Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

shaidata saboda Hajiyan tamai bayaninta, Cikin gidan ta nufa kai tsaye a k'ofar falon ta soma knocking chan aka bud'e wata y'ar budurwa black beauty ce tsaye sanye da Legins bak'i daidai guiwa da farin top gashin kanta mai tsaye, d'an rusunawa Ummy tayi ta gaidata "Daga ina?" Cewar budurwar Ummy ta k'ara duk'ar dakai tace "Hajiya ce tace na dawo yau" Yatsine fuska tayi tana kallanta up and down "Kice y'an maula ne, tho Hajiyar na bacci" Kalmar da budurwar ta kirata dashi sosai ya b'atamata rai, batace komai ba ta k'ara d'ukar dakai. Tsaki taja ta bugo kofan, hawaye suka taru a idanunta a hankali ta juya ta soma tafiya, wata y'ar dattijuwa ce ta tareta tana tambayanta lapia, Bata b'oye mata komai bah, Tsohuwar tayi murmushin takaici. "Badai Hajiyar bace tace kizo" Kai Ummy ta gyad'a, Tsohuwar tace "Ki nemi waje ki zauna, anjima idan Hajiyar ta sauko zan mata magana" Godiya taima matar ta samu waje chan wajan gate ta zauna tana k'ara bin Gidan da kallo. Tana nan zaune wani ya shigo gidan shida wata daga gani likita ne sabda yarinya dake binshi a baya kayan nurses ne a jikinta ta rik'e wani folder. Suna shigowa kai tsaye cikin gidan suka shige. Binsu da kallo Ummy tayi tana tunanin kodai Hajiyarce bata lafiya shiyasa aka hanata ganinta. Takai kusan awa d'aya sannan taga fitowar likitan tareda Hajiya, mik'ewa tayi dasauri ta k'araso wajan daidai lokacin sun gama magana da likitan. "Ina kwana Hajiya" "Aa Ummy lapia lau, har nayi tunanin bazaki dawo bah" Kan Ummy a k'asa tace "Aa ai tun d'axu na shigo ance ne baki tashi bah" Hajiyar ta soma tafiya sannan tace "Biyoni" Falon suka shiga, wani d'aki dake nan k'asan Hajiya ta kaita tareda shaida mata nan ne d'akinta. D'akin ba k'aramin burge Ummy yayi ba duk da ba wani abubuwa bane a d'akin, Gado ne d'an k'arami sai wardrobe dukansu Pink, daga gefen hagu akwai wata k'ofa da alama Band'aki neh. Kayanta ta aje suka koma falo itada Hajiyar, Kan Carpet ta zauna ita kuma Hajiyar ta hakince a kujera "Inaso ki natsu kiji abinda zan fad'a miki" "Tho Hajiya" Hajiya ta gyara zama tace "A tsarina banasan Katsalandan ma'ana banasan mutum na shiga hurumin da ba nashi bah, Sannan ki tsaya a matsayinki na y'ar aiki ba ruwanki da shiga inda ban umarceki bah." Ummy ta k'ara duk'ar dakai tace "Tho Hajiya" Budurwan nan ne ta sauko tana wani juyi da alama wak'a takeji dan ta rufe kunnuwanta da katon earpiece, Tana ganin Ummy tayi saurin zame earpiece d'in daga kunnenta "Danace ki tafi wato baki tafi ba koh" Hajiya tayi saurin cewa "Haba Mabrooka, why kike koranmin mutane idan sunzo gurina" Ta turo baki tareda zama tana hararan Ummy Hajiya ta nuna Budurwar tana cewa "Ga y'ata sunanta Mabrooka sannan inada d'a namiji sunanshi Jamaludeen" Kai Ummy ta gyada har lokacin kanta a k'asa "Mami me tazoyi gidan nan" "Aiki tazoyi" Hajiya ta bata amsa Mabrooka ta gyara zama tana murmushi "Yauwa Mami kamar kinsan Wallahi banasan aikin wannan Baban bata iya gyaran d'aki ba" Murmushi Hajiya tayi "Babu damuwa" Ta maida dubanta ga Ummy "Aikinki a gidan nan shine gyarama Mabrooka d'akinta da nawa sai ki rink'a taimaka ma Baba da ayukan da takeyi" "Tho Hajiya" Hajiya ta k'ara da cewa "Karki manta da ki tsaya a matsayinki" Kai Ummy ta gyad'a Hajiya ta sallameta ta koma d'aki. Bayan azahar Mabrookah ta shigo d'akin tana yatsine fuska "Sai ki taso muje in nuna miki d'akin ki" Bah musu ta mik'e suka soma zagayawa, Sosai gidan ya burge Ummy tanata kallo harda sakin baki. Daddare bayan Alhajin gidan ya dawo Mami ta gabatar da Ummy wajanshi, yayi na'am da zuwanta nan Mabrookah ta shiga k'orafin ita hakanan taji yarinyan bata mata bah, Lallashinta Mami tayi dakyar ta amince da Ummyn. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 9 Washe gari Ummy na sallan asubah ta fito daga d'aki dan soma aikinta, tsayawa tayi a falon k'asa tana k'arema falon kallo dan batasan ta inda zata fara bah. Wata y'ar budurwa wacce bata wuce sa'arta bah ta shigo falon sanye da riga blue iya guiwa da bak'in wando, Ummy tayi mata murmushi tareda gaidata. Yarinyar ta amsa tana cewa "Jiya na ganki Aunty Mabrookah na zagayawa dake, kema aiki zaki fara?" Kai Ummy ta gyad'a tace "Eh jiya nazo, kema aiki kikeyi" "Eh ni ina b'angaren kicin neh, Sunana Laurat" Murmushi Ummy ta sakar mata tana cewa "Ni kuma sunana Jaleelah anma Ummy ake cemin, Hajiya tace zan rink'a gyara mata d'aki da kuma Mabrookah sai..." Toshe baki Laurat tayi ta waiga bayanta ta juyo tace tareda sassauta murya "Kada kija ma kanki dan Wallahi Aunty Mabrook batada mutunci. Wai dole sai an rink'a kiranta da Aunty" Da mamaki Ummy ta kalleta "Aunty kuma?" Laurat ta gyad'a kai tace "Umm barinje b'angarena zamu had'u anjima wajan amsar abinci" Bata jira mai Ummyn zatace ba tabar wajan dasauri, d'aki ta koma ta zauna dan tasan yanzu su Hajiyan basu tashi ba balle tayi aikinta. K'arfe bakwai da rabi ta fito, Hajiyar ta hango da Mabrookah kan dinning suna breakfast, dasauri ta k'arasa ta rusunna ta gaida Hajiyan, da fara'a ta amsa, ta juya ta gaida Mabrookah daketa cika tana b'atsewa kauda kai Mabrookah tayi bata amsa bah, Hajiya tad'anyi murmushi tace "Yau zaki fara aikinki, inaso ki kasance mai gaskiya sannan ki tsaya a matsayin ki. ina fata kin ganeh" Kai Ummy ta gyad'a tace "Insha Allahu Hajiya zan kiyaye" Mabrookah ta mik'e tad'au handbag dintah tana cewa "Mami zan tafi" ta juya ta kalli Ummy cikeda tsana tace "Make sure kin gyara min d'akina yanda nakeso dan idan bai gyaru ba na dawo sai kin sake" taja dogon tsaki tabar falon tana surutai, ga mamakin Ummy sai ganin Hajiyar tayi itama ta mike tad'au handbag dina da keyn mota ta fita. girgiza kai kawai tayi ta mik'e ta shiga store tad'au tsintsiya, mopper da parker ta haura sama zuwa d'akin Mabrookan. Batsa batsa ta sameshi kamar ba d'akin mace bah, wani dogon tsaki taja tana bin d'akin da kallo "Ji d'akin mace, sai shegen k'azanta" Kayan dake zube a k'asan d'akin ta soma kwashewa, sannan ta cire bedsheet d'in dan shima yayi dati sosai, Wardrobe ta duba ta ciro wani ta shimfid'a, dak'in ta gyara tsaf tayi shara tayi mopping tareda fesa room freshner, nan da nan d'akin yad'au kamshi, toilet ta shiga ta wankeshi tas ta kwashe kayan dake laundary basket ta fito dasu, tana saukowa k'asa ta had'u da wannan likitan data gani da nurse suna haurowa, gefe ta matsa ta gaidasu sannan ta sauko. Mamaki neh sosai ranta, tho ko meh wad'an nan mutanen ke zuwa yi gidan kullum? Da wannan tunanin ta zagaya chan bayan gidan ta soma wankin kayan, wani tsoho ne ya zo wajan rik'e da bokiti da wasu kaya, tsoho ne sosai dan a kalla zai kai shekara saba'in, gaidashi tayi ya amsa ya soma kici kicin fara wanki da alama kayanshi, k'arasawa tayi inda yake ta rik'e bokitin tace "Baba kawo na wanke maka" Ya

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82