Chapter 30
Chapter 30
kin ɗora mata lalurar dole?to wallahi sai na kashe ki na kashe banza". Amira ce da ta shigo ɗakin yanzu taji abinda ke faruwa ta sheƙa da gudu tana kiran mutane,sosai ɗakin ya cika da mutane kun san gidan yawa ɗuuu kowa ya shigo.wanda bai san abinda ya faru bama yanzu ya sani,hajiya kaka ma ta shigo don tana cen tana kukan abinda ya faru,mero ma ganin kakan tana kuka ita ma sai ta hau kukan sai yanzu ne da suka jiyo ihu suka firfito har mero. Da ƙer aka cire hannun mama daga wuyan hajiya iklima ta haɗa wata uwar zufa sosai,kamar wadda ta yi babban yaƙi,hannunta na kan wuyanta tana murzawa ta samu waje ta zauna a bakin gadonta,tana tarin wahala. Sosai hankalin kowa ya tashi da jin duk abubuwan da suka faru,wasun su sun yadda wasu kuma basu yadda ba,hajiya kaka tana kuka ta ce"kai gaskiya zulaiha inyamurai sunyi asara da suka haifo ki a matsayin ƴarsu,yanzu kuma bayan hanyar da ki ka saka ƴarki shine ki ka biyo kishiyarki har ɗaki zaki kashe ta?ah to wallahi ba agidan nan za'ayi kisan kai ba,zo ki fita cen garinku na ƴan obwa musho,kije cen ki yi,idan kinga da ma-ma ki shiga boko haram ko kuma ƴar kidnapping amman mu ba'a nan ba". Tana faɗar haka taja ƙeyar mama har ɗakinta tana tsaye ta ɗibi kayanta ta fito,sai dai me?sai ga yaya Aliyu ya shigo kallon mama sosai ya yi,sannan ya kalli hajiya kaka wacce fici-ficin idanuwanta suka kuma komawa ciki sosai,alamar rashin mutunci take ji ko kallon Aliyu ɗin ma bata yi ba. "Mama lafiya me ya faru?ya na ganki da aƙwati kuma?" Duk alokaci ɗaya ya jerowa mahaifiyar tasa tambayar,mama ta kallesa cikin tausayinsu sannan ta ce"Aliyu yau zamana agidanku ya ƙare,zan tafi da kewarku amman ga ƙanwarku nan,i'ta kaɗai ce mace acikinku don Allah ku kulamin da i'ta kamar ina nan?ga ƙaninku da ke makarantar ƙwana shima ku kulamin dashi don Allah". Kasa gane maganar mahaifiyar tasa ya yi,kansa ya yi masa nauyi sosai harshensa ya kasa furta komau har maman ta fita baki ɗaya daga cikin gidan,da sauri yabi mahaifiyar tasa,gudu ya ke sosai a motar sai dai yana zuwa titi yaga ta hau mota,da sauri yabi motar hankalinsa duk a tashe. A babbar tasha aka ajje ta,tana fitowa taga Aliyu ya biyota,ta gyara zaman mayafinta sannan ta ce"Aliyu yanzu sai da ka biyoni?da ka zauna kusa da ƙanwarka ka lallashe ta,don a yanzu tana buƙatar mai taimakonta akusa da ita,wanda zai share mata hawayenta bayan rashinta. "Mama wai me ya faru da khairat ɗin?wani abu ne ya faru da i'ta?". ɗan murmushi mama ta yi wanda ake ce wa yafi kuka ciwo,babu abinda ta ɓoye mishi tun farko har izuwa yanzu. I'danuwansa suka yi jawur alamar zuciyar Ali gadanga ta motsa bakinsa ya yi masa nauyi sosai,ya ma rasa wani irin mataki zai ɗauka akansu mama iklima?ko da kashesu ya yi ba zai daina jin baƙin cikin ɓatawa ƙanwarsa suna da aka yi ba,ƙanwarsa da ya ke so ya ke ƙauna fiye da kansa?don yana matuƙar jin tausayinta tunda i'ta kaɗai ce mace acikinsu. [03/09, 20:31] Ummu Maher(Miss Green): "Aliyu ba na faɗa maka bane don ka ɗauko mataki,a'a na faɗa maka ne don ka kula da ƙanwarka,kana da gida Allah ya hore maka don haka ka kai khairat gidanka,ban yarda daga yau ta ƙara ƙwana acikin gidan nan ba,saboda nasan abinda zai biyo baya,mahaifinku mutun ne mai matuƙae zuciya musamman idan abu ya fice masa aransa,don haka ka kula,kada ka ce don mun rabu wai zakajo haushinsa,a'a mahaifinka ne kuma shima yana da haƙƙi mai girma akanka don haka a ƙarshe ina ƙara jadda da maka ka kula da ƙannenka kai ne babba don Allah". Cikin kuka ya riƙe hannun mahaifiyar ta su sannan ya ce"haƙiƙa na yi baƙin cikin rabuwa da ke mamana,mahaifiya ta gari,mai son cigaban ƴaƴanta ako da yaushe,aduk inda ki ke ba zanyi ƙasa a guiwa wajen zuwa ba,insha Allag zaki sameni a mai yi miki biyayya ko da bakya nan." Sai ya ƙwantar da kansa a hannun mahaifiyar tasa abin tausayi,ako da yaushe idan ya shugo gidansu idan mahaifiyarsa bata nan sai yaji gidan tamkar kango ne,tafiyar wuni kenan?ina ga kuma tafiyar da mutum zai yi baki ɗaya izuwa wani gari na daban?.a dai dai nan Aliyu ya ƙara fashewa da wani irin kuka mai ciwo,tabbas uwa garkuwa ce a wajen ƴaƴanta,uwa ita ce tushen al'umma. Anan na ke janyo hankalinku ƴan uwa na,muso iyayenmu so na haƙiƙa ba wai son ƙarya ba,musamman ma uwa,uwa ita ce mau tattalin ƴaƴanta da son farin cikinsu a ko da yaushe,uwa ta ƙwammace da taci abinci bata bawa ɗanta ba gwara ta bawa ɗan yaci i'ta ta zauna a haka. Wa'iya zubillahi!a wannan lokacin namu na yanzu wasu sun mayar da iyayensu tamkar bayinsu,sun ƙwammace su farantawa ƴaƴansu da matayensu akansu,tabbas duk mutumin da bai gama da iyayensa lafiya ba,to wallahi ya yi asarar zaman duniya da kuma na lahira,Allah ya tsaremu aminya bamu damar gamawa dasy lafiya,waɗanda iyayensu suka rasu Allah yajiƙansu amin. [03/09, 20:40] Ummu Maher(Miss Green): Kuɗi sosai yaya Aliyu ya ciro a acc ɗinsa ya bawa mahaifiyarsa,yana tsaye har motarsu ta tashi sai Benin,asalin garin iyayen mamanmu. goge hawayen fuskarsa ya yi yana jin wani irin zafi acikin zuciyarsa. *** aranar na bar gidanmu tafiyar da ban taɓa tunanin zanyi irinta ba,ga shi mahaifiyata sanda ta tafi ban sani ba,na yi kuka har na gaji zan shiga sashen hajiya kaka don yi mata sallama,yaya Aliyu ya riƙe hannuwa na yana girgiza min kai alamar a'ah. Ina ji ina gani na shiga motar muka tafi,kewar mahaifiyat dana gidanmu suka taru suka yi min yawa,haƙiƙa bawa baya taɓa tsalla ke wa ƙaddararsa,Allah ya bamu ikon cinye dukkanin ƙaddarorinmu. Yaya Aliyu sai tarairaya ta ya ke tun acikin mota,ni kuwa sai kallonsa na ke ina kuma tausayinsa don nasan dannewa kawai ya ke don ya farantamin amman hankalinsa duk atashe ya ke,fiye da na wa nima. Muna isa gidan da kansa ya fitomin da kayana har cikin gidan na kallesa na yi murmushi idanuwa na da ƙer na ke ganinsu saboda kukan dana sha. "A.ah don Allah ku tsaya anan!ina zaka jemin da wannan gantalalliyar ƙanwar ta ka?". *miss green ce* [23/09, 16:19] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI* ummu maher(Miss green)🍀🍏 *sirrinmu* rarrashin mai gida ya yin fushi😃💋🤝 *haba mijina abin alfaharina,haƘiƘa fushinka agareni kanar garwashin huta ne,ka taimaka ka yafemin ko da zan samu sassauci,Allah yabarmu tare my hubby,sai ki shafa hannayensa a hankali* Wallahi ko shaiƊan ne shi sai ya sakko😃😒 *By miss green dr mata😃* 31🟨32 . . . ."haba wannan abu har ina?ƙanwar ka ta yi cikin shege har ta yi Ɓari,shine ni yanzu za a wani kawo min i'ta gida na?a to wallahi ku koma inda kuka fito amman wallahi ni dai ba dani ba". "Ke ce dai zaki bar min gida na,kuma idan naji kin Ƙara zagin Ƙanwata da mummunar kalma wallahi sai kin Ƙwammace baki zage ta ba,ya janyo hannuwa muka shiga gidan. kallonsa kawai take yi da mamaki don da zasu shiga na har bugeta ya yi,hankali na duk a tashe ya ke,wato kowa yasan abinda ya faru kenan?i'ta da take nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87