Chapter 36
Chapter 36
faɗi hakan ina kallonta. Sosai mamaki ya game ƙwaƙwalwar Rashida ta ce"wai kina nufin baki san za'ayi aurenki nan da sati biyu masu zuwa ba?".Ta faɗi hakan tana kallona. Da sauri na tashi tsaye na ce"haba Rashida kada ki sanya zuciyata ta buga da waɗannan kalaman na ki maras tushe?Don Allah ki faɗamin abinda ke faruwa"?. Ɗan huras da numfashi ta yi sannan ta ce"hmm khairat nasan za kifi kowa farin ciki dajin wanda zaki aura,Yaya Bilak shine wanda zaki aura,har an kai kuɗi da komai tun wata uku da suka wuce".sosai na waro idanuwa duka waje na ce"Wai Rashida kin tabbatar abinda ki ke faɗamin gaskiya ne kuwa"?.Kallon banza ta yi min sannan ta ce"ai kin san na saba yi miki haka"?. Rasa tudun da fawa na yi na ce"lallai Rashida ni mai sa'ace kiga duk tsayin shekarun dana yi da dakon bawan Allahn nan azuciyata ashe nan kusa zan aureshi".na faɗi hakan ina rungume da filo a ƙirjina,Rashida ta ce"ah to kinga mune manyan ƙawaye kuma ƙannan miji ba?".Ta faɗi hakan tana kai min dukan tsokana. Sai dai tun yanzu na fara tunanin wani irin zama zamuyi da Yaya Bilal?Yadda ya tsaneni kamar mutuwarsa?lallai aƙwai babbar matsala a wannan rikitattan zaman na mu. Ranar dai na yi yinin jin daɗi,Rashida ta ce"baki tambayeni mutuniyarki Nadiya ba"?.murmushi na yi sannan na ce"hmm Rashida ni fa yanzu gwara inyi nesa dasu don zama dasu ba alkhairi ne arayuwa ba,kina ganin dai halin dana fa ɗa saboda su,ni tunani na ma kada Yaya Bilal ya zargeni akan hakan kinga bazai taɓa ganina da mutunci ba".?Na faɗi hakan kamar zanyi kuka. Cikin tausayina Rashida ta da fa kafaɗa ta sannan ta ce"Khairat kada ki yi wannan tunanin,ba kowani tunani ɗan adam ya ke sakawa a zuciyarsa ba,saboda kada wataran ya rasa tunanin mw zai yi,don shima tunanin da na shi lokacin,kuma yana da kyau ki kyautata kyakkyawan zato a karan kanki,kada ki yadda da duk abinda mutane zasu faɗa akanki,ke dai tunda kin yadda da kanki shikkenan,sauran ki barwa Allah zai miki sakayya da gaggawa." Goge hawayen fuska ta na yi sannan ce"Hmm Rashida wannan ƙazafin da aka yimin ya kasa gogewa acikin zuciyata,sunyi min illar da bazan taɓa warkewa ba,sun cutar min rayuwata,sun wargazamin farin cikina,ina rayuwa da mahaifiyata da ƴan uwana cikin aminci da kuma ƙaunar juna,amman yau duk ina wannan Rashida?Ya tafi har abada bazai dawo ba".Na faɗi hakan ƙwalla na fitowa daga cikin idanuwa na. Sosai Rashida ke bani baki sannan ta ce"kibar komai ba komai ba,insha Allah muna nan zaune zakiga sakamakonsu,insha'Allah khairat ba zaki taɓa taɓewa ba,komai ya yi farko yana da ƙarshi,yanzu bikinku tare za'a haɗa dana yayyin ki biyu". Tuni na fito da idanuwa na waje na ce"ikon Allah da kuma su waye?".Dariya Rashida ta yi sannan ta ce"hmm buɗe dai kunnenki sosai kiji,Yaya Salim da Mero,Yaya Aliyu da Maryam".har dafe ƙirjina na yi sannan na ce"oh ni wannan aure aƙwai rikici to shi Yaya Salim daman yana son mero ne?".Dariya Rashida ta yi sannan ta ce"ina a'i wannan duk haɗin tsohuwa Hajiya kaka ne". sosai na ke dariya sannan na ce"caɓɓi lallai Yaya Salim har kuka sai ya yi,saboda shi arayuwarsa yana son mace ƴar boko,to yaya kenan?tunda i'ta dai mero ko aji ɗaya bata taɓa shiga na boko ba". Nan dai muka cigaba da hirarmu har ta rakoni waje,ta ce"khairat amman na yi mamaki da bro Aliyu bai gaya miki zancen aurensa ba"?.Dariya na yi sannan na ce Hmm wata ƙila baya son asani ne?kin san halin matarsa,ni fa wallahi ya ƙara ɗin ma saboda Anty khadina sai a hankali wallahi,ni ɗinma ɗaga mata ƙafa kawai na ke saboda matsayinta na matar yaya na,saboda san bata iya magana ba". Rashida ta buɗe baki za ta yi magana sai ga Yaya Aliyu mijinta da Nadiya ta wani hakimce agaban mota.sosai na yi mamakin ganin hakan na kalli Rashida na ce"ikon Allah sai kallo su kuma yaushe suka zama masoya har haka?". dariya Rashida ta yi sannan ta ce"haba Khairat kamar baki san Mama iklima bane?sun neme sa ne kuma yanzu gashi sun samu,ni dai Allah na saka agabana kullum goshi na yana ƙasa ina roƙar Allah ya fiddani daga zaluncinsu ya bani haƙurin jure duk wani cin kashinta,da i'ta da Yaya Aliyun". suna ƙaraso wa muka gaisa da Yaya Aliyu ya amsa da fara'arsa muna cikin gaisawa Nadiya ta ce"honey zo mu tafi jiri na keji bana son tsayawa".A'i da sauri naga Yaya Aliyu ya bita suka yi saman bene. Har suka hau ban daina kallonsu ba na juyo na ce"Rashida Alkah ya baki haƙurin jure komai, ya ƙwato miki mijinki a hannunki". Muka yi sallama akan za tazo waje na awannan satin,abin mamaki ina fitowa daga gidansu Rashida naga wannan motar a ƙofar gidan,na buga wani uban tsaki kusan awata huɗu amman suna zaman jiran gawon shanu. Hanyar titi na yi ko waiwayonsu banyi ba,har na tsayae da keke napep kawai sai naga wannan mutumin ya fito yaje wajen me keken ya nuna masa wani kati,ai da gudu mutumin ya tafi,ni kuwa haushi duk ya kama ni,na gallawa mutumin harara wani a mummurɗe dashi,na ce"wai don Allah bawan Allah sata na yi muku kome?kun dameni sai bina kuke?". Murtuke fuska ya yi sannan ya buɗe baki zai yi magana,aka buɗe murfin motar,sosai na buɗe idanuwa na ina kallon wanda ya fito daga cikin motar ƴar pos ɗin dake hannuna ta faɗi a ƙasa. *Miss green ce* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 Badi'at Ibrahim _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 Instagram links👇 https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY= Facbook group https://facebook.com/groups/463653111781414/ Telegram links https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *A C Ƙ* MISS GREEN *39⬜40* . . . .ban gama mamakin ba sai da ya matso har kusa dani sannan na buɗe baki na a hankali na ce"daman kai ne"?.Murmushi ya yi har fararan haƙoransa suka buɗe sannan ya ce"Eh ni ne duk da ni ban taɓa ganinki ba?Amman nasan ke ko da a tv kin taɓa ganina,zan gabatar miki da kai na duk da nasan kin san sunan nawa,Ahmad A.Abubakar,commisioner of police bani da aure ayanxu amman ina da niyyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87