Chapter 71
Chapter 71
na ce"Allah ka matso inda na ke Allah ya isa ban yafe ba".da sauri ya matsa gefe ya ce"khairat ni ki kewa Allah ya isa"?.da sauri na ɗaga masa kaina alamar eh dashi na ke. Bai ƙara magana ba ya fita fuuu kamar kububuwa ni kuwa azuciyata na ce.tafi nono fari daman ni haka na keso. ****** Madarar daya siyo ya aiko da ita,ina haɗa musu da ita yara suka yi manya dasu tubarkalla. Tunda Baba na yasan auren mama ya mutu,sai yaƙi yarda ta koma Garinsu ya dinga aiko mata mutane akan ta yi haƙuri ta komawa gidanshi,sai da ƙer ta yadda sai da muka taru dukkanmu har da maher ƙaraminmu,muka saka mata kuka tausayinmu yasa ta aminci. Aka mayar da aurensu,tuni aka ƙara gyara ɓangarenmu aka ƙara fitarwa da mama babban farlo da ƙurya biyu.ya yi kyau sosai su mama iklima kuwa rayuwa ta garasu inda ayanzu duk sunyi aure,sai dai duk ranar da yaransu suka je wajensu to fa da kuka suke dawowa,har tausayi suke bani. Nadiya ma aure ya mutu ta dawo gida,don Yaya Aliyu ya gano har yanzu bata daina lesbian ba,ai kuwa ya sake ta saki ɗaya.tuni ta lalace ra rame sosai yanzu idan ka ganta sai ta baka tausayi. Nadiya me izza da ƙwalisa da rashin kunya,amman yanzu duk babu wannan har ɗakina take zuwa musha hira don tuni ta nemi yafiyarmu nida mama tana kuka. Rashida ce yanzu agidan,har yanzu bayan ɓarin da ta yi bata sake samun ciki ba,Maryam ma dai haka don ita kamar da matsalar jinnu ma.amman dai an dage da magani. *After 2 years* A kullum Bilal hankalinsa na kan Khairat duk zuwan da zaiyi da magiya da naci,don sai ya ɓuge da ɗibarsu haidar wai duk don in dawo masa amman ko kallon ƙurarsa bana yi. Shi kuwa Ahmad commisioner of police ya yi naci har ya gaji na ce bazan auresa ko don matarsa Xuhra,don tun da na haihu bata zo ba,kuma ko a skull yanzu ta daina kulani tunda ya bata labarin ni tsohuwar budurwarsa ce,shikkenan ta ƙaurace min ko aji bata shiga duk inda tasan ina nan.sosai abin ya bani mamaki sai dai ba abin mamaki bane don daman kushinmu na mata ya gaji haka. Saboda ire iren wannan ma na ce bazan auresa ba,to shima ɗin dai bai haƙura ba,yana nan yana naci amman naƙi bada fuska. Ƴan huɗu fa sunyi girma ga baki chaƙwai2 sun san mahaifinsu sosai,don idan yazo nigeria har ya tafi suna wajensa. Rannan na shirya zuwa gidan Anty Halisa.na saka wata doguwar riga ta atamfa ta amshe ni sosai matuƙa don yadda yanzu na ke na zama babbar mace sosai,komai zan zan babu namiji da zai kalleni ya share fatata ta yi luwai luwai. Ina fitowa na buɗe sabuwar motar da Babanmu ya siyomin zan shiga,sai ga shinan ya fito da ƴan huɗu,ganin zan fita yasa suka runtumo da gudu zasu bini,ganin haka yasa ni kuma na figi motata fuuuuuuuu..... .✍🏿 07068606171 *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 _*Miss green ce*_🤙🏿 [23/09, 16:29] Miss Green🍀: 87. . . . . . .88 . . . .sosai abin ya bawa Bilal mamaki wato har ƴaƴanta ma bata barsu ba,ka dinga ƙin ƴaƴanka saboda kana ƙin mahaifinsu,shi kuwa zai ga ƙarshen rashin kunyarta don xai yi maganinta. Wani super market na fara sauka me mugun kyau da tsari,na shiga na wuce ɓangarensu biskit da halawa na fara siya saboda yaran anty Halisa,ina cikin siya sai naji kamar ana kallo na na tsargu na juyo.wani kyakkyawan saurayi na gani kusa dani wanda yafi kama da balarabe don wannan ko kusa bai yi kama da hausawa ba. Saurin janye idanuwa na na yi daga garesa don kada ya gane ina kallonsa,murmushi ya yi ya iso kusa dani na juya masa baya na cigaba da siyayyata,naga wata alawa dasu Haidar keso na saka hannu xan ɗauka,shima ya saka nashi hannun da kallon kallo muka shigayo ni da shi.naji gabana yana faɗuwa sosai na yi saurin sunkuyar da kaina ƙasa. Cikin harshen turanci ya ce"ya ke ma'a bociyar ƙwarjini da kuma ƙuruciya,zanso ki bani dama in taya ki siyayyar."sosai kalamansa suka daki zuciyata sam bana son ƙara fuskantar wata rayuwa dana miji,sai inga kanar bani da sa'ar wannan. Babu yadda zanyi don mutum ne shi me mugun naci don haka na biyesa ma dai har na gama siyayyar.muka jera atare yana ta kallona sosai kamar zai haɗiye ni,ni wannan mugun kyaun nasa ne ma ya ke bani mamaki kamar ba mutum ba,i'na zuwa wajen biyan kuɗi na ciro atm card ɗina na miƙa shima sai ya miƙa hannu. Ya basu nashi ya ce su ciri kuɗi ko nawa ne a abinda na siya.kallonsa kawai na ke ina mamakinsa,ya kannemin ido ɗaya yadda yaya Bilal ke yimin.tuni naji gabana yana faɗuwa tun farkon fara kallonsa dana yi. Da sauri na fito daga cikin wajen don bana son ya ƙara takuramin kuma.don ni wannan ma tsoro ya ke bani,murmushi ya yi ganin na fita sosai yaji mugun sonta na ratsa duk jikinsa ayanzu yana da shekara 29 aduniya,amman bai taɓa jin yana son wata ƴa mace ba sai yanzu gata baƙa kuma ba wata kyakkyawa ba amman sai yaji ta yi bala'in ƙwanta masa. Da sauri ya riƙe hannun motar tawa ya ce"haba rayuwa ina kuma ki ke son zuwa ki gudu ki barni?idan ki ka tafi ina zan ƙara ganinki".?da sauri na zaro idona ina kallonsa,cikin tsoro na ce"Don Allah bawan Allah ka yi haƙuri ka kyaleni in tafi,na gode sosai da kuɗin da ka biyamin." na faɗi hakan cikin tsoro don tsakani fa Allah ni tsoro ma ya bani.zama ya yi agaban motar tawa sannan ya ce"Ni sunana Shahid ni ba ɗan nan ƙasar bane,ni ɗan ƙasar masar ne uba na bature ne shi ɗan asalin england ne,mama na kuma masar kuma a masar ɗin aka haifeni,munzo nan gari ne ni da mamana wajen buɗe wani campany ɗina,mahaifina ya rasu tun ina shekara biyar,to yana da hannun jari sosai a ƙasashen waje ciki harda ƙasarku nigeria,to shine yanzu na buɗe wasu company a ƙasar nan,kuma ina jin daɗin zaman ƙasar ashe zan haɗu da rayuwata a garin?". "Don Allah ki faɗamin sunanki don Allah,wallahi tun ganin farko dana yi miki naji kin masifar ƙwantamin don Allah ki yadda ki soni kamar yadda na kesonki please,Ammina za taji daɗin hakan sosai tun kafin in kai yanzu take son inyi aure wai saboda mu ƙara ahali,tasha haɗani da ƴaƴan ƴan uwanta amman haɗin bayz yiwuwa saboda sam basu ƙwantamin ba,amman ke kallon farko ki ka tafi.da rayuwata." Da ƙer na buɗe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87