Skip to content

Chapter 50

Chapter 50

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,313 words 0 views Progress saved
Download Book

ke ɗakuna uku ne a ɓangare na,ɗakina sai nasa sai kuma ɗakin baƙi sai tsore da kitchen,sai banɗaku na har guda uku. Ni abin ma mamaki ya ke bani da kuma ɗaure kai,mutumin da ko inuwa ɗaya baya san haɗawa dani,amman wai yau shine harda wani zuwa inda na ke,nafi awa ɗaya zaune awajen har dai na gaji na ɗan leƙa ɗakin nasa,na hangosa yana shirya kayansa akan wadrope. Mamaki sosai abin fa ya ke bani,kamar wani wanda daman jinnu ne ajikinsa,to ko dai yana dasu ne?ko kuma asiri aka yi masa?tunda dai daman Anty Halisa ta ce mata wannan turaren yana karya asiri. Ɗakina na shiga,na ɗakko wayata na kira Anty Halisa tana ɗauka ban bari ta fara magana ba na gaishe ta,don yanzu ganinta na ke kamar wata uwata,don wallahi matar ta gama min komai tunda ta dawo min da hankalin miji na gare ni. Ta ce"khairat kada ki godemin ki godewa Allah,don wallahi Khairat asiri aka yi wa Bilal,don wallahi ni nasan halin Bilal,miskili ne shi sosai don yana zuwa wajen mijina kuma nasan halinsa,ke ban taɓa gani ya yi dariya ba sai dai murmushi shima sai ta kama,wannan turaren dana baki khairat yana karya duk wani asiri,abinda zan gaya miki ki ƙara tashi sosai akan addu'ah kifi ƙarfin mahassada,don na lura idan ki ka zauna sakaci abin bazai yi kyau ba,zanzo gobe insha Allah". Godiya na yi mata na yi shiru ina tuno labarin da hajiya kaka tasha bani,Gaskiyar zancen Anty Halisa aƙwai lauje cikin naɗi ko kuma saran ɓoye acikin wannan maganar tata. Abinda khairat bata sani ba shine,Bilal yana matuƙar sonta alokacin da tana ƙarama sosai,don tun haihuwarta ya ke cewa maman khairat idan ta girma zata bashi ita ya aura.sai dai kowa ya yi tayi mai dariya ana ganin ƙuruciya ce. A ƙalla Bilal ya bawa khairat kusan shekara 15,don sanda aka haifi khairat ɗin yafi shekara 14 tun tana ƙarama ya ke masifar sonta,don shifa acewarsa bazai auri mace fara ba,don shi ya gaji da ganin fararen don duk ƴan gidansu farare ne ƙal,khairat ita kaɗaice ta fita zakka,baƙa ce kalar mahaifiyarta amman baƙinta mai kyau ne,gashi tun tana ƙarama tana matuƙar burgesa sosai,bata yadda da kowa sai Bilal da kuma Hajiya kaka,sai su yini asashen Hajiya kaka,idan suna hira yakan tambayi hajiya kaka ce wa,idan khairat ɗina ta girma ita zan aura,kaka zaki bani ita?Hajiya kaka sai dai ta yi dariya tana jin daɗin hakan har cikin ranta,ta kance masa haba Bilal me zai hana kuwa?ai ko uwarta inya mura bata isa ta hana afkuwar hakan ba. Ganin irin sonda Bilal ke yi wa khairat,yasa su mama iklima baƙin ciki sosai,su ga nasu ƴaƴan ko kallonsu Bilal baiyi sai wata khairat,yarinyar ma baƙa wacce ƴaƴansu suka fita komai.daman kuma su Nadiya sun girmi khairat amman da watanni wata baƙwai nr tsakaninsu,Rashida da khairat kuma wata uku ne,Rashida ta girmi khairat,acikinsu dai Khairat ce ƙarama,don bayan maman khairat ta haifi Salim sai da ta yi shekara 8 sannan ta haihu harma ana tunanin ta gama kenan,to cikin ikon Allah sai ta haifi khairat,bayan khairat ɗinma ta sake haihuwa ta haifi maher tsakaninsu da Maher shekara uku ne. To su mama iklima fa ba suyi ƙasa aguiwa ba suka wuce wajen boka,don araba khairat da kuma Bilal,ya tsane ta tsana mai yawa wacce ko inuwa ɗaya baya son su haɗa. Ai kuwa hakanne ya faru,Bilal ya fara canjawa khairat,kunsan abin yaro ta saba dashi tana ganinsa za tayo wajensa shi kuma,ya ture ta ya tashi daga wajen,har Hajiya kaka ta gane hakan,tun daga nan ta hana khairat zuwa wajensa,ko tana kuka wai akaita gunsa sai Hajiya kaka ta hana ta,to wannan shine musabbabin tsanar khairat da Bilal ya yi. Wanka na shiga,wankan da atarihi na ina tunanin ban taɓa yin irin saba,na gurzu sosai sai da na yi kusan awa ɗaya cikin bathtube wanda na cika masa turaren wanka,daman gama haila na kenan na yi wankan tsarki,na haɗa ganyen magarya na yi tsarki dashi na wanke jikina fes,gashina na wankesa na busar dashi,sannan na fito ɗaure da tawul ina goge kaina wanda na wanke yanzu. Turus naja na tsaya ganin mutum a bakin gadona daga shi sai boxer sai singlet,jikin mutuniyarku fa ya fara rawa,mamaki,ruɗu,duk suka cika ni,tuni wannan ƙwarjinin ya bayyana akan fuskarsa,gashin ƙirjinsa dana ke gani ba ƙaramin haukata lissafina ya yi ba. Na murɗa ƙofar banɗakin zan koma sai kuwa ya ce"a'ah ina zakije? dawo mana,ke da ɗakinki,ni tafiya ma zanyi".ya faɗi hakan yana tashi. Turo ɗan ƙaramin baki na na yi sannan a hankali na fara tafiya,don tawul ɗin dana saka very small ne,ya yi guntu don da ƙer ya rufe ni,na koma gaban madubi ina wani muxurai,sai na hangosa ta cikin madubin yana tsaye yana kallona,tsoronsa sosai naji yadda na hango sa kamar wani ɗan rastling,duk jikinsa awani mummurɗe,da sauri na sumkuyar da kaina. Ya ce"mara kunyar ƙarya kawai".yana faɗar hakan ya fita,na dafa ƙirjina wanda ya ke kai kawo,anya kuwa xan iya wani jan aji yanzu,wallahi dana gansa sai naji duk ƴar nutsuwata ta shige,da ƙer na yi control ɗin kaina na shirya cikin wata doguwar riga amman ta atamfa,koda na kalli kaina sai da na yaba,saboda yadda ta amshe sosai komai a mulallinsa,na zauna na shirya ɗaurina,Xahra buhari ya yi min kyau sosai na shafa hoda na gyara girata na shafa lipstick leɓena ya yi kyau sosai daman gani da ɗan ƙaramin baki. Na samu wani ta kalmi na high hill me igiyoyi wanda ya ke kalar kayan green da kuma ja,na feshe jikina da turaren Anty Halisa,tuni na fara wani irin ƙamshi mai daɗin daɗaɗawa. Tun kafin in iso ƙamshina ya iso wajen,ya buɗe idanuwansa manya ya tsuraminsu,tuni naji ina neman gurɗewa saboda takalmin dana saka. Wow na ce azuciyata shima wanka ya buga da wata ɗanyar shadda ruwan skye blue ta yi masa matuƙar kyau,kamar ka ɗaukesa don gaskiya Yaya Bilal babu laifi ya haɗu. Bansan ina kallonsa ba sai dana ji ya ce"Yi a hankali dai kada ki faɗi?ki wani zuro min ido,da wasu ficicin idanuwanki".hararsa na yo na murguɗa mai baki na wuce dining inda na shirya abinci na,na buɗe na zuba a plate na fara cin abinci na cikin nutsuwa. Sosai ya ƙuramin ido har na tsargu na ɗago na kallesa sai kuwa ya ce"ni baza a bani abincin ba"?. A hankali na fara zuba masa ko kafin in ƙarasa zuba masa ɗin ma har ya iso inda na ke.sosai numfashinmu ya haɗu waje ɗaya,ya tsugunna agaba ya ɗakko plate ɗin abincin ya ɗebo loma ya miƙomin,na kauda kaina gefe ina wani ɓata rai.ya ƙara ɗebowa na kauce. Ajje abincin ya yi,banyo tsammani ba kawai naji anyi sama dani,sai babba ɗako wato Ɗakin Yaya Bilal,sai wani shure shure na ke amman shi ko ajikinsa shi rashin kunyar khairat ma sha'awa take basa,ai kuwa na ƙulla araina sai rafka masa rashin mutunci. Ba'azo inda na keso azo ɗin ba,aƙwai dai lokaci,amman yanzu zan nuna masa duk abinda ya baka tsoro wataran shi zai baka dariya. *Kamar yadda kuka sani na yi muku alƙawarin koya muku abubuwa a wannan book ɗin* To yanzu zan fara da maganin ƙuraje ko wani iri. *Sirrinki🌈👂🏻* 1 *Yadda ake maganin ƙurajen fuska.* Daga ummu maher Asamu garin

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87