Skip to content

Chapter 81

Chapter 81

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

kama hannunsa suka zauna a falon, itama Ammi ta zauna. Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Kamar yanda na baka labarin abinda ya faru damu shekarun baya har hakan yayi sanadiyar b'atanka. A lokacin da Mahaifiyarka ta tafi dakai ni kuma suka b'alle k'ofan suka kamani sukamin duka a nan suke shaida min wani Alhaji Dauda ne ya aikosu su kasheni. Alhaji Dauda Abokin kasuwanci na neh, tare muka shiga harkan kasuwanci dashi, sanda muka fara Allah ya soma bud'amin sosai sai ya soma min zagon k'asa dajin haushina. Shima a lokacin yana samu saidai ba kamar ni bah.. Tun sanda na bud'e shagon zinari tsanar dayake min ya yawaita, har takaiga ko na gaishe shi baya amsawa." "Tun a wannan lokacin na gane ba masoyina baneh. Mutanen daya aiko suka harbeni na suma, sai sukayi tunanin na mutu ne suka tafi. Alumma annabi suka taimakeni aka kaini asibiti. Kwana hud'u da faruwan hakan mahaifiyarka ta dawo, babu wanda na fad'ama abinda suka shaida min sai matata. Ita ta cigaba da kula dani a asibiti saida na shafe wata hud'u sannan aka sallameni" "Kwana na Uku a gida a ranar na hud'u na fita kasuwa, abin mamaki duk shagunana wasu sabbin ma'aikata na samu nan na soma fad'a akan waya basu izinin shiga shagona, a nan sukama Alhaji Dauda waya sai gashi yazo yake shaida min Shaguna mallakinsa ne ba nawaba. Nayi mamaki sosai na dangana ga Office d'in 'yan sanda, bayan nakai k'ara aka umarci wasu 'yan sanda su taho dashi. Ina nan zaune suka zo dashi aka d'au statement d'inmu akace naje sai gobe na dawo. Washe gari dana koma abin mamaki 'yan sandan suka nuna basu sanni bah haka zalika basu san zancen bah har suna k'okarin kulleni" Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "370million shine darajan kayan shagona, Ba takaicin rashin kud'in nake bah, takaici na d'aya yanda ya hak'ikance akan rashin gaskiya. A lokacin babu Ofishin 'yan sandan da banje bah anma duk magana d'aya ce. Haka na had'a sauran kud'in danake dashi muka haura k'asar Masar da Mahaifiyarka, a chan na cigaba da kasuwanci cikin ikon Allah abubuwa nata hab'aka" "Bayan dawowa na naji labarin ta dalilin dukiyata Alhaji Dauda ya zama babban d'an siyasa wanda a halin yanzu yake da babban matsayi a siyasar da muke ciki yanzu, shine nad'au alwashin saina d'au fansan abinda yayi min. Anma kash babu wani jami'in tsaron daya mara mani baya sai wani guda d'aya dake cikin garin kaduna, shi kuma bana samunshi sai dare lokacin ya dawo aiki. Duk sanda kaga nayi fitar dare Kaduna nake zuwa duba D'an sandan sannan kuma mu tattauna akan abinyi, ta bakinsa na samu labarin har yanzu Alhaji Dauda bai daddara ba yana cigaba da kwacen dukiyar mutane batare da ance uffan ba saboda d'aurin gindin dayake dashi a gwamnati" Jamal ya sauke ajiyar zuciya cike da gamsuwa da maganganun Abban nasa, yace "Abba mai zai hana nayi ma Mifzal magana, nasan insha Allahu za'a dace, kuma kaga IG k'anin Abbansa neh" Ammi tace "Jamaludeen kenan babu wani babban d'an sandan da ba'ayi masa magana bah" Abba yace "No ki barsa ya jaraba wata k'ila a dace" Ran Jamal ya sosu sosai da jin labarin da Abban ya bayar "Insha Allahu Ammi za'a dace, In Allah ya yarda K'arshen Alhaji Dauda yazo kuma wallahi bai isa yaci kud'in Abba bah sai ya amayo su" Abba ya mik'e yana bubbuga kafad'ar Jamal "Allah ya bada sa'a my Son, go and have some rest" Saida safe ya musu ya koma d'akinsa cike da tunani kala kala. Washe gari da asubah Ummy ta sulale ta koma d'akinta, Shima bai tashi da wuri bah sai k'arfe goma, Koda ya fito Ya samu su Ammi da Mama zasu Kasuwa siyaiyar kayan da Maman zata buk'ata a sabon gidan nata. Gaidasu yayi tare da musu sallama suka fita. A ranar ya nemi izinin Abba na zuwa Zaria don su gama da Mifzal, ba musu Abba ya amince masa da Bilal suka tafi, sun samesa sun masa bayani, ba tare da b'ata lokaci bah ya kira k'anin Abbansa ya masa bayanin abinda ke faruwa. Nan ya shaida musu su had'u a Abuja ranar Sati, sunmasa godiya sosai basu dawowa ba sai washe gari, a ranar suka d'auko Umman Bilal basu d'auko Bahar ba dan yana karatu a ABU kuma yana tsaka da karatu. Ranar da suka iso Mama da Umman suka tare a sabon gidansu, Godiya wajan Umma da Bilal ba'a magana dan sunyi matuk'ar farinciki sosai. Kwana biyu tsakani Mifzal ya iso a ranar suka samu ganawa da IG gaba d'ayansu harda Abba, ba'a dau lokaci ba aka fara Bincike kan maganan. Cikin satin Ummy ta tare a nata gidan Bakin Jamal har kunne. Soyayya Jamal ke nunama Ummy nasa kamar ba gobe, yana tattalin abinsa sam bayansan abinda zai tab'a matar tasa. Kyautatawa babu irin wanda Jamal bayama Sarakan masa. *Bayan Wata Biyar* Cikin Ummy yayi girma sosai yakai watan haihuwa, kulawa babu irin wanda bata samu daga wajan Mijinta da surukan nata harda su Mama. Dole Ammi tasa Jamal ya d'aukota ta dawo kusada Ita, cikin yayi nauyi sosai har anata tsammanin ko 'yan biyu ne anma duk scanning d'in da'akai d'aya yake nunawa. Hakan yasa kullum da yanma Jamal ke sata gaba sai sun fita road work duk bayan la'asar. Yauma kamar kullum sun fito suna tafiya a hankali sai sannu yake mata tanata tura baki, kamar daga sama taji an kira sunanta "Ummy!" Juyawa tayi dasauri wa zata gani in ba Laurat bah, da mamaki Ummy tace "Laurat kece" Da murmushi ta k'araso inda suke tace "Ni ce Ummy ashe da rabon zamu sake had'uwa" Ta gaida Jamal ya amsa fuska a sake dan ya ganeta, tace "Ina aiki ne a nan bayan layin, Allah sarki tun bayan barina Gidan Mami bamu sake had'uwa bah" Jamal yace "Yanzu ku muje mu k'arasa gida sai kuyi Hiran dakyau" Ba musu Laurat tabisu har gida, Ammi ta amsheta dakyau suka k'ulle a d'aki sunata hira. A nan Laurat ke shaida mata tasan duk abinda ke faruwa a gidan ta bakin wani Mai gadi dake unguwar d'an anguwansu ne dake chan kaduna. Ta sauke ajiyar zuciya tace "Gaskiya Mami batada imani, zataga K'arshenta insha Allahu" Ummy tayi murmushi dai batace komai bah, Laurat tace "Wai meya faru da Mabrookah dan kwanaki na ganta a wani guest house a nan garin, nifah yanda na ganta kamar karuwanci take" "Karuwanci?" Cewar Ummy tana zare ido "Wallahi kuwa, bakiga ma kayan jikinta bah" "Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun" cewar Ummy tana dafe da goshinta, ta cigaba da cewa "Gaskiya Mabrookah ta b'ata wayonta, Allah ya kyauta" Laurat ta amsa da Ameen suka chanza hira, tad'an dad'e a gidan sannan ta tafi bayan tama Ummy kwatancen Gidan da take. Bayan kwanaki Akayi shar'iar Alhaji Dauda da Abba kuma Alhamdulillahi shari'a ta tafi yanda akeso dan su Abba sunyi nasara. Bayan fitowa daga shar'iar wanda Ram ya kasance Lawyern Abba, nan suka samu chinchirindon mutane masu son abi musu hak'insu wajan Alhajin Daudan, nan aka sanar dasu kowa za'a bashi hak'insa sukayi ta godiya. Kwana biyu tsakani Akama Mifzal k'arin girma tare da transfer ya koma Abuja,

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82