Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

Laurat ta shigo Garden d'in dasauri dan ta hangosu ta windown kitchen sanda take wucewa dashi. Ummy na ganinta tayi saurin share hawayen fuskanta "Ummy lafiyarki kuwa? Kin tab'a ganin an fito dashi idan ba fita za'ayi dashi bah" Ummy ta d'ago tana murmushin takaici "Bantab'a gani bah, anma kuma yanda ake masa baya min dad'i. Bai kamata ace kullum yana guri d'aya bah, yakamata a rink'a fitowa dashi yana chan iska" "Nidai da zakiji ta nawa da kin maidashi Ummy, karki jama kanki" Yatsine fuska Ummyn tayi tana cewa "Nifah bazan koma dashi ba sai mun gama shan iska" Laurat ta girgiza kai "Nidai ba ruwana" Bata jira mai Ummy zatace ba tabar wajan dasauri. Tsaki tayi ta zauna gabansa ta tankwashe k'afarta tana kallansa Labarin dariya da tatsuniya taita bashi, tanata magana ita kadai ita a dole suna hira, idan ta bada labarin dariya saidai ita tai dariyan, Wani lokaci kuma ta fashe da kuka. haka suka k'arashi zamansu ta gungurashi ta maidashi d'akinsa. Kamar kullum yauma tana gyara d'akinsa bayan ta gama nasu Mami, wardrobe d'inshi ta bud'e ta soma gyara masa kayansa dake ciki, wani riga ta d'aga wasu hotuna suka zubo daga k'arkashin rigan, hotunan ta d'auka ta soma dubawa, Jamal ne tun yana d'an yaronsa da kuma wani wanda yana ya fara tasowa har zuwa wanda ya d'addauka sanda yake makaranta a egypt, shagala tayi da kallan hotunan, Allah sarki rayuwa kamar ba'ayi bah. Wasu hawaye suka gangaro mata ta juya tana kallanshi cikeda tausayawa. A sanyaye ta k'arasa gyaran ta dawo kusada shi ta zauna, kurani ta d'auka a kan bedside ta dawo gabansa ta zauna ta soma karantawa cikin zazzak'ar muryarta. Suratul Yasin ta bud'e tana karantawa a hankali kanta k'asa, tayi shafin farko tana a nabiyu bata ankara ba taga Jamal ya fad'i tim a gabanta. Tho Fah! Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* OMG gaba d'aya littafin nawa ni kad'ai, Babu abinda zance sai nagode Allah saka da Khairan ya barmu tare my Swt *Ummu Farheen* Allah yasa yanda kika fara wannan littafi *K'alubalen rayuwa* lapia, Allah yasa ki gama lapia. Ameen Page 15 Tayi shafin farko tana a na biyu bata ankara ba taga Jamal ya fad'i tim a gabanta. A tsorace ta aje kur'anin ta zaro ido cikeda tsoro, dasauri ta k'asara ta juyoshi dakyar tana kallanshi cike tsoro, ga mamakinta ganin idanunshi tayi a rufe, ba shiri ta fashe da kuka ta soma jijigashi a tsorace "Jamal, Jamal" Dagudu ta fito daga d'akin tana kuka wui wui, haraban gidan ta nufa, ko Mabrookah dake gyara parking motanta batayi ba ta nufi wasu maza dake wanke mota da sauran ayukan gida tana cigaba da kuka, rok'onsu tayi su taimaka mata a d'aga shi. Mabrookah sukazo suka wuce har lokacin tana tsaye bakin motanta, ganin sunyi ciki itama ta bisu dasauri, Ummy ce ta musu jagora har zuwa saman tana cigaba da kuka. A tsorace suma mazan suka karasa inda take kwance suka d'agoshi, har lokacin yana k'asa idanunshi a rufe, kan wheel chair d'in suka d'aurashi. Daidai nan Mabrookah ta shigo rai b'ace tana binsu da ido, wani razananen k'ara ta saki ganin idaunshi a rufe fuskanshi yayi ja sosai, mazan summ summ suka bar d'akin dan sunsan halinta batada mutunci. Ummy bata ankara ba taji saukan mari a kuncinta, a gigice ta d'ago idanunta da suka rune zuwa ja tana kallan Mabrookah "Kin kasheshi kin huta, me ya miki da zaki kasheshi" Jin maganan Mabrookah yasa Ummy sakin wani sabon kuka mai k'arfi ta fad'i k'asa tana kallanta "Wallahi ban kasheshi bah, hakanan naga ya fad'i, dan Allah ki yarda dan..." "Shut ur dirty mouth" Mabrookah ta fashe da kuka ta fit daga d'akin tana laluban Mami a waya. Kuka sosai Ummy keyi ta rarrafo ta dawo gabanshi ta tsugunna tana kallansa. "Dan Allah karka mutu, ka rufamin asiri, nikad'ai ce wajan Iyayena, Allah ne gatanmu ni ce gatanmu" Ta sake rushewa da kuka ta rik'e wandonshi tana girgiza shi a hankali kanta k'asa. Labari ne ya cika gidan na cewa Jamal ya mutu, duka ma'aikatan gidan sun taru a haraban gidan kowa fuskarsa d'auke da damuwa. Horn akayi masu gadi suka bud'e gidan, Motan Abba da Mami a tare suka shigo, ba wanda yayi k'wakwaran parking Mami sai kuka take suka shiga cikin gidan dasauri. Mabrookah najin motsinsu ta fito daga d'akinta tana kuka, duk a tare suka shiga d'akin, har lokacin Ummy na tsugunne gabanshi tana kuka. Saurin d'agowa tayi tana kallansu tana girgiza kai "Wallahi ba abinda na masa Mami ki yarda dani" Ga mamakinsu ganin shi sukayi zaune yanda yake kamar da, idanun nan nasa a kafe. Wani nauyayyan ajiyar zuciya Abba ya sauke ta sunkuya ya tab'a kirjinsa, jin yana numfashi yasa ya juya yana kallan Mami "Yanada rai ba abinda ya samesa" Tsagaita kukanta tayi tana kallan Ummy rai b'ace "Meh kika masa Ummy" Cikin kuka tace "Ki yarda dani Mami ba abinda na masa hakanan ya fad'i" "Karya kikeyi, hakanan ba abinda kika masa zai fad'i?" Mabrookah ta fad'a tana nuna Ummy da yatsa Abba yayi saurin katsesu yace "Ya isa, tsautsayi neh nasan" Ya juya ya kalli Ummy yace "Sai a kiyaye gaba" Fuuu Mabrookah tabar d'akin, Mami da Abba suka bar d'akin a sanyaye, Mami ce ta fad'ama masu aikin bai mutuba, nan kowa hankalinsa ya kwanta suka koma bakin aikinsu. Duk da haka hankalin Mami bai kwanta ba saida ta kira likitansa yazo ya dubasa tareda tabbatar musu yanada rai sannan ba abinda ya samesa. Sosai Mami taja ma Ummy kunne akan kula dashi. zage dantse tayi wajan Feeding d'inshi akan lokaci da kuma bashi magungunansa. Haka kullum takan sauko dashi k'asa taita zagayawa dashi. Sam bata gajiya da d'awainiyar Jamal dan tausayinsa takeji sosai. Wannan watan kamar yanda Abba ya alkawarta, dubu d'ari ya biyata albashi, murna wajan Ummy ba'a magana har kuka saida tayi data amsa kud'in, dama ranar sati neh, dakyar Mami ta yarda ta barta taje gida weekend dan yanzu bata cika zuwa ba saboda hidimar Jamal, itama sam batasan barinsa saboda halinda yake ciki. Da murna isa gida, iyayen nata ta tarar a tsakar gida suna shan iska, da murna ta taresu, Mama ta soma fara'a tana "Lale lale, barka da zuwa" Ta k'arasa ta rungume Mama tana dariyar farinciki, Baba ma murnar yake yanata lallubenta da hannu, ta rik'o hannunshi ta d'aura a kanta tana dariya, ya shafa kanta yace "Allah ya miki albarka Jaleelah" Ameen Mama da Ummy sukace, ba b'ata lokaci ta ciro kud'in albashinta ta d'aurama Baba a hannu tana cewa "Baba ga albashina na wannan watan" Kud'in yake tattab'awa baki bud'e "Ummy ina kika samu wannan kud'in haka? Wannan daga ji yafi albashinki" Sai a sannan ta musu bayani, Iyayen nata sukaita murna tareda sa mata albarka. Ganin yanda suketa murna yasa ta fashe da kuka, Mama ta rungumeta tana lallashinta. Kasuwa ta shiga tayi siyaiyan kayan abinci sosai harda Umman Bilal, atamfofi kala shidda ta siya masu sauk'in kudi, tasai shadda d'aya da yadi biyu na Baba sannan tasai masa magungunansa da kuma sauran y'an abubuwan anfanin gida sannan ta dawo. Atampha

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82