Chapter 9
Chapter 9
Ummy tai saurin cewa "Baba dama inaso nai maka wani tambaya" Ya dawo tareda zama kan benchn dake gefensu yace "Allah yasa na sani 'yata" Ta nisa tace "Baba ranan na tab'a ganin wani mara lapia a gidan nan, a wani d'aki yana zaune akan keken guragu. Wai shi wanene" Nan da nan fara'ar dake fuskan Baba ya kau, ya d'ago yana kallansu yace "Sunanshi JAMALUDEEN, shine babban d'a ga Alhaji Surajo, nakai shekara goma a gidan nan ina aiki tareda Alhaji, lokacin danazo nasamu Jamaludeen yanada shekara goma sha shidda, Alhaji Surajo mutun ne mai san mutane da kuma tausayin talakawa" Ummy da Laurat suka zubamai ido suna kallanshi ya cigaba da cewa "Bakuga ma'aikatan dake gidan nan ba, saboda tausayi dayake dashi yasa yaketa d'aukan marasa k'arfi da marayu suna aiki yana biyansu. Jamaludeen yaro neh mai hazak'a da tarbiya gasan mutanen..... Ku biyoni a page na gaba dan jin cigaban labarin JAMALUDEEN UmmyAbduol✍🏻 [3/12, 8:24 AM] +234 806 215 4020: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Indo Magulmaciya(Aisha Abduolqadeer)* wannan shafin naki neh kyauta Page 12 "Jamaludeen yaro ne mai hazak'a da tarbiya ga son mutane, ya samu tarbiya mai kyau daga Iyayensa, da wuya kaga Jamaludeen yayi zagi ko wani abu daya sab'a k'aida." Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "Yayi karatunsa a nan k'asa nigeria, yayi saukar alkurani tun yana aji hud'u a sakandari, daga bisani mahaifinsa ya turasa k'asar misira ya k'arashe sauran karatunsa..." Hawaye suka gangaro ma Baba yasa hannu ya share yace "Ban tab'a ganin abokin fad'an Jamaludeen bah, yaro ne mai ladabi da biyaiya, yana matuk'ar san Iyayensa kamar yanda suma suke sanshi sosai. Ya d'au kowa d'aya a gidan nan, baya nuna banbanci dan mu masu aiki neh.." Laurat tayi saurin k'atseshi da cewa "To Baba wai meya samesa neh?" Ummy ta zungureta tana hararanta "Keh kin cika garaje" Baba ya kallesu yana murmushi "Da gaskiyarta Ummy gwara data tambaya, dan idan na tsaya baku labarin kyawawan hali irin na Jamaludeen zamu kwana neh a nan mu yini bamu gama bah" "Yauwa Baba ashe ka fahimta" cewar Laurat tana hararan Ummy "Shekara uku kenan da fara rashin lafiyarsa, bayan kamalla makarantarsa da shekara d'aya ya had'u da wannan tsautsayin a hanyarsa ta zuwa kaduna yayi hatsari." "Hatsari??" Ummy ta maimaita tana kallan Baba gabanta na dukan uku uku "Kwarai y'ar nan, hatsari ya samu akan hanyarsa ta zuwa kaduna, lokacin da aka kawosa duk an d'auka baida rai sai daga baya likitoci suka tabbatar da yanada rai" Ummy ta sauke ajiyar zuciya tace "Wannan wane irin ciwo neh haka? Baba wallahi idan ka ganshi zakayi zatan gawane dan ko kyafta ido bayayi" Murmushin takaici Baba yayi yace "A hakan ya samu lapia kenan, dan baki gansa baneh da. Ba k'asar da ba'a kaishi ba anma ba wani cigaba, a nan na yarda da maganan nan da akecewa ba komai dukiya ke siya bah" "Lallai wannan bawan Allah yaga jarabawar rayuwa" Cewar Ummy tana rik'e hab'anta Baba yace "Kwarai da gaske Ummy, yanzu ina gatan yake? Ina dukiyar da mahaifinsa ya tara? Ina ilimin dayake dashi? Duk kinga basu masa anfani bah" Laurat ta gyara zama tace "Anma kuma Baba sai naga kamar Iyayensa basu damu dashi ba yanzu" D'an dariya yayi yace "Ina! aiko shi Iyayensa suka damu dashi, har yau har gobe yana cikin gata kamar yanda yake dah. Kunga dai duk dukiya da matsayi irin na mahaifinsa hakan bai hanashi kullum da safe shi da kanshi yake zuwa yanama d'an nasa wanka ya shirya shi, bai yarda wani ya masa wannan bah. Ko turawan nan da kuka gani anfaninsu kawai kula da lokacin shan maganinsa dakuma abincinsa" "Allah sarki yabani tausayi, Allah ya bashi lapia" cewar Ummy tana girgiza kai cikeda alhini Baba da Laurat suka amsa da Ameen. Godiya suka masa ya mik'e ya koma bakin aikinsa jiki a sanyaye Suma kicin suka nufa suka cigaba da ayukansu. Da daddare tunanin Jamaludeen neh ya cikama Ummy zuciya, sosai labarinsa ya bata tausayi har take tunanin bashi nata gudun mawar a rayuwarsa ko Allah zaisa a dace. (Kujimin k'arfin hali) Tunani ta soma kan yanda zata b'ulowa alamarin a haka bacci ya d'auketa. Washe gari da safe kasancewar ranar juma'a ce da wuri Ummy ta tashi, yau ana public holiday dan haka Hajiya da Mabrookah suna gida, sai wuraren sha d'aya na rana suka fito daga d'akunan su, saman ta haura bayan ta gaishe su ta soma aikinta, d'akin Hajiya ta gyara farko sannan ta zarce na Mabrookah shima ta gyara tsaf. Fitowa tayi ta juya tana kallan k'ofar d'akin da Jamaludeen d'in ke ciki, wata zuciyar na ingizata akan ta shiga wata zuciyar na hanata. Hajiya ce ta hauro ta tarar da ita a haka, sunanta ta kira tayi firgigit ta juya tana kallanta tareda rusunawa "Meh kikeyi a nan a tsaye?" Gabanta ya fad'i ta dake tace "Fitowa na kenan daga d'akin Aunty Mabrookah na gama gyaran" Hajiya tad'anyi jim sannan tace "Yau kibar gyaran b'angaren Alhaji tunda yana nan" Ta kalli Uniform d'in jikin Ummyn tace "Kije ki sauya kaya kizo ina jiranki a d'akina" To tace ta sauka dasauri ta shiga d'akinta, atamfarta ta sallan bara ta ciro daga k'asan ghana must go d'inta ta saka tad'an murza farar hodan dake cikin kayanta, gaban madubi ta tsaya tana kallan kanta, wasu hawaye ne suka gangaro mata, lokaci guda ta fashe da kuka tareda jingina kanta a jikin Mirror tana cigaba da kuka "Ka tafi ka barni Ya Bilal a lokacin da nafi buk'atarka" Zoben hannunta ta soma murzawa tana cigaba da hawaye "Kayimin abubuwa da dama a rayuwa nida Iyayena wanda bazan tab'a mantawa dashi ba, ciki kuwa harda sutura" Tad'anja rigar dake jikinta tana kallan fuskanta a madubi tana hawaye, ta dad'e a haka sannan ta shiga toilet ta wanke fuskanta ta fito ta nufi d'akin Hajiyar, a corridor tayi kicibus da wad'an nan turawan maza sun gunguro Jamaludeen suna k'okarin sauka dashi. Binsu da ido tayi tad'an matsa gefe suka wuce, Hajiyar ta samu nan d'akinta, a nan Hajiyar ke sanarda ita cewa zasu fita ne takeso suje taro. Murmushi tayi tace "Tho" Kallan kayan jikinta Hajiyar tayi tad'an yatsine fuska ta juyar dakai, d'akinta ta koma ta d'auko hijab tasa ta fito daidai nan Hajiyar itama ta sauko. Mabrookah wacce shigowanta knan gidan ta kalli Hajiya tace "Mami naga Jamal a waje ina za'a kaisa?" Hajiya tace "I want to spend this day with my son" Ta k'are maganan tana murmushi, girgiza kai Mabrookahn tayi tareda yatsine fuska "I'm hungry dana biku" "Aa kiyi zamanki ga Ummy zata rakani" Ta nuna Ummyn dake tsaye gefensu tana muzurai "What?, yanzu Mami da wannan k'azamar zaki salan ta shafa masa wani cutan dama gashi muna fama" Hajiya ta had'e rai "Banasan Haka Mabrookah behave ur self whats all dis" Zumb'ura baki tayi ta haura sama tana gungunai, ita harga Allah batasan Yarinyan nan she dnt knw why. Hajiya ta juya ta kalli Ummy tace "Kiyi hak'uri ki kyaleta wata rana zata daina" Kai Ummy ta d'aga suka fita, already sun tarar har an sakashi a motan Hajiyar, Mercedes benz E350 sai d'ayan kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82