Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Abin Cikin Kwai Book One Complete Hausa Novel 1,325 words 0 views Progress saved
Download Book

ta dafe Ƙirjinta ta ce"yau na shiga Ɗaka ban fito ba ni Ramatu,kai Bilalu me ka yi mata?da sauri ya kalli hajiya kaka ya ce"kaka don Allah ki taya ni bawa khairat haƘuri ta yafemin don Allah".da sauri hajiya kaka ta ce"a'ah badani ba?kai sunduƘi ne da baza ka iya bata haƘuri ba?to ni dai babu ruwa na Allah,Kuma kazo ka fitar min aƊaki tunda ba Ɗakin RuƘayya bane,ba kuma da kuƊinta muka haƊa muka siya ba,itama dai cin arziƘi take ko?to maza yi hanyar waje,indai na kallon wannan koƊaƊƊiyar fatar ta ka". Sosai maganar hajiya kaka ta basa haushi ya fita fuuu,hajiya kaka ta ce"uwarka RuƘayya ita ka kewa wannan haushin kamar kare amman fa ba Ramatu ba."ta faƊi hakan tana hararata ta ce"yauwa sauran kuma wataran yazo ya yi miki daƊin baki ki sakar masa fuska,tunda bakisan inda ke yi miki zafi ba,kema sai kin rama duk Ɗibar albarkar da akayi miki,ni Ɗinnan zan baki goyon baya ki luguiguitamin shi ya yi liss,wannan Ɗaga kan nasa duk sai ya daina sa." ni haushi ma kalaman kaka suka bani na ce"ni don Allah kema ki fita ki barni ni kaƊai,kuma ni ce miki na yi zan kulasa,ni dashi har abadan wallahi,sai dai ya nemi wata matar ya aura amman ni na tsanesa wallahi".ƙuri hajiya kaka ta yimin da ido na magantu na ce"a'ah lafiya kuma ki ke kallo na?". Sai kuwa ta fara magana cikin fushi"wato kin tsanesa ko?to ki kashe sa mana?Ai kanki ki ka yiwa asara ba Ramatu ko RuƘayya ba,ko kuma Abdullahi bawan Allah ba,Ɗanki ki ka yiwa asara don shine zai taso maraya,don kinga nidai ina da ƳaƳa da jikoki da yawa kinga don na rasa Ɗaya bazanyi hauka ba".Ta faƊi hakan tana harara ta,ranar faƊa sai da mukayi faƊa da hajiya kaka don kuwa ko girki ma da kaina na tashi na yi danaji uwar yunwar dana keji tana neman kassara ni,don har yanzu ban daina wannan mugun cin ba,da za'aajjemin indomie huƊu tas zan cinye,ai kuwa bayan na daga jallop Ɗin taliya me ruwa ruwa wadda taji nama sosai taji attaruhu,na baje a falonta na zauna ina ci,ciki na kuwa ya yi kamar tulu idan zan tashi da Ƙer na ke tashi yanzu sai da dabara. Taliya Ɗaya na dafa na zauna ina ci hajiya kaka ta harare ni sai kuwa ta fara magana kamar za tayi kuka ta ce"ni dai wallahi Bilalu ya cuce ni daya sakeki ki ka zo kina cinye min abinci na,jiya ma fa taliya biyu ki ka cinye gaba khairat,wannan wani irin cine haka?ni wallahi ina tsoro ko ƳaƳan aljanune suke cinye wannan abincin da ki ke ci"?.da sauri na kalleta ina lomar taliya ta na ce"Allah ya tsare ni wallahi,ni ki daina yimin wannan fatan gaskiya,kaf ƳaƳanki da jikokinki babu ƳaƳan aljanu,kawai ni kuma sai ki wani ce ƳaƳan aljanu ke ciki na?". Da sauri ta ce"a'ah fa khairat dole inyi magana gaskiya,barni in faƊi gaskiya wallahi,ga cin nama kamar kura sai ki cika min naman miya acin girkinki,ni wallahi ina zargin ma kina cinye kilo biyu kullum,nima naga ai ba kullum ake kawo min naman miyan ba".da sauri na kalle ta na ce"kaka nifa wallahi ki barni tunda dai aƘwai abincin ki barni inci haka kawai in zauna da yunwa".muna cikin wannan fafatawar yaya Aliyu da babanmu suka shigo,na yi yunƘurin tashi sai naji na kasa dole ne na zauna na gaishesu,babs ya kalleni cikin tausayi na ya ce"ya jikin na ki khairat"?. "Da sauƘi baba". Murmushi ya yi sannan ya ce"kina zuwa asibiti kuwa"?.kunya duk ta isheni sai na ce"a'ah Baba bantaƁa xuwa ba".da tsoro ya ke kallona sannan ya ce"haba khairat yaya mace me ciki zata zauna bata zuwa asibiti?ai bazai yiwu ba ko".?da sauri hajiya kaka ta ce"yauwa gaya mata dai,kaima da ka ke namiji kasan dai dai ba?amman wannan yarinyar sai binta na ke akan taje asibiti amman fafur ta Ƙi zuwa,koda ya ke dacen ma fa cewa ta yi wai zubar da cikin za ta yi?." Da sauri Baba da yaya Aliyu suka haƊa baki wajen ce wa zubar da ciki kuma?".Hajiya kaka ta ce"eh Ƙwarai kuwa ai yanzu wannan khairat Ɗin da kuke gani ba irin tada bace,ta yanzu sai fitsara abu kaƊan ta hauka da rashin kunya ko kuma musu,ga taurin kai kamar ubanta lokacin yana yarinta". ta kalli babanmu tana hararata,Baba kunya ta ishesa ya ce"kai amman khairat abin ya bani mamaki,ina iliminki na addini?ina wayewarki take?ai ko jahili bazai zubar da ciki ba.amman ke da hankalinki".nan dai Baba ya dinga yimin nasiha sosai,na fashe da kuka na ce"kuyi haƘuri insha Allah bazan Ƙara ba,nima ba laifi na bane laifin zuciyata ne,sai inji wani lokacin duk haushin kai na ma nake ji,balle kuma wani shiyasa duk na ke hakan". Baba ya ce"babu komai a halin da ki ke ciki ai ya kamata ayi miki uzuri,don haka idan har ki kaji kina jin hakan ki dinga addu'ah sosai".na Ɗaga masa kaina yana Ƙasa,sai kuwa kaka ta ce"yauwa malik kada kaga abincin da ka ke kawowa yana saurin Ƙarewa.To ba wani ke cinyesa ba sai wannan buhun simintin Ƴarka,wallahi taliya biyu take cinyewa kullum,biredi Ɗan Ɗari uku cinyesa take,naman da kuke siyomin wallahi idan aka siyomin na sati Ɗaya yadda ake da,to fa wannan aƘwana biyu take cinyewa". sosai abin ya bawa su Baba dariya,yaya Aliyu ya ce"caƁƁijan ki ce nima in Ƙaro kuƊin da na ke Baki ko?".da sauri ta ce"ai kuwa dai don Ƙanwarka rumbu ce yanzu,shima Bilalu bari yazo sai ya dinga ajjemin kayan abinci buhu buhu".dariya muke ta yi hardani Ɗin amman tana ce wa Bilalu sai naji duk zuciyata ta yi Ƙunci. Baba ya ce mu shirya zamuje duba Baba Abdullahi daga nan sai a duba lafiya ta,haka kuwa aka yi doguwar riga na saka buba me buƊewa saboda yanzu duk kayana sunyi min kaƊan sosai,ai kuwa ciki na ya Ƙara tsini sosai,hijabi na saka har Ƙasa,ruwan coffie wanda ya haskani sosai,daman gashi na yi mugun fari. muna fitowa hajiya RuƘayya ma ta fito har da Bilal,ya hangoni naga yana yimi kallon tsaf,murna fal zuciyarsa yadda yaga khairat na tafiya da Ƙer sai abin ya basa tausayi sosai,yana so ya taimaka mata amman kuma yana tsoron abinda zai biyo baya,motar yaya Aliyu muka shiga da ya ke jip ce,kusan mazaunanta 14 ne,hajiya RuƘayya sai wani nan nan take dani,ni dai kallon kowa kawai na ke,nidai hankalina yanzu yana kan cikina in haihu lafiya in basu Ɗansu don ni yanzu hankalina ya koma kan karatuna don ma su zainab na taya ni wasu abubuwan . jikin Baba Abdullahi ya yi sauƘi sosai don ranar ma yana zaune ana ta hirar yadda abin ya faru,yaya Aliyu ya ce"kai gaskiya Ƙasar nan tamu aƘwai gyara,yanzu fa babu yadda za'ayi ace gwamnati bata san abinda damas ya ke ba,amman anyi shiru an zuba masa ido,yana Ɗibar yaran mutane kamar awakai".wani tunani ne ya faƊomin azuciyata na ce to Allah ya cika min burina,amman tabbas ina son kawo Ƙarshen zaluncin damass. hajiya kaka na ganin duk an taru ta ce"yauwa Bilalu riƘe jakar khairat ka rakata Ɓangaren masu ciki don a binciki lafiyarta".ai kuwa da sauri ya ce"to. . .to kaka bari in rakata".ya faɗi hakan cikin zumuɗi. Wata muguwar

Table of Contents

Chapters

87 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87