe da kuka mai tsananij gaske. rungume ni ta yi tana dukan baya na a hankali itama hawayen yana fitowa sosai acikin idanuwanta,tabbas tana matuƙar son Khairat don tun tana ƙaramarta ta ke sonta kuma tun tana ƙaramar Allah ya jarabce ta da son Yayan na ta,tana tausayawa yarinyar sosai yadda ya kamata saboda Khairat yarinya ce mai haƙuri,tabbas da za ta iya da tuni ta sakawa Bilal son Khairat don da ya ke mutuminta ne bayan wajen Kaka akaf gidannan babu ɓangaren da ya ke shiga ya yi hira idan ba sashenta ba,tasha yi masa nasiha akan yaso mai sonshi kanar khairat amman abu shiru kamar ma turasa ta ke yi wani lokacin,idan ta yi masa maganar Khairat ba zai sa ke shigowa sashenta ba,har sai ta je ɓangarensa ta basa haƙuri sannan komai zaiyi dai dai. Jikina babu ƙwari na koma ɓangarenmu don ƙwana biyu bana zuwa sashen Hajiya Kaka tunda munyi faɗa,ina shiga Hajiya Iklima da Anty Zeenat suka kalleni sheƙeƙe sannan Hajiya Iklima ta ce"ke zo nan tunda baki iya ganin mutane ki gaishesu ba". ina zuwa ta ɗaukeni tas da maruka har biyu sannan ta ce"na yi maganin mara kunya wuce ki bani waje da wata uwar baƙar fuskarki wacce uwarki inyamura tuban muzuru ta shafa miki". Sosai abin ya yi min zafi zuciyata tana ƙuna bansan sanda wani kuka mai ƙarfin gaske ya zomin ba,daman abokin kuka na ke nema don daman a cikin matsala na ke yanzu gashi kuma an to noni. Mama da ke ɗakin Abba tana gyara masa shimfiɗa ta jiyo ihuna ta fito da saurin gaske har tana tumtuɓe ta ce"ke Khairat lafiya me ya faru?". ban iya ba ta amsa ba da sauri na rungumeta ina shesshaƙa kamar zan haɗiye zuciya,ta gane me ya faru don haka bata ce komai ba taja hannuwa na muka koma ɗakinta. "Da mana ayi magana in zageki tsaf kema don daman akanki na ke son hucewa,da anyi magana sai miji ya ce Zulaiha! zulaiha!wai ita ga ta matar so,ko uban waye ba matar so ba oho". Anty Zeenatu ita ce ta tsakiyar da ya ke matan babana uku mama na ce Amarya sai kuwa ta ce"Hmm Iklima ai mu da sauƙi tunda asalinmu musulmaine munsha ruwan musulunci ita kuwa fa,tuban muzuru ne fa". ashe wannan ihun da na yi Hajiya Kaka ta ji alokacin Ƙasim ɗan Baba Auwalu zai kaita unguwa sai kuwa ta ce"kai Ƙasimu ni kukan wa na ke ji ne?". "gaskiya Kaka ki daina ce min Ƙasimu haka kawai da suna na Aqasim mai daɗi sai kuma a ɓata min,gaskiya a kiyaye?". "don ubanka ko Auwalu bai isa ya bani doka da order ba,don ba shine ya haifeni ba ni ce na haifesa,don haka ka ki yaye wallahi,ko inci uwarka mai ƙosan siyarwa,ni dai Ƴaƴana sun ɗebowa ruwan dafa kansu daga taimako sai kaga sun auresu ni kuma azo ana gasa ni,akan me ban hana aurensu ba sai kuma ni ace za a takuramin,to wallahi ni babu ruwana gaskiya tana zuwa zan faɗa sai dai mutane suji haushi". tuni har Ƙasim ya shige mota yana hango Kaka tana ta surutanta don shi bai ma san abinda ta ke ce wa,ya kalli jakar da tasa ka shi riƙewa wai ita daman cen idan zasu fita da mijinta kakansu shine ya ke riƙe mata jaka,duk da kasancewarsa soja baya jin kunya haka ya ke riƙewa,Ƙasim ya yi tsaki yana wani hararar Kaka. Har ta fara tafiya sai kuma ta ƙara jiyo sautin ihun da ya ke sashenmu ne akusa dana Kaka,don haka duk wasu abubuwan ana iya jiyo su. Da sauri ta yi sashenmu tana ce wa"wani mai son aci mar mutunci ne ya saka jikata kuka?".tana faɗar hakan tana shigowa farlon da ƙer don ya yi ɗan tsayi tudun farlonmu. Dukansu shiga taitayinsu sukayi suka haɗe fuska suna gaishe da Kaka amman ko kallonsu ba ta yi ba ta ce"waye ya saka Khairat kuka a cikinku?".sunkui da kai suka fara yi suna ƴan muzurai tare da sosai ƙeya don duk abinsu suna matuƙar jin tsoron Hajiya Kaka don aƙwaita da tonon asiri. "Ba daku na ke bane ku ke wani sunkui da kai kamar baƙin ɓarayi"?.da ƙer Anty Xeenatu ta ce"da man Hajiya Kaka Khairat ce ta yi wa Hajiya Iklima rashin kunya to shine". . . "shine me?". Babu wanda ya ce kanzil duk kawunansu a ƙasa,dai kuwa Kaka ta ƙwala ƙara tana ce wa"Zulai ke Xulai wai kina ina ne kizo ana son kashe miki ƴa". da sauri muka fito daga ni har Mama fuskata ta kumbura sosai ga marin Yaya Bilal ga kuma na Hajiya Iklima sai abin ya yi min yawa kumatun na wa suka kumbura sosai abin tausayi. "La ha ila ha illallahu muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam,Khairat me na ke gani a kuncinki kamar mari rututu haka?,ɓoye fuskar na yi ina muzurai don nasan tunda Kaka ta zo to tabbas ko wa sai ya taru agidan,don Kaka aƙwai son jikoki tun ma ba ni ba. Dukkansu tashi sukayi tsaye suna bawa Kaka haƙuri don sun san ko da basu ma tashi ba to yanzu zasu tashin don sai ta tara musu mutane. Ko kallonsu ba ta yi ba,tana ta faman girgixa ƙafafu alamar yau aƙwai masifa a gidan. Ko da Ƙasim ya gaji da jiran Hajiya Kaka sai ga shi ya biyota sashenmu ya tarar ana dirama,gurin zama kawai ya nema ya zauna don yasan wannan tsayuwar da kakar ta sa ta yi sai akai dare ana abu ɗaya,don kaka bata san ta yi abu ɗaya ta yi shiru ba. Tun ana abun tsakanin ɓangarenmu har ƴan sauran ɓangaren sashen suka fara tururuwar shugowa har ana ƴan rige rige. Umma ce kawai bata shigoba mahaifiyar Bilal don dawowarta daga makaranta kenan,don ita ce headmaster a makarantar ƴan matan da take. Kowa ya baza idanu ya ji abinda zai

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87