Chapter 31
Chapter 31
har an bugo mata waya an gaya mata,ina zaune a babbar kujera ina kallon saman Ɗakin kamar dai wani hotone aka ajjemin shi a saman Ɗakin. Ina zaune naga yaya Aliyu ya fito daga Ɗaki dagashi sai t.quater da singlet ya shiga Ɗakina wanda na zauna Ƙwanaki dana zo,ba dai wani datti ya yi sosai ba ya shiga ya sharesa tsaf har ban Ɗakin sai da ya share tsaf,sannan ya fito ya sameni na zabga uban tagumi hawaye wasu na bin wasu. Kawai sau naga yaya Aliyu a gabana ya tsugunna ya cire min ta gumin dana yi,ya saka hannayensa ya gogemin hawayen a hankali sannan ya ce"khairat!me yasa baki yadda da Ƙaddararki ba ne?ashe Allah bai i'sa ya jarabci bawansa bane?to daga yay kada na sake ganinki acikin makamancin wannan halin,ni nasan ke wacece fiye da sanin kanki,ni yayanki ne uwa Ɗaya uba Ɗaya,ko da ace abinda ya faru da gaske ne babu abinda zau saka in guje ki,don Allah khairat ki Ƙwantar da hankalinki ki cigaba da rayuwarki kamar da,gidanmu da mutanen gidanmu ki Ƙyalesu ki manta dasu kamar yadda suka kasa fahimtarki asannu gaskiya xa ta yi halinta kinji Ƴar Ƙanwata".ya faƊi hakan da murmushi akan fuskarsa. anty khadija na tsaye ta harƊe hannuwanta akan Ƙirjinta ta wani taƁe bakinta a zuciyarta ta ce daga baya kenan,ammsn bata baru maganar na ta ya fito ba,saboda duk iskancinta tana matuƘar jin tsoronsa. yaya Aliyu da kansa ya shiga kitchen ya dafamin indomie har biyu da Ƙwai wanda yasha su tumatir sai tashin Ƙamshi ya ke,ya dafamin ruwan Ɗumi da madara wadatacciya,har Ɗakin ya kawo min ina ganinshi na yi saurin cire tagumin ina murmushi don naga halin da ya ke shiga idan ya ganni acikin tashin hankali. da kansa ya dinga bani,na kallesa wasu zafafan hawaye na zubowa acikin idanuwa na,na saka hannuwa na gogesu saboda tausayin yaya Aliyu hannuwansa har kakkarwa suke don ya ciyar dani,shima kana ganinsa zai baka tausayi don ciyar dani ya ke amman jijiyoyin kansa duk atashe. na kallesa na fara magana murya ta na rawa na riƘe hannuwansa na ce"Yaya aliyu don Allah ka yi haƘuri kaji?wallahi ban san me ya faru da rayuwata ba?ina cikin ruƊu sosai,akan abinda ya faru dan . . . . .saurin rufemin baki ya yi sannan ya ce"shhh kada in ƙara jin kin yi magana,abu ɗaya zaki yi ki faranta min?shine kada in ƙara ganinki acikin damuwa sam,ki manta komai kamar ma ba'ayi ba kinji?".ɗaga masa kai na yi ina ɗan murmushi ya cigaba da bani abincin sai da na cinyesa tsaf daman na ɗakko uwar yunwa,tun jiya rabona da abinci. maimakon ya ƙeleni ya tafi,sai ya samu waje ya zauna ya dinga bani labari har da na abin dariya,sai gani ina dariya kamar bani ba,daman hakan ya ke buƙata ya tashi ya fita har fita kuma sai ya dawo ya sa ke zama ya ɗauki wayata da ke gefena,ya buɗe ta ya shiga playstore ya buɗemin manhajar arewabook,ya yi murmushi ya ce"yauwa kinga wannan manhajar ina son ki kasance da ita a kullum ammanfa garin karatu kada ki dinga zama ba sallah ko rashin tsafta,duk da dai nasan ƙanwar ta wa aƙwai tsafta."ya faɗi hakan yana murmushi,ya sanya min data har ta wata ɗaya sannan ya bani wayar ya fita. Yana fita na danna number mamana na kirata bugu ɗaya ta ɗaga,na fashe mata da kuka, sosai ta hau yimin faɗa da nasiha sosai nasiharta ta ratsani na bata haƙuri akan bazan kuma ba,ta bawa mamansu waya wato kakarmu sosai ta yi min nasiha itama tare da ƙwantar min da hankali,sannan ta yi min alƙawarin suna nan zuwa idan matar Aliyu ta haihu,sosai na yi farin ciki don ayadda cikin anty khadija ya ke yau ko gobe ma za ta iya haihu don cikin ya yi girma sosai kamar cikin ƴan biyu. ***** Tun safe da abin ya faru hajiya kaka baki ɗaya taƙi sakin jikinta,duk wanda ya shigo sai ya ganta ta rafka uban tagumi,tana zaune yanzun ma mero na ta takalarta faɗa amman taƙi koda kula ta,koda aka kawo abinci ma mero ta takurawa kaka wai sai ta ci,amman taƙi ce tun abincin safe ne acikinta,tunanin halinda khairat kawai take ciki take,anya kuwa ba wani abu aka yi wa yarinyar nan ba?i'ta dai ta yarda da khairat yadda ta haƙiƙa ba ta tunanin za ta aika ta irin wannsn ta'asar. Sallama har sau uku ƴaƴan hajiya kaka sukayi amman bata ma san sunayi ba,Baba usman da Baba auwalu,suma duk sunji abinda ya faru shiyasa suka shigo sashen mahaifiyar tasu don su ƙara jin komai,don dai su har ga Allah basu yarda da abinda aka faɗa ba,don kaf yaran gidannan ta fisu nutsuwa yadda ya kamata,ba tada surutu ko wata fitina ko kuma rawar kai,don haka dole ayi mamakin hakan. Azabure hajiya kaka ta ɗago tana kallonsu don ta tsorata da shigowarsu,ta tsuke fuska ta ce"ko kuma lafiyarku kuka shigomin ɗaki babu sallama".da faɗanta take musu magana,alamar tana cikin tsananin damuwa da kuma ɓacin rai. Ganin haka yasa Baba usman ya fara magana don duk ya fisu sanin kan hajiya kaka ya ce"hmm umma daman hankalinmu ne wallahi duk a tashe,da wata magana da mukaji mara daɗ?shine mukazo muji gaskiyar lamari"?.ya faɗi hakan kansa yana ƙasa don yasan halin mahaifiyarsu maganar da kai ka ke tunaninba komai ba ce to awajenta komai ce. Ai kuwa sai ta ce"yau naji ikon Allah?to su guntsi fesin matan na ku da suka faɗa muku basu gaya muku komai ba?sai ni kuka zo kuka tsare kuke son in gaya muku?to bari in gaya muku, khairat dai ban yarda da abinda ya faru da ita ba,wata ƙulalliyar aka ƙulla mata don haka yanzu inason ku tashi kuje ku samu munfukan matan na ku,ku ce inji ni na ce"sharri aka yi mata kunji"?. dukkansu sunkuyar da kawunansu suka yi,suna son ƙwantar mata da hankali i'ta kuma taƙi yarda da hakan don sun san da ƙer idan baza ta yi rashin lafiya ba,don yadda take son khairat akaf cikin jikokinta,wai don khairat ɗin sunanta taci. Babu yadda suka iya haka suka fice don taƙi basu damar magana,hankalin hajiya kaka bai ƙara tashi ba sai da ta aiki mero kai mata abincin dare aka ce bata nan,anan ne hankalinta ya tashi sosai ta tafi ɓangarensu khairat ai kuwa taci karo da mama iklima tana jin abinda hajiya kaka take faɗa sai kuwa ta ce"hmm ni fa lamarin yarinyar nan mamaki ya ke bani,yarinya sai kace shaiɗan". azafafe hajiya kaka ta juyo ta ce"akanki wallahi idan shaiɗanun yara ne kina nan dasu,amnan wallahi ba akan khairat ba,ke ni fa wallahi ban ma yard daku ba?yadda kuka tsani yarinyar nan zaku iya yi mata komai don daman ba sonta ku ke ba?amman babu komai Allah yana tare da i'ta,don shi Allah ba azzalumin bawansa bane. [04/09, 18:40] Ummu Maher(Miss Green): Sosai mama iklima ta tsorata sa jin hakan sai dai idan hajiya kaka tasan wata bata wata ba,za tayi maganin shegen akun bakinta. *** "Hajiya daman fa ke ca ki ke son wannan yarinyar amman ni daman cen na tsane ta wallahi,tsana mafi muni arayuwata,yanzu ai gashinan ta fito da halinta afili,sai ku gane halinta a'i". Ce war Bilal wanda ya ke danna computer
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87