Skip to content

Chapter 35

Chapter 35

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

sanyaye ta mik'e tabi bayanta har k'asan, kamar yanda Mabrookan ta barshi haka ta dawo ta sameshi zaune, kujera Mabrookah taja ta zauna, ganin haka itama Ummyn taja ta zauna kanta k'asa. Gyaran murya yayi yace "Banasan tashin hankali, inaso ku zauna lafiya." Ya juya ya kalli Mabrookah data turo d'ankwali gaba yace "Kece k'arama dan haka bansan rashin kunya ko..." "Tab! Haba Ya Jamal wannan ai cin fuska neh, Kasan dai nesa ba kusaba na girme tah" Harara ya watsa mata yace "Ai ko jiya aka haifeta matsawar saida aka d'aura aurena da ita kafin naki to itace babba" K'ara turo baki Mabrookan tayi dan maganarsa sosai ya b'ata mata rai. Itadai Ummy batace komai ba kanta k'asa tana wasa da zoben hannunta. "Banasan hayaniya, kowacce ta kama girmanta. Kada naji wani abun da ba daidai bah" Yanda yake maganan yana kallan Mabrookah yasa ta gane da ita yake "Duk maganan nan da kake nasan dani kake tunda ni kake kallo" cewar Mabrookah Jamal yayi murmushin takaici ya juya ga Ummy yace "Jaleelah!" D'ago ido tayi da mamaki tana kallansa, ba wasa a fuskanshi yace "Ina fata kinji abinda nace" Kai ta gyad'a alamar eh hawaye cike a idonta, wato shi yana ma nufin zata dauwama a gidan kenan. "Kamar yanda aka saba a aladance, tunda Ummy ce babba, ita zan farama kwana bakwai sannan na dawo d'akinki" Ya nuna Mabrookah fuska ba walwala "Anma dai kasan kaci kana biyu koh" "Nasani ai ba bansani bah." Ya fad'a rai b'ace "Sannan ina gama kwanakin da zanyi a d'aku nan ku za'a fara raban kwana" Dogon tsaki Mabrookah taja tad'au handbag d'inta ta fita dan dama da shirin tafiya makaranta take. Zaman kurame sukayi a kan dinning d'in har lokacin kanta k'asa, murya kamar mai rad'a yace "Serve me" Ta d'an d'ago suka had'a ido ta maida kai dasauri, sun kai minti biyar a haka gashi ya fara latti, ya sake d'agowa yace "Na fara latti kuma yunwa nakeji" Ta sake d'agowa ta kalleshi tana b'ata fuska "To mai zan maka" Ta fad'a tana turo baki a shagwab'e "Serve me" Ya sake cewa yana kallanta da narkakun idanunsa "Ni fa bajin abinda kake cewa nake bah, kamin da hausa" Sai a sannan ya tuna da rashin makarantar da batayi bah. Yad'an dafe goshi yace "Serve me yana nufin ki Ciyar dani ko ki zubamin abinci. Duk wanda kika d'auka a ciki" Ta gyad'a kai tana d'an murmushi dan a rayuwarta ba abinda takeso kamar yau taji tanayin turanci. Abincin ta zuba mai ta tura masa gabansa, ya kalli abincin ya d'ago ya kalleta "Wannan abincin da kika zubamin kamar mu goma zamuci" Turo baki tayi ta juya zata bar wajan yayi saurin rik'o hannunta yace "Ai baki isa bah, sai dai ki zauna muci tare dake" Ta soma kici kicin k'wacewa tana k'okarin kuka. Saurin janyota yayi jikinsa ya matseta yana kallan fuskanta "Na gaji da shiru shirunki Baeby, na gaji da kukanki, na gaji da rashin maganarki" Duka ta soma kai mai a k'irji tana kuka sosai "Ni ka sakeni, ka sakeni ko na maka ihu" "Ki natsu Baeby muyi magana" Turjewa ta cigaba dayi tana kuka "Pls ki daina kuka ki tsaya ki saurareni" Rik'on daya mata ya sassauta yana kallanta "Meyasa baki sona Jaleelah, meyasa baki son zama dani? Meyasa kike guduna? Mena miki" Batace mai komai ba sai duk'ar dakai datayi tana kuka "Bani amsa pls, ba kuka zakiyi bah." Murya na rawa tace "Ni kawai bana sanka neh" Gabansa ne ya fad'i, kwalla suka cika idonsa ya d'ago yace "Saboda me baki sona" Shiru tayi ba amsa sai kuka dake. Wani wawan rik'o ya mata har saida ta saki k'ara, gaba d'aya fuskarsa yayi ja saboda b'acin rai "Tel me meyasa baki sona" "Saboda nama Ya Bilal alk'awarin zan aureshi" Hawayen dake mak'ale a idonsa suka gangaro, ya sake matseta a jikinsa tareda d'ago fuskanta suna kallan juna ido cikin ido "Kar kimin haka Jaleelah, ina sanki kamar raina" Yakai hannunta kan k'irjinshi "Kinji yanda zuciyata take bugawa akan sanki, plssssss" Sosai ya bata tausayi ta tureshi da k'arfi tana cewa "Taya zan iya sanka bayan Mami bata sona, Mabrookah bata sona, dan Allah ka taimakeni ka sakeni wallahi bana san zama dakai" Ta fashe da kuka ta juya ta soma hawa sama, jin muryan Jamal tayi yana cewa "Saki kikeso Ummy?" Ta juyo ta kallesa ta gyad'a kai a hankali, wasu hawaye suka gangaro masa yasa bayan hannu ya share yace "Zan sakeki Ummyyy.... ```Zakuyi hak'uri da yanayin typing d'ina da kuma jinkirin posting. Abubuwa ne kwana biyu suka min yawa. Dafatan zaku karb'i uzuri nah``` Ummy Abduol✍🏻 [3/22, 5:21 AM] 0mmer Farouk: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 40 "Zan sakeki Ummy anma dan Allah kiyi hak'uri ki bani lokaci" D'ago ido tayi a razane tana kallasa gabanta ba fad'uwa. Bai sake kallanta ba ya share hawayen fuskansa ya d'au jakansa ya bar wajan. Ba shiri ta sulale a wajan ta fashe da matsanan cin kuka. Ta dad'e a wajan tana kuka Laurat ta shigo side d'in da sallama, ganin Ummyn zaune a wajan tana kuka yasa ta k'arasa dasauri ta d'agota tana tambayanta "Laurat Ya Jamal zai sakeni" "Mene?" Cewar Laurat tana zare ido Kasa magana tayi sai k'ara rushewa da kuk datayi ta mik'e ta haura sama zuwa d'akinta tana cigaba da kuka. A sanyaye Laurat ta mik'e tabi bayanta, kwance ta sameta tana kiran wani number ana ce mata a kashe anma bata fasa kira bah. Saida ta k'araso kusada ita sannan ta hango ashe Bilal take kira. A fusace ta fizge wayan tana kallanta rai b'ace "Haba Ummy meyasa kike haka? Yakamata ki cire Bilal a ranki tunda yanzu ke matar aurece. Ki d'au kaddara kibi mijinkin insha Allahu zakiji dad'i a rayuwarki nan gaba" Ummy ta d'ago hawaye chab'e chab'e a fuskanta tana kallanta "Alkawari fa na d'auka Laurat, karki manta da girman alk'awari" Haushi Ummyn ta soma bata, batasan sanda tace "Alkawarin banza, to ai shi ya fara karya alk'awarin bake bah. Da yana sanki da gaske bazai je ya zauna abinsa bai waiwayi inda kike bah. Kinsan girman zunubin da kike kwasa kuwa Ummy? Kina da miji anma kina tunanin wani" Shiru tayi tana nazarin maganar Laurat "Haba Ummy sai kace baki je bah, karfa ki manta hukuncin macen da tace mijinta ya saketa" Gabanta ya fad'i sam ita batayi tunanin wannan bah. Wani kukan ta sake rushewa dashi ta kama hannun Laurat tana kallanta "Ya kikeso nayi Laurat, ina cikin tsaka mai wuya. Bansan me zanyi bah, gaba d'aya komai ya tsaya min" "Kibi mijinki Ummy shine kawai, Wallahi na rantse kuma bazanyi kaffara bah, Alkhairi ne aurenki da Jamal a yanda na lura. Kiso mijinki, ki janyoshi a jiki, ki basa kyakyawar kulawar daya kamata. Karki bari Mabrookah ta miki tsakiyar da ba ruwa" Ta sake yin shiru tana tunani, tabbas maganar da Laurat ta fad'a mata gaskiya ce, saidai matsalar duk lokacin da tayi yunk'urin yin haka saita kasa. "Ya zanyi Laurat, Ya Jamal yayi fushi dani" "Duk abinda ya faru ke kika ja, kiyi k'okari ki gyara rayuwar aurenki" Ta mik'e dasauri tana gyara

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82