Chapter 16
Chapter 16
Mama da Baba, Jamal ya runtse ido da k'arfi ya bud'e yana kallan Ramadhan "Why is she crying" Mami tace "Ana gyara mata hannu ne dan ta samu karaya" Gabansa ya fad'i, yayi shiru cikeda tunani, sun d'au lokaci a wajan kafin likitocin da nurses su fito. D'aya daga cikin likitocin yace "Bazaku samu daman shiga ba saboda tana buk'atar hutu" Ya mik'ama Abba wani takarda yana cewa "Za'a mata Xray a kanta dan a duba ko fashewan da kan nata yayi ya mata illah" Abba da Ramadan suka masa godiya ya wuce tareda sauran likitocin. Ramadan ya amsa takadan a hannun Abba yaje Ya biya ya dawo ya mik'ama Mami receipt d'in. Sun d'au lokaci a haka ba wanda yace komai kowa da abinda yake sak'awa a ransa, daga bisani wata Nurse ta basu daman shiga. Jamal ne ya soma shiga d'akin, kwace take kan gadon marasa lafiya, kanta nan nad'e da bandage sai d'an kumbura da gefen kan yayi, haka idanunta a kukumbure, hannunta na hagu shima a nad'e. Tausayinta ne ya kamashi ya k'arasa har bakin gadon yana cigaba da kallan fuskanta gabanshi na fad'uwa, Abba yace "Yakamata a sanar ma Iyayenta dan susan halin da take ciki" Mami ta kalli Ummyn cikeda tausayawa tace "Hakane, saidai ina tsoron sanar dasu dan mahaifinta yanada ciwon zuciya kuma ga makanta" Jamal ya juya dasauri yana kallan Mamin. Ramadan yayi folding hannuwansa yace "Dole a sanar dasu Mami coz wannan fa ba k'aramin ciwo bane da za'ace za'a boye musu" Abba yace "Gaskiya ne Ramadhan" Shidai Jamal baice komai bah haka kuma bai daina kallan fuskanta bah, Dare ne ya tsala sosai Abba ya d'au Jamal da Ramadan suka tafi gida ita kuma Mami ta kwana da ita. A chan gida kuwa Bacci ne ya gagari Laurat ta zauna shiru a kitchen ko b'angarensu bata tafi ba, tunanin Ummy ne ya sata gaba so kawai take tasan halinda k'awar nata take ciki. Tana nan zaune a kitchen wuraren karfe biyu na dare su Abba suka dawo, bata san sanda ta fito dagudu ba ta fito falon, ganin Abba dasu Ramadhan yasa taja burki tareda duk'ar dakai "Yaya dai me kikeyi har yanzu baki tafi b'angaren ku bah" Cewar Ramadhan yana kallanta Ta duk'ar dakai hawaye cike da idanunta tace "Ina jiran dawowan Ummy neh" Dama kan Jamal na k'asa jin ta ambaci Ummy yasa ya d'ago yace "An kwantar da ita a asibiti, go and have some rest gobe inasan ganinki da safe" A sanyaye ta juya ta tafi tana kuka a hankali, kan wheel chair d'in ya sauka ya kama kafad'ar Ramadan yana cewa "Na gaji da wheel chair d'in nan" A tare suka haura sama harda Abba ya musu saida safe ya shiga d'akinsa, suma suka shiga na Jamal. Ruwan wanka Ramadan ya had'a masa mai d'an zafi ya shiga ya gasa jikinsa ya fito. Bai cema Ramadhan d'in komai ba ya hau kan gadon ya juya fuska dan duk hankalinsa nakan Ummy. Washe gari da wuri suka shirya, hau Alhamdulillah k'afar tasa tad'anyi kwari, a falon sama suka had'u da Abba, A tare sukayi breakfast sannan suka sauko k'asa. Laurat suka samu zaune kan carpet tana jiransu, Jamal ya k'arasa ya zauna ta gaidashi sannan ta gaida Abba da Ramadhan, Jamal ya kalleta yace "Wacece Ummy a wajanki" Dan shiru tayi sannan tace "A nan gidan muka had'u da ita, k'awata ce kawai" Baice komai ba ya gyad'a kai ya mik'e tareda sa hannayenshi a aljihu yace "Ok zamuje dake sai ki zauna da ita a asibiti" Ta gyad'a kai tace "Tho" Abba yace "haka yakamata kam" Mabrookah ce ta sauko daga sama tana yatsine fuska tana kallan Jamal "Ya Jamal ina Mami" Wata uwar harara ya wurga mata fuskarsa ba walwala "Ke a rayuwarki bazaki tab'a Iya gaisuwa ba koh?" Ta turo baki tareda kauda kai sannan tace "Ina kwana Abba, Ina kwana Ya Ramadhan" Tad'an dubi Jamal d'in tace "Ina kwana Ya Jamal" Baice mata komai ba saima tsaki dayayi yabar falon. A motar Abba sukaje asibitin, Ramadhan na driving, Abba na gefensa sai Jamal dake baya shida Laurat. Suna isa suka samu an gungurota a gado za'a maida ita d'akin da take, Mami na biye dasu. D'akin suka shiga, nan Mami ke sanar dasu cewa anje anyi Xray d'in neh. Laurat ta tsugunna ta gaida Mami sannan ta aje basket d'in kayan breakfast. Abba yace "Ya jikin nata?" "Dasauk'i saidai har yanzu bata farka bah" Ramadhan da Jamal suka gaisheta ta amsa tareda tambayan jikin Jamal d'in, yace dasauki. Abba ne yayi dropping Mami a gida shi kuma ya wuce aiki, nan Jamal da Ramadhan suka wuni a d'akin, Laurat nachan gefe zaune duk a takure ranta ba dad'i ganin halinda k'awar nata ke ciki. Sun dawo la'asar lokacin Laurat na toilet Ummy ta farka, a hankali ta bud'e ido tana bin d'akin da kallo, Jamal ne yayi saurin mik'ewa ya tako zuwa inda take yana kallanta. Had'a ido sukayi ba shiri ta mik'e zaune dasauri lokacit guda ta saki razananen Ihu ta rik'e Hannunta wanda ta karye tana cigaba da kallany Jamal d'in a tsorace. Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 20 Had'a ido sukayi ba shiri ta mik'e zaune dasauri lokaci guda ta saki razananen Ihu ta rik'e Hannunta wanda ta karye tana cigaba da kallany Jamal d'in a tsorace. Kuka ta fashe dashi ta runtse idonta gam tana k'okarin sauka daga kan gadon, Laurat ta fito daga toilet ta k'araso ta rik'e "Lapia Ummy menene" A k'irjin Laurat ta b'oye fuskanta tana nuna mata Jamal da Hannu, Ramadhan ya rik'e kafad'ar Jamal yace "I think tsoronka takeji, muje waje tukun" ya k'are maganan da rik'o hannun Jamal d'in, har sun kai bakin k'ofa Jamal ya sake juyowa ya kalleta, sai kuka take tana cigaba da b'oye fuskanta. Laurat ta d'agata dakyar tana share mata hawaye "Bud'e idonki baya nan, bud'e kiga" Dakyar ta samu ta bud'e ta zubasu akan Laurat din har lokacin kuka take "Ki daina kukan, fad'amin menene" Nuni ta cigaba da mata da hannu tana cewa "Laurat Jamal, yana min fatalwa" Laurat batasan sanda ta kyalkyalle da dariya bah, Ummy ta d'aga kai tana kallanta da mamaki "Kai! Anma dai Ummy kin cika shirme" Ta sake kyalkyallewa da dariya ta zauna bakin gadon tana cewa "Bah fatalwa baneh, Jamal ne da kika sani. Allah ya bashi lapia" Ummy ta zaro ido da mamaki "Dan Allah dagaske" "Ehmana, ashe mutanen b'oye ne a jikinsa ba'a sani ..." Ramadhan ne ya shigo d'akin da sallama, duk'ar dakai tayi kunya ya kamata "Lapia dai Ummy" Laurat tayi dariya tace "Ta d'auka fatalwa yake mata bata san ya warke bah" Ramadhan yayi murmushi yace "Oh Allah sarki, ya jikin naki" A kunyace tace "Dasauk'i Alhamdulillah" Bai kuma cewa komai ba ya fita, chan sai gashi da Jamal d'in sun shigo. Kallo d'aya ya mata ya saki lallausan murmushi, itako sai sunar dakai take cikeda kunya. Kan kujera ya zauna yace "Sannu, ya jikin?" Murya chan ciki kamar mai koyon magana tace "Da...D..Dasauk'i" Murmushi ya sake yi ya juya ya kalli Ramadhan yace "Ram yaushe na zama fatalwa ban sani bah" Dariya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82