Skip to content

Chapter 49

Chapter 49

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

falon k'asa ta had'u da Mamin, suna had'a ido da Aunty Faty gabanta ya fad'i. A hankali ta k'arasa ta zauna k'asa chan nesa dasu tace "Ina kwana Mami" Wani dogon tsaki Mamin taja sannan tace "Sai yau kikasan zakizo ki gaisheni?" Aunty Faty tace "Ai ta rik'a, kinsan itace mai gidan" Kan Ummy a k'asa tana hawaye, Mami tace "Baki isa ki rabani da d'ana ba wallahi, kuma kuruwana da d'ana kur, naman mu d'aci garesa" Ta nunata da yatsa ta cigaba da cewa "Ni nan da kika gani, asiri ya buga dani ya barni, asiri baya cina daga ni har d'ana. Baki isa ki chanza min alk'iblan gidana bah" Aunty Faty ta tab'e baki tana karkad'a kafa "Kuma kina dawowa ki kawo min makullin motan da ya baki, dan baki isa kina hawa mota, 'yata na hawa bah" cewar Mami. Aunty Faty tace "Fita kiba mutane waje" Dasauri ta fita tana hawaye, har lokacin Jamal na tsaye yana ciranta, ganin ta fito tana hawaye yasa ya runtse ido cike da bak'in ciki. Mota shiga driver yajata suka bar gidan har lokacin bata daina kuka bah. _Thank Uh so much My Fans_ I'm now better Alhamdulillah Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 56 n 57 Mota ta shiga driver yajata suka bar gidan har lokacin bata daina kuka bah. Ransa duk ba dad'i ya koma side d'insa, dakin Ummyn ya nufa yana murd'awa k'anshin room freshner had'e dana turaren wuta suka masa sallama, a hankali ya shiga ya soma bin d'akin da kallo, komai tsaf tsaf ba datti sai k'amshi had'e da sanyin Ac ke tashi. Toilet d'inta ya shiga yayo wanka ya fito sannan ya koma nasa d'akin dan babu kayansa a nata. Zaune ya samu Mabrookah sai turo baki take a shagwab'e, yad'anyi murmushi ya k'arasa kan gadon "Morning Sis" Baki ta sake turowa idanunta taf da hawaye "Ayyah Sis kuma, bayan ita Wife kake cemata" Yanda tayi maganan sosai ta basa dariya, gefen fuskanta ya shafa ya sakar mata murmushi ya mik'e ya soma shiryawa dan yayi latti. Duk abinda yake tana nan ta k'uresa da ido har ya gama shiryawa. Sosai yake mamakin irin rashin kunyan Mabrookah, ko gezau batayi ba sanda ya warware towel d'in jikinsa zai saka kaya. Yana gamawa ya juyo da murmushi "Sai na dawo" "A dawo Lafiya" tace tana cigaba da turo baki. Yana fita ya nufi side d'in Mami gabansa na fad'uwa, gaidata yayi itada Aunty Faty, ba yabo ba fallasa Aunty Faty ta amsa masa gaisuwan. Mami ko da fara'a tace "Naga mota Allah ya saka da alheri" Shaf shi yama manta da maganar mota, Ameen kawai yace ya mik'e ya musu sallama ya tafi. Bayan tafiyarsa Mabrookah ta mik'e dakyar ta koma d'akinta, wanka ta sakeyi ta sauya zuwa riga da skirt na material. Da d'angyashi ta shiga side d'in Mami Kan dinning ta samesu suna breakfast, tunda ta shigo Mami ke binta da ido har taja kujera ta zauna tareda "Washh" ta yatsine fuska kamar zatayi kuka "Yaya dai Lafiya?" Cewar Aunty Faty tana kallanta Ta sake shagwab'e fuska "Ba Ya Jamal baneh" Mami ta girgiza kai kawai dan ta fahimci inda maganan nata ta dosa, Aunty Faty tayi kini kini darai "Me ya miki Jamal d'in" "Ba shi baneh ya...." Mami tayi saurin katseta da cewa "Wannan ai tsakanin su ne na mata da miji, mu ba ruwanmu a ciki" Kurrrri Aunty Faty tayi ma Mabrookahn tana kallanta. Chan kuma ta girgiza kai ta janyo plate ta zuba mata breakfast d'in ta tura mata gabanta. Ranar a side d'in Mami ta wuni sai shagwab'a take suna biye mata, bama kamar Aunty Faty har cewa take ta natsu dan k'ila ta samu ciki kada yazo ya b'are suyi asara. Dariya ko Mami tayi har cikinta ya kusa yin ciwo. A b'angaren Ummy kuwa kuka ta dunga yi a mota, saida taga driver yayi parking a k'ofar makarantan sannan tayi shiru ta goge hawayenta ta fito. Gaba d'aya babu abinda ta fahimta a karatun ranar sai dai tad'anji dama dama tunda tabar kurkukun gidan nan. K'arfe uku driver ya dawo ya d'auketa ya maidata gida, d'akinta ta wuce kai tsaye ta cire uniform d'in jikinta ta d'aura towel ta shiga wanka. Tana fitowa ta saka bak'in jallabiya ta shimfid'a sallaya ta tada sallah dan la'asar tayi. Kicin ta shiga ta dafa indomie guda d'aya dan bama ta tunanin zata iya ci, ta fito ta dawo d'akinta. Kad'an taci ta ture gefe ta kwanta, kan kace me bacci ya d'auketa dan dama batayi bacci ba jiya. Tun k'arfe uku yaketa neman layin Wife d'insa anma a kashe, tunaninta ne ya hanasa sukuni, musamman abinda ya faru tsakaninsu d'azu. A daddafe ya gama aikinsa, lokacin ana kiraye kirayen sallahn Magrib. Saida ya tsaya masallacin k'ofar gida yayi sallah sannan ya shigo gidan. Side d'inshi ya nufa kai tsaye, Mabrookah ya samu a falonta taci gayu cikin wani farin top mai hannu d'aya tsawonsa bai kai cibiya bah, sai wani mini skirt na jeans mai kyau. Da d'an sauri ta k'arasa ta rungumesa tareda shiga jikinsa "Oyoyo Honey na" Tab'e baki yayi yad'an rab'ata da jikinsa "Ya kike" Ta turo baki "Bayan ka barni cikin pain da safe kayi tafiyarka" D'an murmushi ya mata, "Ina zuwa" Ya haura sama dasauri, d'akinsa ya shiga ya sami gadon kacha kacha kamar yanda ya bashi da safe, ransa ne ya b'aci yaja dogon tsaki ya aje briefcase d'in hannunsa. Wanka ya soma yi yana mai takaicin hali irin na Mabrookah, a girme dai ta girme ma Wife d'insa naisa ba kusa ba, Anma sam batada hankali da kuma sanin yakamata. Three quater yasa light brown da Bak'in top ya fito. D'akin Ummyn ya murd'a ya shiga da sallama, k'asa ya sameta kwance kan sallaya tana bacci. K'arasawa yayi wajan ya kwanta kusada ita ya janyota jikinsa sosai sannan ya soma shafa albarkatun k'irjinta a hankali. Cikin bacci taji ana shafata, ta bud'e ido dakyar dan bacci ne sosai a idota, ganin Jamal yasa ta k'ara bud'e ido ta soma turasa da k'arfi "Ni ka daina tab'ani, ka fita ka bani waje" Ta k'arashe maganan cikin kuka kanta k'asa. Bai damu da abinda zata masa ba ya sake rungumota jikinsa, kuka ta soma yi mai sauti tana dukansa "Ni ka kyalleni, ka koma wajanta. Shine kukayi tayi dan naji koh, ni bazan zauna ba gid..." Saurin had'a bakinsu yayi waje d'aya, sai yanzu ya gane fushin datake, sosai abin ya basa mamaki ganin yanda kishisa ya rufe mata ido. Ta wani b'angaren kuma yaji dad'i sosai, ko ba komai yanzu ya k'ara yarda tana sansa. Mutsu mutsu ta cigaba a jikinta tana k'okarin k'wacewa anma ta kasa. Saida ya tsotsi bakinta san ranshi sannan ya saki bakin, idanunta a lumshe hawaye na cigaba da gangara daga idanunta, a hankali ya rad'a mata "I'm so sorry!" Ta bud'e idanunta da sukayi ja tana kallansa, "Mabrookah matata ce, dole na sauke duk wani nauyi nata daya rataya a kanta. Pls ki daina fushi dani kinji, i so much love uh" Duk abinda ya fad'a gaskiya ne, sai dai har lokacin haushin sa takeji turesa tayi daga

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82