Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

ba ta sauko ta fita haraban gidan, nan ma ba kowa ta dawo, harta gota d'akin Ummy sai ta juyo muryan mutane a d'akin, a hankali ta dawo ta murd'a kofan. Jamal ta gani da Twins da Ummy sunata hira. Tsawa ta dakama Twins suka fito daga d'akin dasauri, ta hararai Jamal tace "Ka fito inasan ganinka" Tana tafe yana binta a baya har d'akinta, gefen gado ta zauna shi kuma yaja stool ya zauna "Jamal wannan shine zai zama magana ta k'arshe da zan maka akan yarinyan nan Ummy, wallahi ka fita idona na rufe" Ya duk'ar dakai k'asa "Wai mai kakeso ka zama ne Jamal, baso d'aya ba baso biyu ba na fad'ama banasan ganinka da yarinyan nan" "Mami kiyi hak'uri" "Duk ba wannan ba, ya maganan da mukayi dakai na Mabrookah" Dam! Gabansa ya fad'i "Mami pls kiyi hak'uri, wallahi i have no feelings for her" Da Mamaki tace "Me kake nufi knan" Ya sake duk'ar dakai "Yanzu Jamal bazaka iya cikama yayata burinta ba, yarta d'aya Mabrookah, batada burin daya wuce taga tayi aure." Ta turo baki yana jujuya kai "Alhaji zai kiraku ya tambayeku idan kunasan juna, inaso ka amsa kana santa. Hakan ne kad'ai xai sani farinciki" Ya gyad'a kai yace "To shikenan Mami" Tayi murmushi tace "Allah ya maka albarka" Ya mik'e yabar d'akin yana gungunai. Bacci ne ya gagari idon Jamal, shi gaskiya harga Allah bazai Iya auren Mabrookah ba dan baya santa. Wuraren sha biyu ya mik'e kamar wanda aka tsikara ya sauko k'asa, d'akin Ummy yayi knocking a hankali ya shiga, dan yau so yake ayita ta k'are. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:41 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 27 D'akin Ummy yayi knocking a hankali ya shiga, dan yau so yake ayita ta k'are. Tsaye ya sameta kan sallaya tana sallah, gefen gadon ya zauna yana kallan yanda take ganawa da ubangijinta cikin natsuwa. Ji yayi ta k'ara birgeshi, ya sauke ajiyar zuciya yana cigaba da kallanta. Tana idarwa ko addu'a bata tsaya yi ba ta juyo dasauri tana kallansa da mamaki "Lapia Ya Jamal meya kawoka d'akina da daran nan" "Nazo ne muyi wani magana" "Magana? Ka bari mana sai gobe yanzu dare yayi" Baice komai ba ya mik'e ya k'araso inda take zaune shima ya zauna yana cigaba da kallanta "Bazan iya hak'uri har sai gobe bah, maganar nada mahimmanci sosai" Ta gyara zama tana facing d'inshi "Ina jinka, saidai kayi sauri saboda dare kuma ina sallah neh" Ya sauke dogon ajiyar zuciya yana kallanta "Nayi tunanin na b'oye abinda ke raina game dake, wani abu yana neman yazo min wanda bana so" Kurrri Ummyn tayi tana kallanshi, dan sam bata san inda maganar tasa ta dosa bah. "Ina sanki Ummy, wallahi i so much love uh" Ba shiri ta mik'e a zabure tana kallansa da mamaki "Ki yarda ki aureni banasan Mabrookah, na miki alkawarin zan miki duk abinda kikeso pls" Hawaye suka soma gangaro mata a fuska tana girgiza kao tana kallanshi "So kuma? Haba Ya Jamal, dan Allah ka daina wannan wasan" Ya mik'e tsaye "Tun ranar dana fara ganinki naji ina sanki, ina sanki badan komai naki ba, komae.... "Ya isa! Ya isa!! Banaso inji" Hannayenta biyu tasa ta toshe kunnuwanta tana kuka sosai "Abinda yasa kenan kaje ka gyara mana gida, ka siyan mana kayan alatu dan ka siya iyayena...." "No! Ummy ki fahimceni, wallahi ko kad'an badan wani abu nayi haka...." Tayi saurin katseshi cikin muryan kuka "Ka makara, inada wanda nakeso, koda banida shi bazan tab'a sanka bah Ya Jamal. Tun bayan warkewanka nake cikin k'unci da hantara a gidan nan. Talauci bah hauka baneh, indai haka ake k'udi kada Allah ya bani" "No pls Ummy, ki tsaya ki saurareni" Cikin d'aga murya tace "Bazan ji bah, Ya Jamal ka fitar min daga d'aki banasan ji! Ka fita" Kallo ya bita dashi cikin tashin hankali ya fita ya haura zuwa d'akinsa. Ranar daga Ummy har Jamal babu wanda ya runtsa. Washe gari yana kan dinning yana breakfast tazo ta wuce idanunta a kukumbure, hakan ya tabbatar masa da cewa tayi kuka daran jiya. Wani tausayinta neh ya k'ara shiga ranshi, harga Allah yanasan Ummy, so na tsakani da Allah. Dan shi a shirye yake dayayi komai a kanta. Kamar wanda aka tsikara ya mik'e dasauri ya nufi side d'in Abba, saidai kash yana zuwa ya samu Mami a falon, k'eya ya sosa ya juya Abba yace "Yaya dai Jamal, akwai wani abu neh?" Yayi saurin cewa "Aa ba komai" Da sauri ya fita daga falon ya shiga motarshi yabar gidan. Saida Abba ya fita dan ranar zaiyi tafiya, sannan Mami ta fito daga side d'in ta dawo nata, Mabrookah ce ta soma saukowa tana murmushi "Mami dan Allah kiban kud'in, yau nakeso muje nida k'awayena mu fitar da ankon" Sosai maganan Mabrookah yaba Mami dariya, saida tayi mai isarta sannan tace "Mabrookah kenan! Ke kin tab'a ganin inda aka fitar da anko ba'a sa rana bah" Baki ta turo gaba "Mami ai ba sai ansaka rana bah, already Abba ya bashi ni, haka an bani shi. Kuma Mommy ce tace na fitar yanzu" Kai Mami ta girgiza zata haura ta d'auko handbag d'inta ta fita aiki. Ranar sukuku Ummy ta wuni, har lokacin maganan Jamal ne a ranta, harga Allah bazata iya san Ya Jamal ba dan har yanzu bata gasgata maganan rasuwan Bilal bah, har lokacin tana nan rik'e da alkawarin data masa na bazata tab'a auren kowa ba sa shi. ***** Wuraren k'arfe tara da rabi, Ummy na d'aki tana sallan isha'i dan tayi lattin sallan saboda aikin da Aunty Faty keta sata. Muryan Aunty Faty ta jiyo tana salati tana cewa "Maimuna! Maimunatu!! Ina kike an sace min sark'a" Mami dake falon k'asa itada Mabrookah sukayi saurin mik'ewa "Sark'a kuma? Wane irin sark'a" Cewar Mami "Sark'an nan dana siya mana danaje Dubai, Million d'aya da dubu d'ari shidda shi na nema ban gani bah" "Toooh!" Cewar Mabrookah tana rik'e da hab'a Mami tace "Aa bafa zai tab'a yuwuwa bah, dan gidan nan ba'a sata. Yaya Faty kidai k'ara dubawa" "Bafa inda ban duba ba, sark'an nan d'auka akayi" "Mudai je mu sake dubawa" Duka suka haura sama zuwa d'akin Aunty Fatyn, batsa batsa sukayi da d'akin suna nema anma bah sarka. Mabrookah ta rik'e k'ugu tana bin d'akin da kallo "Gaskiya abin nan da mamaki yake, kuma nasan dai masu aiki basa haurowa nan saman" Aunty Faty tai saurin cewa "Saidai Ummy ai ita ke shigowa tana gyare gyare, dan babu wanda zai d'au sark'an nan saboda ke Maimuna da Mabrookah kunfi k'arfin wannan" "Aa Yaya Faty, bana tunanin Ummy zata d'au sark'an nan. Dan duk abin yarinyan nan bata sata" "Maimuna! Lallai baki san talaka ba har yanzu, nidai gaskiya bazan yarda. Million d'aya harda dubu d'ari shidda ba k'aramin kud'i baneh. Gaskiya ban yarda ba sai anyi chaje kuma masu aikin nan za'a duba" Mabrookah tai saurin cewa "Gaskiya ne Mommy, dan tunda nazo gidan nan ba'a tab'a sata ba sai yau" Itadai Mami batace komai bah, Aunty Faty da Mabrookah suka sauko k'asa zuwa d'akin Ummy, ganin Haka yasa Mami ta biyosu

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82