Chapter 22
Chapter 22
sauƙi ko?soyayyarsu kuma da suke yi da Bara'atu su cigaba da yin soyayyarsu ko kada su cigaba wallahi ba damuna zaiyi ba".ina faɗar hakan na tashi na shige kitchen dan ɗora girki don ni ko san hirar yaya mk ɗinma bana son ayi,ni dai ba ni na ce ina sonsa ba?hasalima ni bana sonsa wallahi ni da zai auri Bara'atu wallahi daɗi xanji don sam bana son in koma gida ya cigaba da zuwa wajena a matsayin saurayi sam bana son hakan,wata dabara ce ta faɗomin na fito na samu Anty khadija har ta fara chat ita da yaya Aliyu sai shagwaɓe mai take wai ya dawo,ni dariya ma abin ya bani da kuma kunya bayan sun gama ne na ce"yauwa Anty khadija don Allah magana na ke son muyi".kallona ta yi sannan ta ce"to ina jinki ya aka yi"?. "Anty na don Allah so na ke ki faɗawa hajiya kaka soyayyar yaya mk d kuma anty bara'atu".kallona ta yi sosai sannan ta ce"to wai ke ba kya son yaya mk ɗin ne?". "Eh anty". ɗan murmushi ta yi sannan ta ce"yo ke wa ki ke so"?.anxo wajen kallonta na yi babu ko kunyar ta na ce"na ce yaya Bilal." da sauri ta tashi sannan ta ce"ah yarinya gyara zancanki wannan guy ɗin yafi ƙarfinki wallahi kina ganin mutum har mutum kamar shi ya yi kansa mutum mai izza ji-ji da kai uwa uba ƙyau da komai kin san ba fa zai yadda ya soki ba?don nasan duk nasan irin tsanar da ya yi miki sannan ki ce wai shi ki ke so?ni dai shawarar da zan baki ki yi haƙuri ku cigaba da lallaɓawa da yaya mk ɗin ina ganin hakan zai fiye miki".tun kafin ta gama naji wasu hawaye masu mugun zafi suna zubomin,yanxu idan na fuskance ta tana nufin yaya Bilal bazai iya aure na ba,saboda ni mummuna ce kuma baƙa?sosai maganganunta sukayi min ciwo sosai na tashi na tafi ɗakina na faɗa kan gado na fasa wani irin kuka mai cin rai,ciwo sosai na ke ji acikin zuciyata aduk sanda aka danganta ni da yaya Bilal bazai iya rayuwa dani ba yafi ƙarfina,tabbas nasan da hakan ya fi ƙarfina ne sa ba kusa ba,amman kuma ni a duba yadda na ke sonshi mana ayi min adalci. ta baya na naji an dafa ni na juyo a hankali naga anty khadija ce ta ce"yi haƙuri ABIN CIKIN ƘWAI ta hajiya kaka,ki yi haƙuri kinji ban zata ranki zai ɓaci ba,insha Allah bazan sake ba kinji,ni da ki ke ganina zan tsaya miki har sai na ga kin auri yaya Bilal ɗinki". Sosai na ji wani farin ciki ya baibaye ni na tashi zaune na rungumeta,ta buga baya na a hankali ta ce"yi shiru daina kuka kinji ta yaya Bilal".ɓoye fuskata na yi a bayanta wai ni kunya. Tun daga ranar idan yaya mk yazo sai anty khadija ta ce mishi ai ina gidan koyon ɗinki da ta sakani,tun yana daurewa har dai rannan ya ce azuciyarsa zakusan baku da wayo idan kunsan wata baku san wata ba. rannan da ya tashi zuwa sai ya ɗakko Rashida da kuma aminiyata Maryam,wacce duk duniyw ba ni da aminiyar da ta wuce sai Rashida daman mu uku muke rayuwarmu ita maryam anan ƙasan unguwarmu take iyayanta masu matsakaicin ƙarfine ko islamiyayya da mukeyi tare babanmu ke biya mata har skull ɗinda ta yi babanmu ne ya ɗauki nauyinta,ganin dai irin zaman amanar mukeyi da ita tun muna ƙananu ita ta ce bata ra'ayin yin skull ta boarding mu kuma muka zaɓi boading ɗin to tun daga nan ne fa muka ɗan raba jaha saboda sai mun dawo hutu ne muke haɗuwa. Ina kitchen ina girki kawai sai Naji anyi ihu an rungumeni ta baya,ina juyowa naga Maryam da gudu nima na ɗafeta muna juyi a kitchen ɗin sai kuwa ta ce mu da Rashida ne tana waje a hanya ne taji ciwo,to kinsan Rashida da kafiya yanzu haka da bin bango ta shigo ta hana ko in ɗan taimaka mata"...ai bata ƙarasa faɗar maganar ta ba da gudu na fito don ganin Rashidar to sai dai me Yaya mk na gani yana face ɗi na ya kalleni sosai ya yi dariya sannan ya ce"ah Hajiya me ɗinki ƙaraso mana"?.ya faɗi hakan yana ƴar dariya. Wata best ce ajikina wacce ta ɗameni sosai sai zanin dana ɗaura da kuma irin hular na ta zaren lilo wadda yare suka fiye amfani da ita musamman a awajen bacci. Na rasa yadda zanyi gashi na riga dana fito ya gama kallona tsaf,sunkuyar da kaina na yi kamar wata munafuka kawai sai naji maryam ta zuramin hijabin da ta zo dashi da gudu ta koma farlon. Rashida tazo ta wuce ta kusa dani tana ƴar dariyar mugunta,yadda kasan in shaƙesu haka na ke ji tsabar baƙin ciki,jikina duk a mace na ƙarasa ina kallon ƙasa,na gaishe sa ya amsa sannan ya ce"sannu gimbiya mai koyon ɗinki?Khairat ban taɓa tunanin haka daga gareki ba?banyi tsammanin haka ba?nasan ke mutum ce mai gaskiya hasalima baki iya ƙarya ba?to me yasa ki ke min ƙarya ni?tabbas ko da baki faɗa ba nasan komai Khairat,bakya sona Khairat idan na fahimta kamar dole na yi miki amman ki yi haƙuri don Allah idan na takura miki,zuciyata ce bata yi min adalci akanki son da na ke miki shine ya ɓoye mode ɗin fuskarki gareni,ina son ki fito sosai straight foward ki faɗamin matsayi na agunki don Allah". kasa ce wa komai na yi sai da yaga ƙwalla ta taru a idanuwa na alamar zanyi masa kuka sannan ya ce"sorry yi haƙuri kinji ban ɗauka wannan maganar za ta ɓata miki rai ba,amman don Allah ki yi haƙuri ki daure ki faɗamin abinda ke ranki saboda kada mu ɓatawa juna lokaci tsakanina da ke". Cikin siririyar murya ta na ce"yaya Mk ka yi haƙuri amman wallahi bawai bana sonka bane kunyar anty khadija na ke ji shiyasa na ke ce mata ta ce na je koyon ɗinki".ɗan murmushi ya yi sannan ya cs "khairat kenan uwar kunya to shikkenan yanzu dai ayi haƙuri adinga kulani kinga duk yadda na rame saboda tunaninki ko aiki fa bana iya yi a office?sai dai inyi ta rubutu shirme".dariya ya ɗan bani rayuwa kenan shi yana sona baki ɗaya da zuciyarsa ni kuma ina son wanin sa haka.nan dai muka cigaba da hirarmu ya ɗauko wani ƙaton gift a nannaɗe na miƙomin yana murmushi don shi ma'abocin murmushi ne. Juya abin na yi a hankali sannan na ce"na gode yaya mk Allah ya ƙara arziƙi".ɗan murmushi ya yi yana kallona sannan ya ce"ba komai matata kada kiji komai gobe Baba zai dawo daga tafiya inason in shigar da maganar aurenmu ayi komai a gama". Ai ban san sanda na zaro idanuwa na ba cikin tsoro,kallona ya yi sosai sannan ya ce"lafiya ki ka tsorata haka?ko kuma tsoron auren ki ke"?.mayar da wani malulun da ya tokare ni na yi sannan na ce"ba komai".daga haka ban ƙara cewa komai ba har muka rabu na koma cikin gidan.har na shiga bai daina kallona ba ya shafa gashin kansa sannan ya ce"khairat ina sonki da yawa Allah ya bani ke na more mata". Ina komawa ciki suka fara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87