Chapter 64
Chapter 64
kalli Ogan "Me muka muku? Kud'i kukace kuma na kawo ku sake mu mutafi mana" Ogan ya saki wani irin dariya tare da matsowa inda aka ririk'e Jamal d'in, Fuskanshi yasa hannu ya d'ago, Jamal yayi saurin fizgewa yana kallansa rai b'ace. Shiko Ogan sake fashewa da dariya yayi "Ba'a bamu izinin sakin ku bah har yanzu" "Waye ya saku?" Jamal ya tambayeshi cikin fad'a Baice masa komai bah ya juya ya fita yana dariya, duka mutanen nan biyu sukama Jamal kamar ba gobe, Kuka da Ihu had'e da magiya babu wanda batayi bah. Saida suka masa lis sannan suka sake d'auresa suka fita. Da rarrafe ta matso inda yake dan ita basu d'aureta bah, kansa ta d'aura kan kafafuwanta ta fashe da kuka tana shafa sumar kanshi. Dakyar ya iya d'ago fuskanshi yana girgiza mata kai "Ban kasance miji nagari a gareki bah I'm s..." Tayi saurin rufe masa baki da hannunta, Rigan dake jikinta ta yaga k'asan ta soma goge masa bakinsa da hancinsa dake jini har lokacin bata bar kuka bah. Ya lumshe idanuwansa dan kukanta jinshi yake har cikin ransa. **** Duka sosai Mifzal yasa akama wannan dattijon da Barr. Ishaq dan ransa ba k'aramin b'aci yayi bah. MTN office ya koma suka sanar dashi sun kasa samun location d'in wayan dan a kashe take. Ransa ya k'ara b'aci ya bar wajan shida Ram suka nufi gidansu Jamal. Basu samu kowa ba sai Mabrookah, cikin mamaki Ram yace "Mabrookah ina Mami?" Ba tare da wani tunani ba tace "Basanan sunje neman Ya Jamal dan yau tun safe daya fita bai dawo bah" Ta fashe da kuka tace "Gashi har Magrib suma basu dawo bah" Mifzal ya jinjina kai baice komai bah, Ram ya kalli Mabrookahn dake ta share hawaye yace "Mabrookah inaso ki dubi girman Allah ki fad'amin abinda kika sani" Tsaida kukan datake tayi tana kallasu da mamaki "Ban gane me kake nufi bah" Mifzal ya sauke ajiyar zuciya yace "Me kika sani game da Kidnapping d'in Ummy da akayi" Ba shiri ta sake rushewa da kuka tana kallansu "Wallahi bansan komai akai bah, bani da wata masaniya" Ram ya gyad'a kai ya mik'e yafito daga d'akin, Wasu masu gadi ya nufa yad'an musu 'yan tambayoyi ya fita, daga nan farfajiyar gidan yama Mifzal waya ya fito suka tafi. Su Mami basu suka shigo gida ba sai k'arfe goma na dare, dukansu wujiga wujiga suka shigo, Mabrookah ta fad'a jikin Mami tana kuka "Mami baku gansa bah" Dakyar ta iya cewa "Duk inda kike tunani munje bamu samesa bah, mun kai report duk police station d'in da kika sani dake cikin Zaria" Aunty Faty ta karb'e da cewa "Wani police station da mukaje a nan mukaga motarsa ake shaida mana anga motar neh a wani k'auye anma baya ciki dan ana tunanin shima kidnapping d'inshi ak...." Mabrookah ta soma tsalle tana kuka sosai tare da yarfe hannu "Na shiga uku kada su kashe shi Wayyo Allah" Daga Mami har AuntyFaty babu wanda ya iya magana suka haura sama suka barta nan tana kuka kamar ranta zai fita. Su Jamal yanda sukaga Rana haka sukaga dare, Ummy na nan manne dashi tana mai kuka, dakyar ya lallasheta tayi shiru tana sauke jiyar zuciya. A zaune suka kwana wuraren k'arfe takwas na safe Oga ya shigo d'akin yana murmushi, Jamal ya d'aga kai sukayi ido biyu "Wahalar ku takusa zuwa k'arshe yau, yanzu ranku na tsakanin rayuwa da mutuwa" Ummy ta fashe da kuka ta sake k'ankame Jamal tare da chusa fuskanta a k'irjinsa. Hankalin Jamal ba k'aramin tashi yayi ba jin magana da Ogan yayi. Ogan yayi dariya ya fita daga d'akin. K'arfe Bakwai na safe a MTN office tama Ram da Mifzal. Sunyi sa'a an kunna wayan Ummyn, Nan suka soma bin location d'in a hankali, Bomo Village ya nuna musu, Nan akayi Hacking d'in wayan. Wani lungu chan ya nuna musu, Mifzal ya shafa suman kanshi yana kallan Computern "Ta yaya zamu iya gane wajan nan?" Shiru kowa yayi yana tunani, chan Ram yace "Yauwa Why not mu rink'a communicating dasu sai suna mana kwatance" Mifzal ya saki lallausan murmushi yace "Yes Good Idea" Dasauri suka bar wajan, mota hud'u suka d'auka na 'yan sanda, cikin 'yan mintina suka shiga cikin Bomo Village d'in. Communicating suka soma da mutanen Office d'in yawo sosai sukayi tayi cikin k'auyen basu gane wajan bah. Location d'in ya b'ace ta Office suka kira Mifzal suka sanar dashi. Ransa idan yayi dubu ya b'aci, cigaba sukayi da yawo suka kakkasu waje daban daban suna dudubawa. Jamal na rungume da Ummy aka sake turo k'ofar d'akin, Ogan ne ya sake shigowa da yaransa kusan su hud'u. Tsugunawa yayi inda suke ya cire kyallen dake bakin Jamal d'in, Sannan ya juyaga Ummy ya shafa gefen fuskanta tayi saurin fizge fuska "Karka sake ka k'ara tab'amin matata" Wani dariya Ogan yayi ya juya ya kalli yaran nasa suma suka kyalkkyale da dariya, ya juya ga Jamal d'in dake ta huci kamar zaki "Karna sake tab'a matarka kace?" K'okarin mik'ewa yakesan yi anma ya kasa saboda d'auresan da akayi hannu da k'afa. Ogan ya matso da fuskansa saitin na Jamal d'in yana murmushin mugunta. "Yanzun nan zakaga k'arshen tab'awa" Ta tallafo fuskan Jamal d'in suna kallan Juna "Zanyi Raping matarka a gabanka kuma baka isa kayi komai bah" Ummy ta saki kuka tana k'okarin mik'ewa. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:17 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 78 to 80 Ummy ta saki kuka tana k'okarin mik'ewa. Jamal ya saki wani irin k'ara yana k'okarin mik'ewa ya kasa. Yaran Ogan ne sukayi saurin rik'e Jamal d'in, sai k'okarin kuccewa yake yana huci "Karka sake ka tab'a min matata" Ogan ya saki dariya ya soma tafiya a hankali inda Ummyn ke zaune tana kuka, ja da baya ta soma yana binta yana mata murmushi "Ga mace har mace, ki bani had'in kai kawai dan yau babu wanda ya isa ya hana damo kaiwa ga harawa" Kuka take sosai tana matsawa baya yana cigaba da binta, kokarin kwacewa Jamal ketayi yana wani irin k'ara idanunsa na zubar da hawaye, su uku suka rik'esa duk yanda yayi ya kwace kasawa yayi. Cikin wani irin murya yace "Kada kayi haka dan Allah, ka fad'i duk abinda kakeso zan maka." Ya saki dariya yana shafa gefen fuskan Ummyn, "Bana buk'atar komai sai matarka, tun randa na fara ganinta na kwad'aitu da ita. Dan nasan zan huta da ita sosai" Jamal yayi saurin runtse ido yana cigaba da hawaye, Ogan ya tsugunna inda take makure a bango yana k'okarin kai hannunsa k'irjinta, tayi saurin goceta ta sake fashewa da kuka "Dan Allah kayi hak'uri kamin rai, ni matar aurece. Ka dubi girman Allah ka kyalleni" Ya saki dariya mai sauti yace "Idan kinga nabar d'akin nan sai naga na aikata abinda nakeso dake" Kokawa suka soma, Jamal nata ihu yana k'okarin k'wacewa had'e da rok'on ogan. Wani daga cikin yaransa ne ya shigo d'akin dasauri ya k'arasa inda Ogan ke tsugunne yamai magana a kunne. Mik'ewa yayi dasauri yama sauran yaransa dake rik'e da Jamal alama su sakeshi, ba musu suka sakesa ya fita dasauri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82