Chapter 39
Chapter 39
dubu ɗari biyar haka ta bayar wai duk don ta dawo budurwa. Sosai iyayenta suke tuhumarta akan kashe kuɗinta,amman da ya ke tana musu ƙarya da Bilal sai suka daina tuhumarta ta cigaba da wandaƘarta da kuƊaƊa,sosai ta ware kuƊi don siyan wasu kayan kitchen da sauran abubuwa. Alhaji damas ys samu yadda ya keso,don haka yanzu wani kallon tara saura Ƙwata ya kewa Bilal,gani ya ke tamkar fankonsa ya ke ganinsa,tunda wadda ya bawa amanarsa,ya Ɗauketa matsayin mai tarbiyya to fa ta watsar da komai ga Alhaji damas,ta bashi komai ta yadda shi Bilal Ɗin ko alfarmar riƘe hannunta bai samu ba. sosai wannan abu yake masa daƊi saboda ko ayanzu ya gama da Bilal, gamawar har ya mutu bazai taƁa mantata ba. **** koda aka tashi yin dinner babu yadda Rashida bata yi dani ba,akan inje dinner Ɗin naƘi zuwa tunda dai ni ba sona ake ba,to kuma me zanje inyi?Don yaya Bilak bazai ji kunyar wulaƘanta ni awajen mutane ba. Da Rashida tarasa yadda za tayi dani sai taje ta sanu yaya Aliyu ta gaya masa komai,yazo ya yi min faƊa akan inje,kuma su yaya salim ma duk zasuyi idan har banje ba baza suji daƊi ba,haka dai na haƘura amman can cikin zuciyata tsoro fal. Ana cikin maganar hajiya kaka ta fito daga kinta baya sun gama faɗa da mero.sai kuwa ta ce"kai Aliyu rabu da ƴar banza,ina cewa nan naji kina gayyatar ƙawayenki fatin?sai yanzu za'a wani zo ana wani rarrashinki akan kije?to yasin kada kije ni daman haka zanso sai in hakimce akan kujerarki ince ni ce uwargida. Duk wanda ke wajen sai da ya yi dariya sosai,ni kuwa kallonsu kawai na ke,ɗaurin aurena da za'ayi da Yaya Bilal shine kawai ya tsayamin aƙoƙon zuciyata,ko wani irin zama zanyi dashi oho?. Ƙwalliya aka yimin sosai wacce ni da kaina sai da na yaba kaina,wani farin les ne wanda ya gaji da haɗuwa gashi yaji ruwan stones sai walƙiya ya ke,kamar ka ɗaukeni,ƴar pos ɗina da kuma takalmi na duk ash ne suma sunji ruwan stone,diri na sosai ya fito da ya ke ni dirarriyar macece,sai na haska na yi wani irin bajajjan ƙyau wanda ya amsa sunansa aƙyau,head ɗina ma arsh ne sai net golden shima sai walƙiya ya ke,aka yafamin shi akaina. "Wow gaskiya amaryarmu kinyi ƙyau sosai,gaskiya yaya na zaiyi santin kyaun nan".cewar Rashida wacce ke ta faman ɗauka ta a hoto kamar babu gobe. Bansan lokacin da naji wani hawaye yana zubomin ba,da gudu na tafi naje na rungume mahaifiyata tsam kamar wani zai ƙwacemin ita,i'tama ɗin rungume ni ta yi tana ɗan buga bayana tana rarrashina,har cikin zuciyarta take jin babu daɗi arabuwa da tilon ƴarta mace da zata yi. Su mero ana gefe ansha ƙwalliya sai ka rantse ba meron hajiya kaka bace,ganin khairat na kuka dai yasa duk jikinta itama ya yi sanyi sosai,ta koma gefe ta rakuɓe tana kallon uwarta hansai wacce ke ta shirinta cikin haɗaɗɗiyar atamfarta super wacce Hajiya kaka ta bata. Itama da gudu taje ta rungume hansai tana ta kuka,Hajiya kaka ta ce"kai ku ganemin wani shashanci,don kunga iyayenku na wajen suna ƙefta muka idanuwa ku taso kuyi kuka shine zaku faramin kuka kamar gidan mutuwa?to wallahi ba dani ba,duk shegiyar da ta ƙaramin kuka yasin sai na saka jikana fasa aurenta". dukkanmu juyowa mukayi muna kallon hajiya kaka,wacce ta yi mirsisi kamar ba ita ce ta yi maganar ba,ta ɓantari guntun goronta ta saka abakinta tana tauna,ganin duk muna kallonta sai kuwa ta ce"meye ne kuma kuke kallona?To wallahi kuruwa ta kurr akanku,ina ƙwanannan aka samu wata shegiyar ta yi min asiri cikin matan ƴaƴana?duk da ban yarda da hakanba,don ni dai naci dubu sai ceto,mai dambu kafin ta mutu ta barmin tsari ajikina.kunga kuwa kuma sai dai kuci kanku".ta faɗi hakan tana zare fici-ficin idanuwanta. Dariya mero ta tintsire da ita sosai sannan ta ce"ah to mudai ma idan mayun ne ai sai dai kece kika shafamin?Tunda nidai Babana ƙaninki ne,ita kuma khairat kece ki ka haifi Babanta,kinga kuwa sai dai daga kene wannan matsalar". Hawaye kaka ta farayi sannan ta ce"Allah ya isa na mero da wannan zagin da ki kayimin,kuma wallahi ki yi asannu,don ba ƙaramin aikina bane in saka jikana ya fasa aurenki". Dariya sosai mero ta yi sannan ta tashi taɗan riƙe doguwar rigarta mai kalar blue da fari da ƙaton takalminta me tsini kalar blue,ta tashi a hankali don takalmin shirin faɗar da ita ya ke,a kunnen hajiya kaka taje ta raɗa mata wani abu,ai da gudu ta fita Hajiya kaka tana ce wa"wallahi uwarki hansai ki ka faɗawa magana bani ba,ƴar banzar yarinya mara kunya".ta faɗi hakan tana fashewa da kuka. Kunsan me mero ta raɗawa hajiya kaka?Hmm ku matso kunnuwanku kuma kuji,cewa ta yi to idan ya fasa aurena ke zai aura ki haifa masa yara. kun san kuwa dole maganar ta yiwa hajiya kaka zafi,har aka fara tayi party ɗin bani da niyyar tashi,mama sai rarrashina take amman kukan ƙara bulbulowa ya ke tamkar dai an buɗe famfo. Itama hajiya kaka na bata tausayi sosai,ta rungumeni tana bubbuga bayana sosai da ƙer dai hawayen ya tsaya.Rashida tana tsaye itama kukan take tana sharewa. Tabbas dole ne khairat ta yi kuka,saboda ko ba don komai ba sai abinda ya faru da ita,tasan halin yayanta tsaf yana da zargi sosai,bazai taɓa amsarta amatsayin matarsa ba,musamman yadda taga mahaifiyarsu na nunawa akan auren yaya Bilal da khairat,ta kasa gane cewa komai muƙaddari ne daga Allah,Daman Allah ya ƙaddara khairat matar Yaya Bilal ce babu yadda kuma za'ayi don Allah ya ƙaddara faruwar hakan. Da gudu Rashida ta taho ta rungume khairat,ta bayanta tana ta kuka itama,tuni suka fara bawa Hajiya kaka haushi ta ce"Innalillahi gaskiya nidai ku fitarmin daga ɗakina tunda babu wanda ya mutu balle ku sakani agaba kuna kuka,kamar za'a kaita inda za'a dinga figar namanta ana miya dashi?Haba abinnan ya yi yawa wallahi,duk kowa ya tafi wajen partyn har wannan uwar rawar kan mero ta tafi amman ke kina zaune kina aikin kuka." Mama ce ta rarrashemu mu duka har bakin motar da zata ɗaukemu sai da ta kaimu sannan muka shiga ita kuma ta dawo,ƴan uwanta da sukazo tare muka tafi,don ita ta ce baza ta jeba,don haryanzu zuciyarta bata mata daɗi idan ta kalli gidan mijinta da ta bari abisa sharrin da aka laƙabawa ƴarta,shi kuma Malik ba tare da binciken komai ba ya ɗora mata laifi,bayan wannan ma har da tukuicin saki,ta goge hawayen da suka zubo mata. Hajiya kaka na kallonta tausayin ta duk ya cika mata zuciyarta,ita fa har yanzu bata yadda da abinda aka faɗa akan khairat ba,tabbas aƙwai saran ɓoye acikin lamarin. **** wani irin mummunan bugawa naji gabana ya yi,hango Jidda wacce ta gaji da haɗuwa wajen yin ado da ƙwalliya,ga gogan A.D a kusa da ita,ta saƙalo hannunta ta bayansa ana musu hotuna,na kalli kujera ta babu kowa akai,na rasa tudun dafawa na tsaya kawai,ganin abinda ke faruwa yasa Rashida zuwa wajena,ta riƙemin hannuna ta kalleni sosai cikin dakiya ta ce"khairat ki nutsu fa,kada ki diririce yadda ki ke aduk sanda kiga yaya Bilal,muje ki zauna".ta riƙe hannuna har kan kujera ta. Na zauna duk jikina a sanyaye,ina kallonsu ta gefe,ko ƙura ta basu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87