Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
Download Book

me ye amfanin auren."? "Khairat kenan ita fa wannan tsohuwar haka take ni wallahi har Allah Allah na dingayi mu taho saboda yadda tsohuwar nan ta sakani a gaba wai sau na auri yaya mohd,kuma ni wallahi na fi son har inyi jami'a kafin inyi aure." da fa kafaɗarta na yi sannan na ce"ki yi haƙuri don Allah Rashida akan wannan maganar ki cigaba da addu'a kinga dai yadda kaka ta dage yaya Mohd zaki aura shima kuma ya dage ke ya ke so,to kinga addu'a ita ce mafita don kinga duk su Baba da abinda kaka ta faɗa musu suke amfani don haka kawai sai dai ki yi haƙuri." "Khairat ni fa wallahi bana sonshi wallahi,ke kin sani idan yaya Mohd yana da ƙyau yana da kuɗi amman ni wallahi matsalar mahaifiyarsa ita ce kawai za ta takuramin ko da bayan anyi auran ne?. "Tabbas matar Baba tijjani tana da babbar matsala sosai don ko yaya sulaiman babban ɗanta daya auri ƴar gidan Baba Bashir haka ta takura mata zagin yau na gobe daban,don ma kaka tana ta ka mata burki da abin sai ya ɓaci sosai." "to kin gani khairat to a haka zan auri Yaya Mohd daman kuma duk ƴaƴanta ta fi sonshi sai kawai ace shi zan aura in auri masifa,Allah ni fa bazan aureshi ba gaskiyar magana".tana faɗar hakan ta tashi ta bar wajen. Na bita da kallo ita sonta ma ake ina ga kuma ni da ba son na wa ake ba shisshigina kawai na ke,yadda yaya Bilal ya tsane ni kamar mutuwarsa,ni kuma na nace sai shi,tabbas idan ban auri yaya Bilal ba to wallahi ni nasan ko da wani ya aure ni to gangar jikina ya aura don bazan taɓa sonsa ba zuciyata da komai na wa yana ga yaya Bilal,ina ma zai soni ko da bai kai yadda na ke sonshi ba,da ranar har azumi sai na yi saboda jin daɗin hakan. Mun fara exam ɗin second time wacce zamu tafi hutu sannan mu dawo zana jarrabawar waec da neco,muna ta karatu sosai ba mu da lokacin kanmu sam sai na karatu muna dawowa daga class zamu yi bitar haddarmu ayanzu muna izu hamsin da biyar baƙara ce kawai bamuyi ba itama kuma mun iyata. Rannan malamarmu bata da lafiya mai koya mana karatun qur'ani da asuba aka turo wai inzo zan ƙarawa wasu hadda,abin mamakin ko da nazo su sai naga ƴan ajin su Nadiya ne gabana yana ta faɗuwa na zauna har na ɗakko qur'anin sai na ji Nadiya na ce wa"Hmm wai arasa wacce za ta ƙara mana karatun sai wannan tuban muzurun har yanzu fa wasu daga dangin uwarta basu musulunta ba,adanginsu uwarta ce kawai ta fara musulunta sai manyan arna kakanninta suma suka musulunta kakanta fa babban fasto ne sai ace kuma wai ita ce za ta koya mana karatu?". wasu zafafan hawaye ne suka fara zubomin ba tare da na yi tunanin tare su ba saboda hawayen daman na ke son yi ɗin,dariya sosai suke min big girl oganniyar cikinsu ta ce"au shine kullum ake wani yawo da ƙaton hijab na munafunci?to yau sai mun buɗe hijab ɗin munga abinda ake ɓoye mana?. ban san ta zo kaina ta tsaya ba,ɗaga kan da zanyi naga big girl akaina tana neman ciremin hijabij jikina,da sauri na tashi na matsa lungu idona ya yi jawur ta ƙara matsowa tana ce wa,ai yau Khairat baki da wajen guduwa a hostel ɗinnan muradina na shekaru kusan biyar yau saina cika sa akanki." tana faɗar hakan ta riƙe hannun da na riƙe hijabin ta yi wa su Nadiya fito da sauri suka taho suka rirriƙeni ni kuwa sai kuka na ke ina ihu,wani wawan mari big girl ta yimin sannan ta ce"duk ihunki da wani fizge fizgenki yau wallahi sai na wulaƙanta ki a skull ɗinnan don daman haushinki na keji sosai na karɓemin saurayin da ki ka yi sir Kamil don haka yau sai na rabaki da abinda ki ke tutiya dashi. Sosai na ke kuka ina roƙonta da ta yi haƙuri amman sai naga kamar zugata na ke ita dasu Iman duk sun yayyaga min hijabina ya yi kaca kaca dashi bakina duk ya fashe saboda tsabar shan bugun da ya yi,amman har yanzu ban daina kukan ba,sunyi nasarar cire min hijabina na riƙe rigata sukayi sukayi duk yawansu su cire amman suka kasa wani ƙaton abu Nadiya ta ɗakko tana ce wa"tunda kin ƙi ta daɗi bari muyi miki mai gaba ki ɗaya. Saukar abu na ji akaina,nan da nan na fara ganin wani iri duk sun komamin bibbiyu,ana cikin haka wata secutyn skull ɗin tazo wucewa ta hango duk abinda ke faruwa da dauri ta kaɗa ƙararrawa sai ga duk securityn sun bayyana suka biyota cikin ajin don ganin abinda ke faruwa. Da sauri suka sakeni suna wani wiƙi wiƙi da idanuwa alamun rashin gaskiya,ai kuwa suka cafkesu alokacin ni tuni na yi suman wahala don ban san inda kaina ya ke ba,duk sun yayyaga min rigata,da sauri ɗaya daga cikinsu ta cire hijabin da ta saka ta rufemin sutura ta,don samana duk a buɗe ya ke har hawaye sai da matar ta yi don ba ƙaramin ba ta tausayi na yi ba. Daman sun daɗe suna jin labarin yaran da kuma ta'asar da sukeyi na lalata ƴaƴan mutane amman aka ƙi ɗauƙar mataki akansu ana tunanin sharri ake musu. A ruɗe Rashida da Hasiya suka fito daga Hostel ɗinmu,daman duk sun damu da rashin dawowa ta da wuri don har sunyi mana abincin karyawa amman ban dawo ba. Alokacin an fito dani kamar matacciya zuwa ƙaramin asibitin da ke cikin skull ɗin na mu,su kuma su Nadiya aka wuce dasu ɗakin hukumar makaranta.ɗalibai kowa ya yi cirko cirko masu saurin kuka sai yi suke. Rashida kuwa har bakin ƙofar da aka shiga dani ta shiga tana ta kuka tana ce wa"shikkenan sun kashe khairat wallahi nima bazan taɓa barinku ba nima sai na kashe ku".haka take ta maganar kamar ta ɓaɓɓaɓiya. Hukumar makaranta suka kirawo Abbanmu a waya daman duk shine ya sakamu a skull ɗin don haka hankalinsa a tashe yaje ya tashi yayansa ya ke faɗa masa anyi masa kiran gaggawa daga makarantarsu Khairat. Shima hankalinsa atashe suka fito a hanya suka haɗu da Baba tijjani da Baba Auwalu suka shaida musu abinda ya ke faruwa,suma ka sa tafiya aikin sukayi suka ce zasu bisu makarantar don suma hankalinsu duk a tashe ya ke. Bilal ya fito daga shi sai wandon aikinsa na sojoji da ƴar fal maram itama ta sojojin ce,sunyi masa ƙyau kayan kamar don shi aka yi su,saukarsa kenan awajen iyayen na sa duk yaji abinda ke faruwa don haka kai tsaye ya bisu ko ajje kayansa baiyi ba. Anyi min allurar bacci wani baccin wahala ya ɗaukeni,duk inda naji ciwo kuma an daka plasta an mannesa. Ko da su Nadiya sukayi ido huɗu da yaya Bilal au fitsari sai da sukayi ga shi belt ɗin jibga na jikinsa,ai kuwa ko da yaji abinda ya faru jijiyoyin kansa har wani tashi suke idanuwansa sunyi jawur kamar gauta. Baba Tijjani kuka kawai ya fashe dashi jin ƴaƴansa har guda uku acikin wannan mummanar rayuwar,Baba na ma da ya ke mai dauriyar

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87