Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,266 words 0 views Progress saved
Download Book

FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨 *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *miss green ce* [23/09, 16:15] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_ 📃Littafi na 1 By🪶 *Ummu maher(Miss green)🍏* *GAWURTATTU 5* --------------------- *Wattpad user name* https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333 --------------- *Arewa book user name* https://arewabooks.com/u/rabiattu0444 ------------- *Sirrinmu* manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da saka turare idan zamu tafi don yaɗa xinar idone,don haka mu kiyaye. ------------------------ 7🟩8 . . . .Tun ka fin ta ƙarasa bakin gate ɗin taga duk babu motocin gidan,ta ce"oh mu dai Allah ya tsaremu da mugayen mata yanzu tsabar baƙin ciku don zanje nemawa jikata ƴanci shine za a ƙwashe motocin gidan a ɓoye." Ammar ta hango ɗan gidan Baba ƙasim me bin baba auwalu,da sauri ya fara neman wajen Ɓuya tunda yasan halin kakar ta su,da sauri ta ce"Zo nan Ammaru ko Ƙasimu ubanka bai isa ina masa magana ya ƙi zuwa ba,saboda uwarka ƴar borno tasha ruwan babur na baƙin hali shine ina magana zaka ɓoye?". ɗan shafa kansa ya yi sannan ya ce"haba kaka wane ni na'isa kina magana in ɓuya,ai ban isa ba yanzu dai me ki ke so?". "ayyo to na ɗauka rashin mutuncinne ta motsa tunda kasha nonon babur ƴan maiduguri".kallon kakar ta sa ya yi sannan ya ce"wai ke kaka me yasa kullum sai kin zagar mana iyaye sannan ki ke jin daɗi ne?don Allah ki daina yadda ki keson ƴaƴanki muma haka mukeson na mu".ta ɓe baki Hajiya kaka ta yi sannan ta ce"to rasai ai dole inyi zagi tunda kasha nonon rashin kunya,yanzu dai ni dai ina duka motocin ƴaƴana aka kaisu"?. kallon ɓangaren da Bilal ya ke Ammar ya yi yana jingine a jikin gate ɗin yana kallonda dramar da kakar ta sa ta ke yi,Ammar ya ce"to kaka ni kuma da ba ma hawa motar na ke ba Dady ya hanani ta ina kuma zan san wanda ya fita da motar ni motar Hajiyata kawai na ke hawa a gidannan". "to me Hajiya tunda dai bakasan inda motocin suke ba shikkenan ba sai ka gaya min kai ɗan hajiya bane,tunda ni dai ba ƴar hajiyar ba ce to shikkenan,bari inje in hau motar haya in tafi abuna ni dai yau babu me hanani zuwa ƙwatarwa jika ta ƴanci duk baƙin cikin mutum ma sai dai ya yi don ya yi ta banzar. Tana fitowa waje ta dinga tsare adaidaita amman suna ƙin tsayawa,cen ta hango Bilal yana ɗaga mata hannu cikin motarsa ya yi gaba abinsa. "Kai amman yau muguntar fulanin bauchi ta tashi ai Bilal kasha a maman ruƘayya uwarka dole ka Ɗagomin hannu a mota,yau zanga wanda ya Ɗaure maka gindi a gidan,cikin gidan ta koma tana ta banbaminta ta wuce saahen Mahaifiyar Bilal tana zuwa kuwa ta sameta a farlo tana cike wasu takaddu,da sauri ta ajje aikin da ta ke Rashida da Nusaiba suna tayata aikin da sauri suka kalli kakar ta su don sunsan aƙwai abinda ya kawota. "Yanzu Ruƙƙaya ke ce kika bawa ɗanki Bilal damar wulaƙantani a idon duniya ko?ki ka sakashi ya ƙwashe motocin gidan ya ɓoyesu don kada inje in karɓarwa jikata ƴancin ta ko?". "haba Umma ta yaya zance ya aikata hakan?wallahi ban san komai a game da hakan ba,don Allah ki yi haƙuri idan ya dawo zan samesa muyi maganar". "ikon Allah ki ma samesa kuyi maganar ba ma ki hukuntasa akan ɓata min ɗin da ya yi ba ko Ruƙayya?tunda shi Bilal ɗin shine ya haifeki ba ke ce ki ka haifesa ba ko? to shikkenan idan shi Abdullahi ɗin ya dawo ya yi masa faɗan tunda ke tsoronsa ki ke ji?". tana faɗar hakan ta yi tahowarta,Rashida ta ce"ni fa daman nasan ba alkhairi ya kawo wannan tsohuwar ɓangarenmu ba?ke dai umma kada ki yi magana don wallahi idan ki ka ce wa yaya Bilal hajiya kaka tazo nan kin san zuwa zaiyi suyi ta ɗauki babu daɗi don haka kawai ki saka musu idanu,idan ba haka ba wa ke shiga tsakanin kaka da Yaya Bilal?. shiru dai Hajiya Ruƙayya ta yi kanta na yi mata ciwo ta ce"Nusaiba ɗakkomin paracetamol insha kaina ciwo ya ke".da sauri nusaiba ta ɗakko mata a wani ƙaramin kid tasha sannan ta haɗa kayan ta koma ɗaki. Nusaiba na ganin mahaifiyar ta su ta tashi ta ce"Anty Rashida gaskiya kaka ba ta ƙyautawa wallahi kawai daga abu ya haɗota da Yaya Bilal sai ta ƙare akan Mama ai bai kamata ba wallahi,ki ga fa abinda ta kewa mamansu Khairat kulli yaumin sai ta goranta mata wai ita tuba ce?ai bai kamata ba tunda har ta musulunta." "hmm ke dai bari nusy wallahi matar nan ta tsayamin a ƙahon zuciya jira kawai na ke wataran ta taɓoni tasan ta taɓoni don abinda ta kewa iyayenmu ya isheni wallahi". "hmm Anty Rashida gwara dai abi a sannu mu rabu lafiya tunda ta kusa sheƙawa ma kowa ta huta wallahi da jarabar mafaɗaciyar tsohuwa,ai Yaya Bilal ɗin shine dai dai ita kaf gidannan,yanzu ba ta ce wai za ta faɗawa Baba ba wallahi muna nan da ke baza ta faɗa masa ba,don ni nasan irin son da takewa Yaya Bilal,suna cikin hirar ya shigo don haka suka tsuke bakinsu suna yi mai sannu da zuwa,yasha mur ya ce"ina Mama take?".da sauri nusaiba ta ce"tana ɗakinta yanzu ta shiga don kanta na ciwo". Shigewa ɗakin mahaifiyar ta sa ya yi ya barsu anan,Nusaiba ta ce"Anty wai me yasa Yaya Bilal ya fimu ƙyau ne?shiyasa magana ma sai ya ga dama ya ke mana mu dai sai fari kamar zabaya amman kuma ya fimu ƙyau." "Ke ni dai rabani da maganar wannan bawan Allah kinfi kowa sanin kunnensa yanzu ya iya dawowa ya ɓata mana rai don haka ni dai ki bar maganar". hajiya kaka ranar har kuka ta yi wai Soja ya hanata fita a gidan don yasan shi soja ne,duk wanda ya shigo ɓangarenta sai ta faɗa masa ai soja ya wulaƙanta ta. An sallomoni daga asibiti na yi garau dani kamar ba ni ba,Baba kuma ya kafa musu tsauraran sharuɗa akaina don haka kowacce ta kama mutuncinta arabu lafiya. Sanda aka sallamo ni Yaya Bilal ya koma da daddare na nufi sashensu ina zuwa na tarara da Abba da Hajiya na gaishesu na wayance na shige wajen Rashida har ta fara bacci na tasheta tana mitar waye ya tashe ta sai ta ganni ta ce"gaskiya Khairat ba ki da mutunci kinsan yau yini na yi aiki sai da wannan ɗan wahalar ya tafi sannan muka huta". mamaki ne sosai kam fuskata na ce"waye kuma ɗan wahala Rashida?".banza ta yi min ta shiga banɗaki ta fito tare da ɗauro alwala ta kalleni sannan ta ce"wa ye

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87