Skip to content

Chapter 86

Chapter 86

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,286 words 0 views Progress saved
Download Book

sauri ya ce"Dady yanzu ta daina xaginmu kuma tana sonka".? Da sauri uban ya ce"ƙwarai yanzu duk tana sonmu daman cen tana sonku,kawai dai koya min darasi ta yi." Irfan ya rungumeni sannan ya ce"ilove u my momy".da sauri nima na rungumesa na ce"ilove u too my son".na haɗa ƴaƴa dukansu na rungume,da sauri Bilal ya ce"a'ah ina little khairat ne"?.murmushi na yi sannan na ce"ah ai kasan tana wajen mutuniyarta hajiya kaka". Ranar da daddare har shopping muka je cikin so da kulawar juna. ****** *after three month* sosai na ke shan gyara yadda ya kamata,little khairat na da wata goma har ta fara tafiya ta yi kyaunta sosai,ga ta ƴar lukuta ga tsayi don tayo tsayin mahaifinta. A wannan karon ma Ahmad commissioner of police baiyi sa'a ba,don tuni Yaya Aliyu ya shaida masa an mayar da aurenmu da yaya Bilal ya kuma gaya masa maƙasudin saki na da miji na ya yi.saboda tausayin yaya Bilal da yaji don kada ya rasa rayuwarsa. Yaya Bilal ya danƙara wani gida me kyau da tsari part uku ne agidan wau harda part ɗin yaransa.ɗaya kuma ni dashi ɗaya kuma na baƙi. Sosai aka kashe kuɗi wajen yin kayan ɗaki don Yaya Bilal da kansa ya yimin komai hatta kayan kitchen duk shi ya yi,ya gyara sashen yaransa ya yi mugun kyau da tsari. Da yamma aka rakoni tariya kusan ƴan gidanmu duk sunxo,aka dinga yi mana fatan alkhairi,Hajiya kaka ta rungumeni tana ce wa"Allah sarki khairat insha Allah yanzu zaku zauna zama na har abadan,babu wani tsautsayi da zai gifta muku insha Allah".nima a hankali na buɗe bakina na ce"kaka babu abinda zai rabani da yaya Bilal sai mutuwa mutuwar ma da tana ɗaukar mutum biyu da sai na ce ta ɗaukemu tare." Nan aka tintsire da dariya gwanin sha'awa,Rashida ma sai dariya take itama yanzu tana nan ɗauke da cikinta Wata biyar,yanzu kuma shekararta shida da aure,sai yanzu Allah ya kawo,maryam kuwa har mun saka mata suna uwar haihuwa don yanzu ma tana nan da cikinta har wata baƙwai.tana arba'in ta samu wani. Dare ya yi sai ni kaɗai da yara na,na shiga wanka na fito naji suna oyoyo dady,ita kuma Little khairat ta yi barci.daman ita da wuri take bacci Allah Allah na ke in ga yaya Bilal yau tun safe ban gansa ba. Ta baya na shigo don haka banji shigowarsa ba sai kawai naji ya rungumeni ya ya yi sama dani ya ajjeni akan gado,ya koma farlo ya kunna musu catoon ya kukkule ko ina na gidan,sai masu gadi sojoji har guda biyar sannan ya dawo ɗakin. Na rufe hannaye na da tafukan hannuna kunya duk ta kamani daga ni sai tawul,murmushi ya yi ya faɗa wanka banɗaki sannan ya fito yana goge ƙwantaccen gashinsa,wanda yanzu ya ƙara kyau da tsantsi. Ya saka jallabiyarsa sannan ya kalleni ya ce"mamynmu taso muyi sallah mu godewa Allah"murmushi kawai na yi don da haka ya ke kira na,wato mamynmu yadda yara na ke kirana. Cikin jin kunyarsa na tashi na shiga ban ɗaki na saka rigar bacci me kyau sosai,ruwan pink wacce ta amshi fatata don ayanzu zama a iya kirana da fara,saboda yadda fatar tawa ta ƙara samun cigaba yadda take shan gyara sosai. Bayan mun idar da sallah mukayi addu'o'i muka shafa ya ɗakko fresh milk da wata banƙararriyar kaza wacce girmanta ma kaɗai da maiƙonta zaisa kaci.sosai naci nasha madarar itama shima yasha daman yanzu na ya little khairat don da kanta ta ya ye kanta,sabawar da aka yi mata da madara,kuma yanzu kununta take sha mai matuƙar ƙarawa yaro lafiya. Baki ɗaya ya ɗaukeni yana yawo dani kamar a indian film.Hmm ranar fa an yi ƙwanan farin ciki da ƙaunar juna tsakanin khairat da yayan nata Bilal uban ƴaƴanta. Bayan wasu watanni,ayanzu yaya Bilal ya yi nasarar kama Alhaji Damas biyo bayan tonuwar asirinsa na ayuukan da ya ke yi,sannan su kansu manyan ƙasa sunyi amunna da hakan don suma abin ya shafi yaransu don Alhaji Damas ya ɓata musu yara da basu hodar iblis,ƙarshe har ta yi sanadin kashe ɗan gidan wani babban commisioner,ai kuwa ana kaishi kotu aka yanke masa zaman gidan yari na har abadan.sai dai ya mutu acen biyo bayan laifukan da ya yi wanda ba zai yiwu ya fito ba. Har yaransa duk an kamasu,har da waɗanda aka kamasu sun kashe wan babban ɗan siyasa kuma shi Damas ɗin ne ya aikasu,ai kuwa ganin hakan ƴan duk yawancin ƴan siyasa suka saka hannu akan kama Damas ɗin saboda ɗauki ɗai ɗai ɗin daya fara yi musu. Ɗan damas kuwa tuni Aka harbesa a karan battar dasu Bilal suka kai gidzn Daamas ɗin sai dai muce Allah yajiƙan,duk wanda ya mutu.iyayen jidda kuwa har yanzu Bilal bai fasa taimaka musu ba,don ko ba su ba daman shi mutun ne mai tausayi sosai. ********* bayan shekara goma. Wata hamshaƙiyar mata na hango tana zaune a babban farlonta,ɗauke da ƙaton cikinta haihuwa ko yau ko gobe.dana duba sai na hango muku ashe khairat ɗin hajiya kaka ce.ta ƙara kyau da cika. Wani saurayi ne ya shigo wanda bazai wuce shekara sha shida ba,Kyakkyawan gaske me kama da Bilal,ashe irfan ne sai yanzu aka gane ashe duk yafi kama da mahaifinsa,ya zauna kusa da mamansa ya kalli ƙafarta ganin yadda ta kumbura cikin tsananin tausayinta ya tsugunna yana danna mata ƙafar.musmushi khairat ta yi ta shafa kansa ta ce"Allah ya yi muku albarka baki ɗayanku son."da amin ya amsa mata don shi miskilin gaske ne har yafi babansa ma. Da gudu wata yarinya ta taho me kama da khairat sak,kuma itama ba fara bace kamar su irfan.sai ga Haidar nan ya fito,ya zama ƙato ɗan lukuti shi daman ɗan lukutine,ba kamar su irfan ba. Ya fara magana cikin haushi ya ce"wallahi da kin tsaya da na zane ki mara kunya,ni sa'anki ne"?.da sauri na kallesa na tambayi ba'asi nan ya ke faɗamin wai wayarsa ya saka chaji shine ta zuba masa ruwa akai. Haƙuri na basa,sai ga wata kyakkyawar budurwa itama ta shigo iman kenan wacce har ta fara cika budurwa.sanye take cikin kayan islamiyya ta ƙarasa wajen mahaifiyarta ta ce"Mamynmu na tafi islamiyya".murmushi na yi sannan na ce"to iman kada ki manta ki biya ta wajen Anty halisa ki amsomin saƙon nan".murmushi ta yi sannan ta wuce. Ayanxu ƴaƴan khairat 8 ne ga cikin na 9.bayan ƴan huɗu sai Little khairat wacce yanzu ke masar ta koma wajen mahaifinta tun tuni,don tun tana shekara biyar ya ɗauketa.da ƙer aka samu shahid ya yi aure ya auri wata balarabiya mace me kirki kuwa don tare suke zuwarmin da little khairat.amman har yanzu Allah bai basu haihuwa ba.shiyasa ya ke masifar son little khairat. Bayan little khairat ta haifi twins,Maryam da Hafiz amman ana kiransu Maher da Amira.sai kuma ƙaramarsu me kama da khairat sak itace sarkin ɓarna. Sai na tara yanzu zata haifa,babban ɗan gidan captain Khalil wato ibrahim wanda yanzu ya ke da shekara ishirin da huɗu shine ke son iman,don ya dage sosai shi khairat ya keso,kuma alhmdh yarone me hankali yana da nutsuwa kuma yana da aikin yi.don yanzu har mahaifinsa ya samo masa aiki a babban asibiti lilitan mata wato ghanychology. Ina zaune naji jiniyar mota ta tsaya,irfan da ke

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87