Chapter 84
Chapter 84
faɗuwa tunowa da shahid.don nasan duk wannan abinda na yi yasan komai,na tashi na fita ina kallon yaya Bilal. Ina fitowa na fara bin bango ina tafiya ina cije leɓe,duk jikina ya yi mugun yin tsami,ga haihuwar dana yi wacce ta bani wahala sosai. Da sauri shahid ya taso ganin ina shirin faɗuwa,kome ya tuna sai ya yi sauri ya yu baya zuciyarsa sam babu daɗi ko kaɗan. Abinda ya ƙara bani mamaki bai wuce yadda duk sanda shahid ya kalleni sai inga yana hawaye.abin fa ya taru ya yimin yawa na rasa inda zan saka kai na inji daɗi.gashi kowa na gidanmu bai sakarmin fuska tuni nima na fara wani irin ciwon kai me zafi,sai little khairat ta fara shiga wani hali ma don ko wajen shayarwa an tauye yarinyar.da ya ke babanta na da kuɗi tuni ya samo mata ingantacciyar madara wacce ake bata tana sha.ta yi mul mul abinta gwanin sha'awa. ********* an sallame ni yanzu amman abin mamaki shahid gidanmu ya kai ni,sai duk kaina ya ɗaure,mutumin da ya ke cewa matuƙar na sauka lafiya babu inda zaije yana kusa dani,kullum yana zuwa ya ganni kuma koda yaushe da mahaifiyarsa suke zuwa.sosai suka kawo kayan barka na gani na faɗa,tare da turo kuɗi me yawan gaske wai asai wa yarinya hakika,babanmu ya turowa kuɗin don haka aka siya komai yadda ya kamata. Har yanzu bai faɗawa khairat ce wa ya sake ta ba,ya bari ta yu tsarki tukunna,bai fasa kira na awaya ba,kullum zai kira sau uku har sau huɗu ya tambayeni lafiya ta. Ni na rasa gane kan shahid don haka na saka azuciyata indai yazo zan tambayesa don inji ba'asin abinda ya faru. ********* *40 days* bayan ƙwana arba'in yau na ke cika ƙwana arba'in cas da haihuwata,yanzu dai jiki na ya yi sauƙi don ina samum kulawa daga wajen mahaifiyata,kuma yanzu ƴan gidanmu sun rage haɗemin fuska har da Hajiya kaka ma,kullum da kanta take yimin girki me rai da lafiya ta kawomin,don sun tausayamin sosai da halin rashin lafiyar dana shiga. Yaya Bilal dai shima yanzu ya samu sauƙi da taimakon Allah da taimakon shahid don da kansa ya dinga teatment ɗinsa jikinsa ya yi sauƙi sosai.sai dai fa Yaya Bilal ɗim dana sani ada cen baya to yanzu ba shi bane,don ko da mukaje dubasa ko kallo na bai yi ba,balle in saka ran xai ko kalleni. Abin ya dameni sosai da sosai,har gida shahid yazo ya samu iyayena su duka ya faɗa musu abinda ya yi,sosai suka yi mamakin abinda ya faru shahid ya ƙara da faɗin"kuyi haƙuri nasan zakuga zafi na sosai amman aƙwai hikima acikin abinda na yi,ban saki khairat don bana sonta ko ƙaunarta ba,a'ah sai don tsantsar ƙaunar da na ke mata ita ce ta kawo hakan,na san Bilal yana ƙaunar khairat fiye da yadda na ke ƙaunarta,akan khairat Bilal ya shiga wannan yanayin da ya ke ciki,to ni bazan zama sanadin rabuwarsu ta har abadan ba,ga ɗanta nan irfan yanzu ko zuwa wajenta baiyi akan mahaifinsa.to yaya kuke gani idan wannan yaron ya taso da wannan abin aransa?don haka ni na haƙura na barwa Bilal khairat".ya faɗi hakan yana kuka me sosa zuciya. Sosai iyayena suka fuskanci Shahid,sai dai duk da haka basuji daɗin sakin ba don shi aure sunnah ne kuma ba'a wasa da shi.amman sai suka yi masa fatan alkhairi da samun mata tagari. Babban company Shahid ya buɗe min,wanda Ammi tazo har gida ta shaidamin na yi murna sosai don gaskiya babu ƙarya na tara abubuwa sosai agidan Shahid,gwagwalai duk ina dasu ga filaye na masu yawa don mama bata cin kuɗi na ko kaɗan,baba na take wa magana a siyamin gida ko fili. Da daddare shahid yazo na fito sanye da hijabina har ƙasa,don har na yi shirin barci yazo little khairat tana kafaɗa ta cikin abin ɗaukar yara me matuƙar kyau,itama na saka mata ɗan kayan baccinta na jarirai,sosai ta yi kyau da ya ke yarinyar kana ganinta ba sai an gaya maka ba.kasan tsatsan larabawa ce,ga gashi wanda ya rufe mata goshinta ƙwance luf luf,sai ta zama kamar half case don tayo wani abin irin na wa,misali kumatu na wanda kullum ya ke a lotse musamman ma idan na yi dariya ga shape ɗin fuskata duk nawa ta ɗakko. A hankali ya miƙa hannu ya ɗauki ƴarsa yana yi mata wasa,ya manna mata kiss a goshinta ya cigaba da yi mata wasa,sannan ya juyo yana kalloma gabansa na faɗuwa ya ce. "Khairat ina me baki haƙuri abisa abinda zan faɗa miki,ki yafemin amman ko da baki so ya zama dole in faɗa miki,khairat na sakeki saki ɗaya". Da wata irin razana na ke kallonsa,naji zuciyata nan da nan tana neman fitowa cikin kuka na ce."yanzu ni ka saka?akan me?me kuma na yi maka?,wani abinne ya faru"?. YANA DA KYAU A MATSAYINKI NA MACE KIN SAN ABUBUWA KAMAR HAKA Zama da kayan shan iska a lokacin sanyi koh ki zauna kasan fanka iska yana huraki ta koh ina ba naki bane hakan zaii jawo maki bushewar jiki da rashin dumin jiki Yawo babu slippers tsakar gida koh kasan tiles ba naki bane ya kamata ace kina da slippers na yawo cikin gida dama wajen gidan kodayaushe domin yawo hakannan yana rage maki daraja Zama kan tiles banaki bane er uwa koh kan iron chairs da sukayi sanyi domin hakan yana daskarar da dumin jikinki kuma hq ma zaii zama a daskare knan koda bakida miji yanada kyau ace kina jin wet din jikinki keh kanki balle kuma kinada mijin Ruwan dumi ya kasance shine ruwan tsarkin ki er uwa ba ruwan sanyi rau ba don koda kina da karamin infection wnn ruwan dumin zaii hanashi tasiri da kina using ruwan sanyi karama kanki ciwo zakiyi su kara daskarewa Duk wadda tasamu wnn sako tayi forwarding ma en uwa mata su qaru suma don wnn kananan abubuwan da muka rainasu sune su cutarmu da zamatakewarmu. Wadda kuma taji dadii ta qaru tohh tayi mani adduar *_Ko kin san kama ruwa da ruwan sanyi yana buda mace?_* Ko kin san barin jikakken pant a jiki yana kawo infection? Ko kin san saka hannu a gaba yana kawo infection? Ko kin san shafa petroleum jelly (Vaseline) a kasa yana kashe ni'imar gurin? Ko kin san wanke kasa da medicated soap kamar su dettol yana kashe ni'imar gurin? Ko kin san rabuwa da magungunan mata da baki son asalinsu ba shine zaman lafiyar ki? Ki dinga banbance tsarkin bahaya dana fitsari Kuma ki yi kokari kuna gama lamura da mai gida kiyi tsarki da ruwan dumi da wuri Ki dinga amfani da cotton pant maimakon linon Ki guji yin fiysari a kowane toilet musamman na mutane da yawa {public toilet} idan kuma ya zama dole ki kwara ruwa sosai kafin kiyi, kuma kina dawowa gida ki yi tsarki da ruwan dumi da gishiri, to in sha Allah ko kin debo infection din bazai tasir ba ZAMA A KASA,SIMINTI KO TILES ZAMA TARE DA BUDE KAFA FESA TURAREN KAYA A HQ SAKA JIKAKKEN PANT BARIN PANT YA DADE A JIKI SAKA YATSA A HQ TSARKI DA RUWAN SANYI RASHIN TSARKI DA WURI AFTER XX YAWAN DAGA KAFA KO BUDEWA IDAN AN KWANTA RASHIN SAKA WANDO
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87