Chapter 74
Chapter 74
kallo d'aya ya mata ya kauda kai gefe, Ledan Takeaway da sukayo ya aje mata nan falon ya haura sama, binsa da harara tayi tare dajan tsaki ta mik'e ta d'au ledan tana dubawa. K'amshi ne ya masa sallama yana haurawa Falon, jin motsinta a kitchen yasa ya k'arasa cikin sand'a, tuwon semo ya samu tana tuk'awa tana haki kamar wacce tayi gudu. Tausayinta ne ya kamasa ya k'arasa ya zagaye k'ugunta da hannunsa yana mata sannu, murmushi ta masa tana cigaba da aikinta. Tayata ya soma yi har suka gama, ta had'a komai a tray ta mik'a masa tana turo baki "Dan Allah kakai ma Abba, naji baici wani abinci bah" Farinciki ne ya lullub'esa mara lissaltuwa, ya amsa Trayn "Thank uh so..." Tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai, a sanyaye ya fito daga kitchen d'in ya koma side d'in Abban, Ammi na ganin Abincin ta soma hawayen farinciki "Son Allah ya maka Albarka, ka samu mace ta gari. Allah ya baku zuri'a ta gari" A hankali yace Ameen Sosai Abba yaci abincin dan ya masa dad'i sosai, Saida ya gama sannan ya wanke hannu, Hannu yasa a aljihun Rigansa ya ciro tsabar kud'i masu yawa ya mik'a ma Jamal d'in "Gashi kaba surukata, Allah ya mata albarkah" Ya amsa yana murmushi tare da godiya. Koda ya koma ya samu tayi wanka ta kwanta tana bacci, sosai yayi mamakin Saurin baccin Ummy kwana biyun nan. Gefenta ya kwanta ya shige jikinta shima nan da nan bacci ya d'aukesa. Ba ita ta farka ba sai bayan la'asar, salati tayi ta mik'e ta shiga toilet tayi wanka ta fito tare dayin sallah. Ranar gaba d'aya hidima tayi da sirrukanta, har Mamaki Abba da Ammi suke na irin karramasu da Ummyn keyi. Albarka ko tasha shi wajan Iyayen mijin nata dashi kansa Jamal d'in. Washe gari Areefah ta diro garin zaria itada da drivern su Abban, k'arfe sha d'aya na safe a gidan ta musu tare da taimakon Jamal dayayi tama Drivern kwatance. Sosai tayi murnan ganin iyayen nata, bayan ta huta Ammi ta umarceta data je side d'insu Ummy ta gaishe su, hakan ko akayi, a falon k'asa ta had'u da Mabrookah ta gaisheta, dakyar ta amsa tana yatsine fuska. Areefah ta tabe baki dan a rayuwarta babu abnda ta tsana kamar wulak'anci, Sama ta haura a falo ta had'u da Ummy itama kwance kan kujera Ummy najin sallamanta ta mik'e zaune tana mata murmushi, ta k'arasa ta zauna tare da gaisheta Da fara'a Ummyn ta amsa tana ta kallanta ganin tsantsar kamar da suke da Jamal kamar an tsaga kara harma tafi kama da Jamal fiye da Areef, Ummy ta mik'e tana cewa "Barin samo miki wani abu" Tayi saurin cewa "No Aunty Thank uh. I'm Ok" Ummy tayi kitchen tana cewa "Aa wallahi ai bazai yuwu kixo wajena bakici komai bah" Ya shiga kicin ta kawo mata drinks da 'yan kayan motsa baki. Yanda Ummyn ta tarbeta yasa ta saki jiki ta soma mata hira, Areefah akwai Barkwanci. Daga k'asa Mabrookah keta jin dariyansu, ranta ya k'ara b'aci lallai idan tayi wasa sai Ummy ta kwace mata mutane. Taja dogon tsaki ta shige d'akinta. Tare da Ummy sukayi Sallah, Da taimakon Areefahn ta had'a ma su Ammi abinci a Warmers Areefah ta taimaka mata suka kai. Ammi da Abba sai albarka suke saka mata. Bayan ta fita Areefah ta zauna kan dinning tace "Abba nan gidan wanene?" Ammi ta bud'e baki zatayi magana Jamal da Areef suka shigo falon da sallama, kurrrri tama Jamal tana kallansa, ganin yana kama da Areef, ya k'araso wajan ya tsugunna ya gaida iyayensa. Abba da Ammi suka amsa da fara'a, Itama ta gaidasa ya amsa cikin fara'a yana cewa "Uh welcome sister" Murmushin yak'e ta masa ta d'au spoon d'in gabanta ta saka cikin abincin tana kallansa k'asa k'asa. Ganin sun zauna kan dinning d'in shida Areef dake ta hararanta yasa tad'an kalli Ammi cikin rad'a tac "Ammi wanene wannan" "Just eat" Ammi tace mata. Kasa sakewa tayi sai kallan Jamal take dake ta hira dasu Ammi suna cin abinci. Bayan sun gama Abba ya mik'e ya koma falo, Areefah na ganin haka ta mik'e dasauri ta bisa, Kusa dashi ta zauna tana tura baki "Abba were are we? And hu is he" Ta nuna Jamal dake tahowa shida Areef, Murmushi kawai Abba yayi, saida duk suka zazzauna sannan Abba ya soma ba Areefah labarin duk abinda ya faru da kuma abinda ya faru sanda aka kamasa. Batayi wani mamaki bah ganin tsantsar kamar da yake da 'yan gidansu, Hamdala tayi da k'arfi har saida duka suka juya suna kallanta, ta d'aga Hannu sama tana cewa "Alhamdulillah Thank uh Allah for accepting my Prayers" Sosai ta basu mamaki, ta kalli Areef dake ta kallanta tace "Kullum ina Addu'a Allah bani wani Bro gashi ya bani" Ta nuna Areef fuska a had'e "Mugu to daga yau uh are no more my Bro" Gaba d'aya dariya sukayi banda Areef da ransa ya gama b'aci "Dama ke wake k'anwa dake, jibeki k'azama kawai" Ba shiri ta fashe da kuka "Abba kajishi koh" Ammi ta k'arbe da cewa "Kun had'u zaku fara koh, da baku tare kwana biyu har bakina yayi shiru" Abba yace "Karka sake cema Babyna k'azama, kaga nan k'azami" Jamal sai kallansu yake da sha'awa tare da farinciki. Yace "Zo kiji" Ba musu ta dawo kusa dashi ta zauna, ya goge mata hawayen fuskanta yana murmushi "I'm now ur Bro ki kyalle Areef babu ruwanmu dashi" Gwalo tama Areef ya mik'e "Allah kikayi wasa saina mangareki" "Iyeh!" Cewar Abba "Tho Mangaretan" Ya fita daga falon yana huci, Jamal yace "He's ur brother ki daina masa rashin kunya kinji" Ta tura baki tana shagwab'a "To bashi ke tsokanata bah" Yanda take shagwab'a ta tuna masa da Wife d'insa "How old are you?" "17yrs" tace Jamal yayi dariya "Woaw! Ashe big gal ce" Tayi dariya tana cewa "Bro su waye wanda na gani a wanchan side d'in" Murmushi yayi batare da ya bata amsa bah, Ammi tace "Matansa ne" Baki bud'e tace "Duka biyu" Ya sake sakin murmushi, tab'e baki tayi tace "Nidai Faran tafi kirki, b'akan batada kirki bab...." Ammi tayi saurin cewa "Kull! Karna sake ji" Ta tura baki, Jamal ya mik'e yana cewa "Abba barinje naga Mifzal coz gobe za'a koma court" Abba yace "Eh yakamata, muma ana fitowa daga Court d'in zamu koma" Gabansa ya fad'i baice komai bah ya fita daga falon. Bai samu shiga side d'inshi bah ya wuce station d'in. A office d'in ya had'u da Ram, bayan su gaisa Mifzal yace "Komai dai zaizo k'arshe gobe insha Allahu" Jamal yayi murmushi yace "Pls ko zan iya ganin su Mamin" Dogon tsaki Ram ya saki "Wani me matar nan ta maka neh kabi ka damu da ita haka?" "Ko ba komai ta raine ni ta rik'eni kamar d'anta" Mifzal yayi saurin cewa "Anma ba tsakani da Allah bah koh" Ram ya d'aura da cewa "Wadda ta iya sa a kashe mijinta, kai ko ba mijinta ba ma mutum fah" Ran Jamal idan yayi dubu ya b'aci, ya mik'e yace "Banasan cin fuska idan bazaku taimaka min ba ku bari" Fuuu zai bar office d'in Ram yayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82