Chapter 26
Chapter 26
haɓaka take,wani mugun son Bilal ne ya ke damun jidda ko bacci zata yi idan ta rufe idanuwanta shi take gani,ta rasa wani irin love take masa.uwa uba ga irin taimakon da ya ke mata ba kaɗan bane,yanzu haka ya bada kuɗi a ruguje gidansu a sake musu wani,daga haɗuwarta dashi zuwa yanzu ya kashe mata kuɗi yafi a ƙirga,ko a mafarki ita jidda bata taɓa tunanin za ta auri miji irin Bilal ba,haƙiƙa tafi kowacce mace sa'a.ga wani irin mugun kishinsa da ke cin zuciyarsa sai take ji kamar duk ranar da ta ganshi da wata mace za ta iya yin komai akanshi. **** Ina shiga sashen Hajiya kaka na tarar Mero ta tsaya tana wani muzurai,Hajiya kaka na tsaye da ɗan madoki hannunta,tana bin mero ita kuwa mero sai gwaliya take wa hajiya kaka tana dariya tana mata gwalo tana rufe ido. Sosai abin ya bani dariya,sai kuwa hajiya kaka ta ƙara biyo mero ji ka ke timm,kaka ta faɗi a tsugunne ta kasance a ƙasa hajiya kaka ta saki kuka ta ce"shegiyar yarinya aljana wallahi na ɗauki masifa tun ba'aje ko ina ba". ta faɗi hakan tana fashewa da kuka,sosai na tausayawa hajiya kaka na matso na ɗagata sai kuwa mero ta ce"ai wallahi don baki san yadda na taɓa kada megari bane shiyasa,har rawar banjo na sakasu da na saka musu karara ajikinsu,ni fa wallahi ba'a taɓani in ƙyale".ta faɗi hakan tana yi wa hajiya kaka dariya. Abin takaici abin baƙin ciki yarinya ƙarama na caskare hajiya kaka amman ta kasa magana,ina ƴar dariya ta na ce"to wai kaka me ma ya haɗaki da wannan basa mudiyar yarinyar?ai sai taji miki ciwo wallahi". Da sauri kaka ta ce"ai wannan shaiɗaniyar yarinya ce ta ƙarshe,wai fa daga na ce ta ɓatamin tap ɗina shikkenan take wannan rashin mutuncin".muna cikin maganar yaya Salim ya shigo fuskarnan a murtuke yasha ɗanyar shaddarsa skye blue ya yi ƙyau sosai don shi daman da Babanmu ya ke kama sosai kamar an tsaga kara. Sai kuwa ya ce"a'a Hajiya kaka waye kuma ya taɓa mana ke?".kukan ta cigaba da yi ta faɗa masa duk abinda mero ta yi mata.cikin ɓacin rai ya ce"ke ma kaka ai kinga matsalarki ko wace shara sai ki kama ki ɗakko mana i'ta,ai gashinan yanzu kin ɗebo ruwan dafa kanki". Sai kuwa yaji mero ta ce"caɓɓi ai wallahi ko yanzu idan ta yi min wallahi sai na rama,tsohuwa masifaffiya kawai. . .tun kafin ta ƙarasa maganar yaya salim ya ƙwarfeta ta faɗi ƙasa ta hau kuka wai ya bugeta a cikinta,ƙara haurinta ya yi sai kuwa ta tashi zumbur za ta arta ana kare ya cafkota sai kuwa ta rungumesa taba ce wa"don Allah kaji ƙaina ka ƙyaleni wallahi ƙafafunka da guduma aka yi su". wani irin shork yaji tunda ga kansa har ƴan yatsunsa da sauri ya saketa yana nuna ta da yatsansa ya ce"to oya! ɗauki bocket kije ki ɗabo ruwa a tap ɗinmu ki cika mata komai ko kuma inyi miki tsinannan duka wawiya ƴar ƙauye kawai. Sosai ta zabura ta ɗauki bocket ɗin ta fita tana mita,inno da ke cikin ɗaki tana yi wa ƴar ta addu'ar Allah ya shirya mata mero.tunda mero ta taso bata huta da magana ba ita ce ta shiga gonar wane,ta tsokani wane. Ni na nuna mata yadda ake ɗiban ruwan a tap sannan na wuce sashen maman arman. Tare da maman arman muka fito sashen Hajiya kaka,sai dai fa muna zuwa naga mero tana kallon kaka tana murguɗa baki,kaka kuwa tana tsaye idanuwanta sun cika,na ce"a'ah hajiya kaka bata gama ɗiban ruwan bane?". Kaka ta ce"hmm taya ni baƙin ciki khairat yarinyar nan hawan jini take so ta sakani,yanzu fa tunda ki ka fita babh abinda na gani na alamar an zuba ruwa." sai kuwa mero ta ce"anty khairat don Allah zo muje in nuna miki inda na zuba ruwan"binta na yi kamar raƙumi da akala sai me a masai ta zama take ta zuba ruwan". sai kuwa mero ta fashe da kuka ta ce"wallahi anty tun ɗazu na ke ta zubawa ya ƙi cika"?sai kuwa ta fashe da kuka. Dariya ce ta kamani har da riƙe ciki,lallai na yadda da abinda kaka ta faɗa ƙauyanci da gidadanci sun cika ƙwaƙwalwar mero. *hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba* *GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇* 1, *MU GANI A ƘASA...*🔥 _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚 _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨 _Miss Hajo_ Guda biyar 1k Guda huɗu N700 Guda uku N600 Guda biyu N500 Guda ɗaya N300 *DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC Bank. Domin tura shaidar biya👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇 0817 952 3215 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f *TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨 *YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS* Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: - *Enter your name:* (Cikakken sunanki) *Enter your mail:* (Email ɗinki) *Enter an username* (Sunanki) *Enter your password:* ( misali 12341234) *Confirm password:* (misali 12341234) Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂. *Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye. *Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks. *_AREWABOOKS LINK kai tsaye_* https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3 Masu iPhone Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com *miss green ce👉🏿* [23/09, 16:19] Miss Green🍀: *_🥚ABIN CIKIN ƘWAI..!🥚_* NA💋 *_Ummu maher(miss green🍀)_* GAWURTATTU BIYAR✨✨ 27🟨28 . . . .duk wanda ya ke wajen sai da mero ta bashi dariya,har ita kanta hajiya kakar wacce aka yi wa laifin,tsabar Ƙauyanci mutum ya yi ta zuba ruwa acikin shadda kuma ya ce wai ta ƙi cika?. babu yadda na iya dole ni dai na nunawa mero komai,Ta kalleni tana dariya ta ce"la anty ashe mahaya ce ban sani ba?sai kuwa ta fashe da kuka".rarrashin mero na dinga yi hajiya kaka ta ce"ai da kin rabu da ita sai inga duka na za ta yi kome da ta wani Ƙwalalomin manyan idaniyanta wanda inno ta shafa mata,amman ni dai Ɗan uwana sale ba haka ya ke ba". tana faƊar hakan ta koma Ɗakinta tana mita,naja hannun mero muka wuce sashenmu,a farlo na tarar dasu nadiya suka wani kalleni sheƘeƘe sannan iman ta ce"he!this girl ina zakije mana da wannan mahaukaciyar yarinyar"?.ta faƊi hakan tana mana wani kallon banza. na buƊe baki zanyi magana sai kuwa mero ta yi caraf ta ce"ah tsaya waye Mahaukacin?". Da sauri nadiya ta matso kusa da mero ta ce"ke!ke!!kece mahaukaciyar ko dukanmi zaki yi?ƴar Ƙauyen banza kawai". "A'ah gyara zancenki ai Ɗan Ƙauye shine jahili me zagin mutane amman fa ni ba ni bace,idan kina neman mahaukaciya ki hau saman bene zaki same ta". Sai kuwa nadiya ta kalli saman benen,kuma mahaifiyarta na saman kamar mero tasan tana sama Ɗin. Wani banzan mari nadiya ta bawa mero
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87